𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum Dan Allah ina da tambaya macen da ta yi ɓarin ciki aka mata wankin ciki bayan nan sai jini yake zuwa mata ya dai bayyana jinin ciwo ne. Shin za ta dinga wanka ne lokacin da za ta yi kowace sallah? Ko kuwa tsarki kawai za ta yi lokacin sallah?
𝐀𝐌𝐒𝐀👇
To dan'uwa Za ta yi tsarki kuma ta yi alwala ya yın kowacce sallah, saboda hukuncinsu ɗaya da mai jinin istihala, kamar yadda Annabi ﷺ Ya umarci Fadimatu 'yar Abi-Hubaish a hadisin Ibnu Hibban mai lamba ta: 1354, da yın alwala yayin kowacce sallah, lokacin da ya tabbatar tana yın jinin cuta.
Don neman karin bayani duba: Risala Fi Dima'u
Addabi'iyya: 45
Allah ne mafi sani.
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa
Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/BXjuXb1WxX99NV3OsXPnLV
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.