Ni Maye Ne?

     Wani ne ya je wurin walima sai ya zauna layin gaba. Sai aka shigo da abinci🍲🍜🍝. Sai aka fara rabawa daga baya. Kafin a zo wurinsa abincin ya ƙare😀☺; Sai ya tashi ya koma baya. Aka shigo da naman kaji🍗🍖 sai kuma aka fara rabawa daga gaba. Kafin a zo wurins naman ya ƙare😀😃😳; Sai ya tashi ya koma tsakiya. Haushi ya ƙule shi. Ya kwantar da kansa bisa tebur kawai sai ya ji an ce malam bismillah. Ya ɗago kai sai aka miƙo masa tsinken sakace🍟 tunaninsu har ya gama ci hutawa yake. Sai ya tashi ya shara wa mai rabon abincin mari ya ce: "Aka gaya maka ni maye ne, ban ci abinci ba ban ci nama ba sai itace??" 😂😜. 

    Ni Maye Ne?


    Write your comments below or send us jokes to upload. 

    Rubuta tsokaci a ƙasa (comment), ko ku turo mana labaran barkwanci domin mu ɗora a kafar.


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.