Ya Yi Bakance Ya Kasa Cikawa. Yaya Zai Yi?

    Farko dai shi bakance makaruhi ne, a wani É“angaren kuma haramun ne a wajan wasumalaman, saboda Annabi {s.a.w} yana cewa:

     Bakance bayazuwa da alkairi, kamar yadda Muslim ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 1639. Sai dai ya wajaba a cika bakance idan aka yi.

     Wasu daga cikin malaman hadisi sun tafi a kan cewa idanmutum ya yi bakance ya kasa cikawa zai iya-yin kaffararrantsuwa,

     Saboda hadisin da aka rawaito daga Muslim alamba ta:1645. a sahihinsa, wanda Annabi {s.a.w} yake cewa:

     Kaffarar bakance irin kaffarar rantsuwa ce.

    Duba Alminhaajna Nawawy 4/269.

     Saboda haka a bisa abin da ya gaba ta mutum zsi iya-yin kaffarar rantsuwa wato:

     Ya ciyar da miskinai goma, idan baida halin haka to, ya tufatar da su, idan baida halin haka, to ya 'yantakuyanga (baiwa),

     Idan babu hali, sai a yi azumi uku, kamar yadda ya zo a suratul Ma'idah ayata: 89.

    ALLAH shi ne mafi sani.

    **************************

    Wannan É—aya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Æ˜ur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waÉ—anda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta Æ™arin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.