𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Salam. Ina da tambaya
Na ranci kuɗi fam biyu kamar shekaru (62) da suka wuce, ban biya ba. In zan biya yanzu da haka fam biyun zan biya koko ya za a yi?
𝐀𝐌𝐒𝐀👇
Wa alaikum assalam
Wasu malaman sun tafi a kan cewa zai biya kima ne, na
kuɗin da ya ranta, misali Fam biyu me za ta iya siya a wancan
lokacin, sai a bada kimarta a yanzu, saboda in an biya da adadinsu akwai
cutarwa ga wanda ya ba da bashin, kuma yana daga cikin ka'idojin Sharia tunkude
cuta gwargwadon iko.
Malaminmu Sheikh Ibnu Jibrin (Bajimin malami, mai amsa
fatawa a Saudiyya) ya tafi a kan cewa ana iya biyan kwatankwacinsu daga kuɗin da darajarsu ba ta faduwa
kamar Dalar Amurka.
Allah Ne Mafi Sani
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa
Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/GEahmrOpR4pA5TmW0ZW0cU
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.