Shawara A Kan Neman Taimako Saboda Sharrin Kishiyoyi

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu Alaikum. Ƙanwatane za ta yi aure kuma me mata uku za ta aura, shi ne ake ta ba ni shawara a kan na nema mata taimako saboda sharrin kishiyoyi, shi ne na ce barina tambaya me ya kamata a yi mata wanda bai kaucewa addiniba?

    𝐀𝐌𝐒𝐀👇

    Toh abun da za ayi shi ne a koya mata yadda za ta kyautatawa mijinta da yadda za ta girmama dangin mijinta sekuma anuna mata muhimmancin kiyaye sallah da gaskiya da rikon amana ban da tsegumi ban da gulmace gulmace ban da albazaranci da dukiyar miji sannan ta mutunta sauran matansa duk wani me haƙƙi a kanta tadaure ta ba shi haƙƙinsa sekuma a koya mata zikirran safiya dana yammaci shi ke nan a kai ta dakin mijinta, babu wani taimakon da za a nema mata bayaga wannan kuma.

    Allah ya sa mu dace

    Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/BXjuXb1WxX99NV3OsXPnLV

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    ************************************** 

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.