𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Malam Dan Allah Ina so Ina fada maka Wani Abu Da ya dame ni Ina
so Ka ba ni Solution Akai Ina da Wata Ƙawa Sunanta Rabi Atu Kusan
Girmammu Ɗaya Kuma Maƙociyar mu ce Ammade Su Talakkawane Wani Lokacin Sai ta Tashi
Ta Tafi Tana Zuwa Gidajen Masu Kuɗi Tana Ƙwanƙwasamusu Tanacewa Me Aiki ce
Idan Ana buƙata Wlh Setai Ta Bingidaje Tana
yin Haka Kuma Nacemata Tadena Taƙi Tom Dan Allah Ina so Ka ba
ni Shawara a kan Haka Dan Injawo Hankalinta Tadena Saboda Hakan Ina ga Kamar Ba
Abu ba ne Mai kyau Amma Dan Allah malam Meza ka ce Gameda Hakan Nide Banason
Hakan Da Takeyi Wlh.
𝐀𝐌𝐒𝐀👇
Abin da ya dace a nan shi ne. Ku za ku yi Contribution
ku ba ta wani kuɗi mai dan yawa, sai ku ce ta je tana yin Sana'a. Ina
ga idan kuka yi Mata hakan. Kun Kubutar mata da Mutuncinta, Sannan kuma za ku Sami
Lada mai Tarin yawa a wajen Allah.
Kuma Abin Mamaki irin abin da yake Faruwa a Irin wannan
zamanin ke nan. Talauci ya yi yawa. Fatara ta yi yawa. Mutane ba kowa ba ne
yake da zuciyar Taimako da Alkairi. Mutane sun zama Marowata. Rowar Bala'i ta
yiwa Mutane Yawa. Wai kuma a Haka Ake Nema Aljannah...
Na tabbatar da Cewar idan har wannan yarinyar Budurwa
ce, ba Karamin Tunani ta yi ba. Idan ba ta yi Hakan ba. A Banza wasu za su
Lalata mata Rayuwa suna daukar Nauyin ta. Kamar yadda a Yanzu haka Wasu matan
suka Tsinci Kansu.
Jiyan nan wani yake bani Labari ya ga Wasu 'yan mata
da suke Neman Abincin da za su ci a yi Iskanci da su. Idan har ba ta hakan ba.
Ba za su samu abincin da za su ci ba. INNA LILLAHI WA INNA ILIHI RAJI'UUN.
Sabida haka Wajibin Al'umma su dage da taimakawa
Junansu. Wajen Baiwa Juna Kayan Abinci da Tufafi da jari na kasuwanci da samarwa
juna aikin Yi. Wanda Mace da Namiji kowa zai dogara da Kansa. Domin idan ba
haka ba akwai matsala. Idan aka yi Hakan an Taimaki Juna kuma an Taimaki
Musulunci da Musulmai. Kuma an magance Wasu Fituntunun.
Sabida haka Abin da ya dace a nan shi ne ku hada mata
Jari ku ba ta ta kama kasuwa kafin Allah ya fito Mata na Gari.
Allah shi ne Masani.
Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa
Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/FmJ5Ojsns1KFolTP8ƙu9GT
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.