Shin Akwai Surori Da Aka Keɓance A Sallar Shafa'i Da Wutiri?

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamaalaikum. Mlm ina da tambaya Sallar shafa'i da wutiri

    Aka ce raka'ar farko suratul A'ala za a karanta ta biyu suratul kafirun ta ƙarshe kuma suratul iklas Mlm haka ne Kuma Mlm ni bana iya karanta suratul kafirun sai na kalli Alƙur'ani da suratul A'ala shin Mlm zan iya karanta surorin danake da haddarsu akaina ko wa'inanne

    Kuma wai da gaske Idan anfara ba a denawa ko wataran irin Idan m

    utum ya ji ya gaji haka?

    𝐀𝐌𝐒𝐀👇

    Waalaikumussalam warahmatullahi wabarakatuh.

    Alhamdulillahi Ala Ni'imatul Islam.

    "Bayan haka: haƙiƙa Allah maɗaukakin sarki ya wajabta bauta akanmu mu bayin sa shi kaɗai domin nuna godiyar mu a bisa halitta da kuma fifikon da ya yi mana a kan sauran bayin sa"

    "Ni a iya sanina gaskiya ban san inda aka ƙayyade cewa a sallar wutri ga wasu surori da aka keɓancesu ake karanta su a cikinta ba, yawancin wannan kuma yana zuwa ne daga gurin masu ta'ammuli da bid'ah"

    "Tabbas a cikin sallolin nafilah akwai irin waɗanda suka zo a hadisai masu yawa waɗanda suke nuni da cewa Manzon Allah sallallahu alaihi wasallama yana karanta Surah kaza a cikin sallar nafila kaza, to amma kuma hakan bawai yana nuna wajabci ba ne, yin hakan sunnah ne bawai farillah ba, idan ka wajabtawa kanka, to lallai bawai musulunci ne ya wajabta maka ba"

    "A cikin sunnah babu inda aka keɓance wata sallah ta nafilah ko ta farillah cewa dole ga irin wata surar da za a karanta mata, sai dai wata-ƙila a sami cewa Annabi ya fi karanta sura kaza a cikin sallah kaza da sura kaza"

    "Sannan kuma shi Alƙur'ani duk inda ka karanta shi a cikin sallah to alƙur'ani ka karanta, bawai sai dole ka haddace shi ba ne sannan za ka iya bautawa Allah, mutum zai iya karanta kowace Surah a cikin sallarsa, amma duk da hakan baya hana kuma mutum ya ƙara neman ilmin alƙur'ani, ma'ana ya dage da haddar wasu surorin domin daɗa yalwata karatun sa ta mabanbantan surori"

    "Malamai suka ce babu laifi idan mutum bai iya karanta alƙur'ani ba a haddace, zai iya buɗewa ya kalla musamman idan sallar tasa ta kasance ta nafilah ce, duba da hadisin Nana Aisha Allah ya ƙara mata yarda da take umurtar bawan ta ya buɗe alƙur'ani ya karanta domin ya jagorance su sallah da azumi"

    "Hadisi ya zo daga Manzon Allah sallallahu alaihi wasallama ya ce: mafi soyuwar aiyuka a gurin Allah maɗaukakin sarki, shi ne aikin da bawa ya dauwama yana akansa yana aikata shi ko da kuwa ɗan kaɗan ne"

    "Amma wannan baya hana kuma idan mutum ya yi ibadar ya gaji wataran kuma sai ya ɗan taƙaita domin ya huta"

    Wallahu A'aalmu.

    Ya Allah ka yafe mana dukkanin laifukan mu, Ameen.

    Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/F1YV6JhrD89EfJddPLvƘ32

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.