Shin Wanda Ya Rasa Sallar Jumma'a Uku Ya Kafirta?

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum, Allah shi gafarta mallam, shin wai idan mutun ya rasa sallar juma'a 3 ya zama kafiri?

    𝐀𝐌𝐒𝐀👇

    Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuh. Alhamdu lillahi rabbil alamin wassalatu wassalamu ala rasulillah wa ala alihi wa sahbihi ajma'in.

    Subhanallahi, wanda ya rasa juma'a uku, da gangan, ba kuskure ba, yana sane, ba mantuwa ba, da zaɓi ko ganin daman sa, ba tilasci, toh bai kafirta ba. Amma Annabi ya ce duk wanda ya bar sallar juma'a uku yana mai sakaci da ita, Allah zai masa ɗaba'u (khatamu) a kan zuciyar sa, a nan duniya, ga hadisin

     عَنْ أَبِي الْجَعْدِ الضَّمْرِيِّ- وَكَانَتْ لَهُ صُحْبَةٌ- أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: ((مَنْ تَرَكَ ثَلاَثَ جُمَعٍ تَهَاوُنًا بِهَا طَبَعَ اللَّهُ عَلَى قَلْبِهِ)).

    Yana da kyau mu san mene ne ɗaba'u a wannan gaɓa. Ɗaba'u wata azaba ce ta kulle ko rufe kafar ji (kunnuwa) da fahimta (zuciya), ta yadda alkhairin da ke wajen zuciya ba zai samu shiga cikin ta ba, haka kuma sharrin da ke cikin ta ba zai fita daga cikin ta ba.

    Ma'ana dai ɗaba'u, wata nau'in azaba ce a duniya da ke sababin kai mutum halaka a nan duniya a lahira kuma gidan wuta, Allah ya tsare mu. Har ila yau ɗaba'u na kai mutum ga halaka ne saboda haifar masa da rashin fahimta, jahilci da son zuciya ba son gaskiya ba, har ta kai ga yana biyayya ga zuciyar sa ne ba ga Allah ko Manzo ba.

    Haka ɗaba'u na kai mutum ga munafunci kamar yadda alƙur'ani ya yi nuni a kai

     

    (وَمِنۡهُم مَّن یَسۡتَمِعُ إِلَیۡكَ حَتَّىٰۤ إِذَا خَرَجُوا۟ مِنۡ عِندِكَ قَالُوا۟ لِلَّذِینَ أُوتُوا۟ ٱلۡعِلۡمَ مَاذَا قَالَ ءَانِفًاۚ أُو۟لَـٰۤىِٕكَ ٱلَّذِینَ طَبَعَ ٱللَّهُ عَلَىٰ قُلُوبِهِمۡ وَٱتَّبَعُوۤا۟ أَهۡوَاۤءَهُمۡ)

    [Surah Muhammad 16]

    A taƙaice dai ɗaba'u, shi ne kuma khatamu, ciwon kafirci ne da Allah ke azabtar da kafirai da shi, Allah yana azabtar da musulmi da shi sai idan ya tuba, Allah ya ce

     

    (أَفَرَءَیۡتَ مَنِ ٱتَّخَذَ إِلَـٰهَهُۥ هَوَىٰهُ وَأَضَلَّهُ ٱللَّهُ عَلَىٰ عِلۡمࣲ وَخَتَمَ عَلَىٰ سَمۡعِهِۦ وَقَلۡبِهِۦ وَجَعَلَ عَلَىٰ بَصَرِهِۦ غِشَـٰوَةࣰ فَمَن یَهۡدِیهِ مِنۢ بَعۡدِ ٱللَّهِۚ أَفَلَا تَذَكَّرُونَ)

    [Surah Al-Jathiya 23]

     

    Don haka wannan mutum ya gaggauta tuba da nadama, ya daina ƙin halartar juma'a don ya tsira, amma yana nan matsayin shi na musulmi bai kafirta ba.

    Wallahu ta'aala a'lam.

     Amsawa:

    Malam Aliyu Abubakar Masanawa

    Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/GEahmrOpR4pA5TmW0ZW0cU

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.