Ramadan

 Wannan na ɗaya daga cikin jerin waƙoƙin Malam Khalid Imam da a kullum suke faɗakarwa da ilimantarwa da nishaɗantarwa. Yana taɓo fannoni daban-daban a cikin waƙoƙinsa, ciki har da abubuwan da suka shafi lamuran yau da kullum.

Yau ga Ramadana ya zo,

Dausayin rahama da tuba,

Mai rabon baya sakewa,

Yai ta bacci ibada.


Ramadana watan farauta,

Maharbi ba shi bacci,

Ya ce zai kama giwa,

Sai yai himma da naci.


Watan naci da himma,

Watan zikiri da salla,

Al'kur'ani karimi,

Karanta ɗan uwana.


Ramadana watan salati,

Sadaka kyauta ka dage,

Ko da tsagin dabino,

Bayar domin Razzaƙu.


Leda ta ruwa ka shayar,

Allah Zai ba ka lada,

Kason azumi ka samu,

Mai ciyarwa na rabauta.


Dangi zaga ku gaisa,

Kai zumunci ɗan uwana,

Gaba kar kai da kowa,

Ba shakka zaka dace.

Malam Khalid Imam
08027796140
khalidimam2002@gmail.com

14/03/2023

Post a Comment

0 Comments