𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum,
Shin Malam Mutumin da yake siyar da abu kamar shinkafa a asalin farashinsa idan an ba shi sabon kuɗi, idan kuma aka ba shi tsohon kuɗi sai ya kara kuɗi mene ne hukuncin sa?
Na ji wasu sun ce Riba a yake ci.
Ya abun yake?
𝐀𝐌𝐒𝐀👇
Wa alaikumus salam
Ba riba ba ce ya halatta, tun da ba canji ba ne.
Annabi ﷺ ya hana nuna bamabanci ne tsakanin kuɗin da suke jinsi ɗaya a canji ba a cinikayya
ba, kamar yadda ya zo a hadisin Ubadah da Abu hurairah
Ba kowanne wuri ake amsar tsohon kuɗi ba, wannan ya sa in ya
bambanta bai Yi laifi ba, tun da ba canji ba ne tsakanin kuɗin da kuɗi .
Allah ne mafi sani
Dr Jamilu Yusuf Zarewa
Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa
Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/GEahmrOpR4pA5TmW0ZW0cU
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.