Pioneers ɗin Pi Netwok da dama sun yi koken cewa passphrase ɗinsu ba ya aiki ko ya daina aiki. Idan dai a baya phassphrase ɗin na aiki, to akwai yadda za ku iya gyara shi. Ku bi matakan da aka zayyano a ƙasa dalla-dalla domin magance matsalar.
1. A ɓangaren saitunan wayarku (settings), ku tabbatar da cewa an kashe Private DNS (wato an saka shi a OFF). A ƙasa an kawo bayanin yadda za ku yi:
a. A wayarku, ku buɗe wurin saituna (settings).
b. Ku danna kan network and internet >>> Advanced >>> Private DNS. Idan kuka kasa samo shi, to ku nemi "Private DNS." (ta hanyar amfani da search). Idan har yanzu kuka kasa samun sa, to ku naimi taimakon masana wayar.
c. Ku zaɓi Private DNS Mode: OFF.
2. Ku kashe manhajar burawuzar Pi (Pi Browser App), sannan ku sake shiga ciki ta hanyar Pi App Menu >>> Pi browser.
Yanzu sai ku sake gwada buɗe pi wallet ɗinku ta amfani da private passphrase ɗinku.
👉 Idan kuka kammala wannan, to a cikin saitunan wayarku (phone settings), ku zaɓi Private DNS Mode: AUTOMATIC
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.