Shin abaya tana ɗaukar hukuncin hijab?

Abin da ya wajaba ga mace musulma shi ne, ta sanya tufafin da zai suturce jikinta, in ban da fuska da tafin hannu a wajan wasu malaman suna ganin fuska al'aura ce.

Don haka ita ma ya wajaba a rufe ta, tun da a nan kyawun mace yake, sannan kayan da zatasa su zama masu kauri, baya halatta ta yi ado inba a cikin gidan mijinta ba, ko tare da muharramanta.

 Suturar mace musulma ba a so ta yi kama da kayan maza, kamar yadda ba a so su zama kayan da za su ja hankali, ko waɗanda aka fesa musu turare mai ƙarfi.

 Sannan mutuƙar Abaya ko jallabiyya ta suturce jiki yadda ya kamata, ba ta matse jikin mace ba, to za ta ɗauki matsayin hijabin da ALLAH daManzonsa {s.a.w} suka yi umarni.

Don neman ƙarin bayani duba:

Majmu'ul-fataawa 22/110 da Hijabul- Mar'atulmuslima shafi na: 54 zuwa 67.

ALLAH shi ne mafi sani.

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments