Ticker

Ranar Da Na Fara Zuwa Zance

 Wani lokacin idan na tina yarinta sai na yi ta dariya🤣

Na Tina ranar da na fara  zuwa  zance, tin daga sanyi safiya na wanke wata shadda ta na sanya Mata sitati, na wuni Ina goge ta da dutsin guga.😅

Akwai wani ta kalmi sau ciki Mai Kama da kwale kwale, na dauko shi Akwai wani Mai wankin takalmi ya wanke man shi tass🌻

Hula ta kuwa na dade da karbo ta daga wajan wanki.

A ranar wuni na yi Ina shirya Kai na,kai ka rantse da Allah cewa wajan shugaban kasa za ni ko kuma wajan wani Attajiri🙈

Tin da nagama sallar magariba na shira, na dauko shaddar Nan da na wuni Ina gogewa tana she ƙi,😍 na ɗauko hula da takalmi na na kifa🙈

Na nufi gidan su yarinyar da yake lokacin bani da waya 😥 tin akan hanya na dauki hayar wani yaro da zai kiraman ita muka tafi tare da shi😎

Muna Isa kofar gidan su yarinyar na ji gabana ya soma faduwa 😳 yaron ya Shiga domin ya kirawo ta, na tsaya  ƙikam a kofar gidan kamar tabarya ko motsin kirki bana iya Don kada Karin guga ta ya karye 🙈

 Zuwa can sai ga yaron ya dawo inda nake, yaceman Wai gata Nan  zuwa, Nan take na ji wani gumi ya karyoman🥶 kan kace kwabo gumi ya wanke man fuska,🙆 koya na ɗan ji motsi sai inji bugun  zuciya na ya karo,  zuwa can na ji an danno kofa🙆😳

Yarinyar ta fito ta nufo wajan da nake tsaye , duk tako daya idan tayi da nufin isowa wajena, sai na ji bugun  zuciya ta  ƙaruwa yake😥 A karon farko kenan Dana fara  zuwa  zance na ji kamar na she ƙa da gudu🙈🤣

Yarinyar ta  ƙaraso ta dubeni, ta ce sannu ,Kaine kake kirana?

Saboda tsabar ruɗewa na ce Mata ba ni ba ne 🙈🙆🙄🚶


Post a Comment

0 Comments