Yadda Salaf Suka Kasance Suna Shiri Domin Fuskantar Watan Ramadan

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Ya salaf suka kasance suna shiri domin fuskantar wañnan wata Mai Albarka (Ramadan). Mene ne koyarwarsu, da matafiyarsu akan hakan? Kuma ya shauƙin su yake ga wañnan wata??

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Dabi'ar magaba ta Kamar yadda yake a rubuce a cikin littafai' Wanda aka ruwaito da sanadinsu daga amintattu: cewa lallai su sun kasance suna rokon Allah Mai girma da ɗaukaka da yakaisu wañnan wata (Ramadan) kafin isowarsa. Domin abun da suka sani dangane dashi na Alkhairi da daraja dake cikin sa. Sannan bayan shigar watan: suna rokon Allah ya taimake su akan ayyukan Alkhairi, bayan Kuma Ramadan ya fita suna rokon Allah ya karɓa musu ayyukan dasuka gabatar acikin wañnan wata. Kamar yadda Allah Mai girma yake fada:

    وَالَّذِينَ يُؤْتُونَ مَا آتَوْا وَقُلُوبُهُمْ وَجِلَةٌ أَنَّهُمْ إِلَىٰ رَبِّهِمْ رَاجِعُونَ

    Da waɗanda ke bayar da abin da suka bayar, alhali kuwa zukatansu suna tsõrace dõmin suna kõmawa zuwa ga Ubangijinsu.

    (Suratul Muminun 60)

    أُولَٰئِكَ يُسَارِعُونَ فِي الْخَيْرَاتِ وَهُمْ لَهَا سَابِقُونَ

    Waɗancan suna gaggawar tsere a cikin ayyukan alheri, alhali kuwa suna masu tserewa zuwa gare su (ayyukan alheri).

    (Suratul Muminun 61)

     

    Sun kasance suna ƙoƙari wurin yin aiki, bayan sunyi aikin Kuma sai su dinga tunani shin Allah ya amsa ayyukan su ko Bai Amsa ba! Wañnan Kuma Yana faruwa dasu ne sakamakon sanin girman Allah da suka yi. Da sanin Allah ba ya amsan wani aiki sai Wanda aka yi shi da (iklasi) Kuma aka yi Shi yadda Annabi yakoyar. (Mutaba'a) sun kasance ba sa tsarkake kansu, Kuma suna tsoron abun da zai ɓata musu ayyukan su. Samun Aikin su ya karɓu yafi damun su fiye da wahalan yin aikin, domin fadin Allah Mai girma:

     

    إِنَّمَا يَتَقَبَّلُ اللهُ مِن المُتَّقِيْنَ

     

    Allah Yana karɓa daga masu taƙawa ne.

    (Suratul Ma'ida 27)

     

    Sun kasance suna rage neman duniya, suna kashe lokutansu a masallatai, suna kiyaye azumin su ba sa cutar da kowa. Suna kiyaye lokutan su cikin karantu  littafin Allah. Ba sa sake da lokacin su ya tafi a asara, Kamar yadda mutane suke awannan lokacin. Suna raya dararen su da salloli . Yinin su Kuma cike take da azumi, karatun Ƙur'ani, zikiri da sauran ayyukan Alkhairi. Ba su kasance suna barin wa lokaci daidai da minti ɗaya ko second ɗaya ba face sun gabatar da Aikin Alkhairi a cikin sa.

     

    WALLAHU A’ALAM

                                    

    Fatwa: Sheikh Salihul Fauzan.

     

    Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Fadakarwa  a Sunnah.

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/ECƘsg2ycfS0FUI3fHfIdjƙ

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.