Mu San Hukunce-Hukuncen Fiqhu - Darasi Na [17]

    Wannan É—aya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waÉ—anda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta Æ™arin fatawowi.

     

    Tambayoyi Da Amsoshi

    GAME DA ADDU'A BAYAN SALLAME SALLAH

    Idan muka duba da nassin hadisi da bayanai da suka zo a cikin litattafn fiqhu, babu inda aka samu cewa Manzon ALLAH {s.a.w} yana yin addu'a a bayan sallar farillah wacce har zai É—aga hannu sama ko kuma yana karanta wata addu'a shabbai su ma karantawa bayan ya faÉ—a babu wannan kwata-kwata, sai dai iya azhkar daya koyar, shi kuma wannan kowane mutum zai yi nasane shi kaÉ—ai.

     Amma hakan ya samo asaline daga gurin malaman gargajiya wanda yin haka bidi'ah ne ba koyarwar Manzon ALLAH {s.a.w} bace.

     Manzon ALLAH {s.a.w} ya kasance yana shigar da duk wata addu'arsa ne cikin sujjadarsa ta farillah a ya yin sallar farillah ko a Æ™arshen tahiya bayan kammala salati da addu'o'i na sunnah sai kuma mutum ya roÆ™i duk wata buÆ™ata tasa da yakeso ya roÆ™a.

     

     Amma da zarar anyi sallama ba a shigo da wata buÆ™ata sai iya abinda aka samu a nassi Annabi {s.a.w} yanayi kuma ya sunnantawa sahabbansa (R.A) yin hakan.

     

     An sunnanta a kowacce sallar farillah idan mai sallah zai shigo da buÆ™atarsa to ya roÆ™a a cikin sujjadarsa ta sallah, a sujjadar farko ko a ta Æ™arshe ko kuma a cikin ko wacce sujjadah a cikin sallar farillah sai ya faÉ—awa ALLAH buÆ™atarsa.

     

     Manzon ALLAH {s.a.w} ya ce:

     

    Babu gurin da bawa ya fi kusanci da UBANGIJINsa kamar a cikin sujjada don haka ku yawaita addu'a a cikinta.

     

     Sannan kuma ana roÆ™on ALLAH a Æ™arshen tahiyar sallah kafin ayi sallama, ananma za ka iya shigo da duk wata buÆ™atarka, kuma ita addu'a ana iyayinta a cikin ko wanne nau'in yare.

     

     Amma bayan anyi sallama ba a É—aga hannu a roÆ™i ALLAH babu hadisi a kan wannan, hasalima ita addu'arq da aka yita a cikin sallah tafi domin za a É—auki sallarka tare da addu'arka akaita ga UBANGIJINka a tare ba a rarrabe su.

     

     Kawai dai anayin azhkar da aka sunnata a bayan sallar farillah ne wanda Annabi {s.a.w} ya karantar kuma sunanan damÆ™am a cikin hadisai ingantattu.

     

     Musammam idan mutum yanaso ya sami cikakken bayani ya nemi littafi mai suna Siffatus-salatun Nabiyyi {s.a.w} musamman na Muhammad Nasiruddin Albani (R.h) zai sami ingantattun hadisai tareda maganganun malaman fiqhu a cikinsa.

     

     Amma a sallar Nafila ana iyayin addu'a a cikin sujjadah haka kuma ana iyayin addu'a a Æ™arshen tahiya kafin sallama, ana kuma iya É—aga hannu sama a roÆ™i ALLAH duk wata buÆ™ata bayan an sallame sallar nafila.

     

     Idan mai sallah ya yi sallar Nafila yana iya É—aga hannunsa sama ya roÆ™i ALLAH dukkan damuwarsa bayan ya gama saiya sauke hannunsa ba a shafawa a fuska ko a wani guri, babu hadisi ingantacce da ya zo da cewa Annabi {s.a.w} yana shafe fuskarsa bayan ya gama addu'a.

     Wannan bayanai muna kawo su ne domin dukkan al'ummar musulmi susan sallar Manzon ALLAH {s.a.w} da kuma yadda za su bi wajen kiyaye koyi da shi a cikin sallarsu, domin ALLAH baya karÉ“an ibadar da ba a koyo ta daga Manzon ALLAH {s.a.w} ba.

     

    ALLAH shi ne mafi sani.

    Duk mai neman ƙarin bayani ya tuntuɓe mu ta private.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.