Yaushe Ake Azumin Ramadan

     Yin Azumin Ramadan yana wajaba da É—ayan abubuwa guda biyu:

    1• Ganin watan Ramadan

     ALLAH TA'ALAH ya ce:

    Duk wanda ya tabbatar da tsayuwar watan to ya azumce shi.

     Al-BaÆ™ara ayata:185.

    Idan mutum ya ga watan Ramadan shi kaÉ—ai, kuma shi mutumin adali ne, wanda aka aminta da adalcinsa, to za'ayi aiki da maganarsa ta ganin wata a wajen mafi yawancin ma’abota ilimi.

    Abdullahi ibn Umar (R.A) ya ce:

    Mutane sun ga wata, kuma ni ma na gan shi, don haka, sai na je na bawa Manzon ALLAH {s.a.w} labari, sai Annabi {s.a.w} ya yi Azumi, kuma ya umarci mutane su ma su azumta.

     [Abu Dawud ne ya rawaito].

    2• Cikar Watan Sha’aban Kwana Talatin.

    Idan sama ta yi duhu gajimare ya rufeta a ranar ashirin da tara, ba a ga wata ba, har aka wayi gari ranar talatin ga wata, to wajibi ne a ranar talatin kowa ya É—auki Azumi.

     Abdullahi ÆŠan Umar (R.A) ya ce:

     Manzon ALLAH {s.a.w} ya ce:

    Wata dare ashirin da tara ne, don haka kar ku yi Azumi har sai kun ga wata, idan kuwa sama ta yi girgije, to saiku lissafa kwana talatin.

     [Bukhari ne ya rawaito]. 

    ************************************** 

    Wannan É—aya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Æ˜ur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waÉ—anda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta Æ™arin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.