Yaushe Ne Lokacin Shan Ruwa (Buɗa Baki)

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum malam khamis Muna godiya sosai. Allah ya saka muku da alkhairi Ameen. Tambaya ta a nan shi ne Yaushe ne lokacin buɗa baki (shan ruwa)?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Lokacin buɗa baki ya na tabbata ne da zarar rana ta faɗi.

Dalili kuwa shi ne, hadisin da aka karɓo daga Sahk ibn sa'ad, ya tabbata acikin Sahīhul Bukhārī daga Sahl Ibn Sa’ad ya ce: haƙiƙa Manzon Allah ya ce: Mutane ba zasu gushe tare da alheri ba matuƙar suna gaggauta buɗa baki.

Amma abin mamaki ayanzu sai kaga waɗansu mutane suna jinkirta buɗa baki har sai sunyi sallar magriba.

Haƙiƙa yin haka ba ƙaramin kuskure bane, domin ya saɓawa koyarwar Manzon Allah . Waɗansuma sai kaji su na cewa sai taurari sun bayyana, sannan suyi buɗa baki. Irin waɗannan mutane a tunanin su yin haka shi ne daidai, alhali kuwa ya saɓawa Sunnah, kamar yadda akayi bayani a hadisin daya gabata.

Manzon Allah Yana cewa:

قال رسول الله صلى الله عليه وسلم

ﺑﻜﺮﻭﺍ ﺑﺎﻹﻓﻄﺎﺭ ﺃﺧﺮﻭﺍ ﺍﻟﺴﺤﻮﺭ

[📕ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ.(2835)]

 

Manzon Allah (saw) Ya ce: Ku Gaggauta Shan-ruwa, Kuma ku Jinkirta Sahur.

 

قال رسول الله صلى الله عليه وسلم

ﺛﻼﺙ ﻣﻦ ﺃﺧﻼﻕ ﺍﻟﻨﺒﻮﺓ: ﺗﻌﺠﻴﻞ ﺍﻹﻓﻄﺎﺭ، ﻭﺗﺄﺧﻴﺮﺍﻟﺴﺤﻮﺭ، ﻭﻭﺿﻊ ﺍﻟﻴﻤﻴﻦ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﺸﻤﺎﻝ ﻓﻲ ﺍﻟﺼﻼﺓ

[📗ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ.(3038)]

 

Manzon Allah (saw) Ya ce: Abubuwa Uku Suna daga Cikin ɗabi'un Annabta,

1- Gaggauta Shan-ruwa,

2- Jinkirta Sahur,

3- 'Dora hannun dama akan hagu a Sallah.

Haka hadisin da aka karɓo daga Abdullahi Ibn Abī Auf ya ce: "ya kasance tare da Manzon Allah a lokacin tafiya suna azumi, sai rana ta faɗi, sai Manzon Allah ya ce da wani daga cikin sahabbansa ya sauka ya shirya musu kayan buɗa baki sai, sahabin ya ce: "Ya Manzon Allah da sauran rana, akayi haka har sau uku, Manzon Allah na cewa da shi ya shirya musu abin buɗa baki. Daga ƙarshe bayan sun kammala sai Annabi ya ce: “Idan kuka ga dare ya gabato daga nan (wato rana ta faɗi), haƙiƙa mai azumi ya buɗe bakinsa (ana nufin koya sha ruwa ko bai sha ba)

Bukhari da Muslim  suka ruwaito shi.

Daga Ansa bn Malik(RA) ya ce: Manzon Allah() ya kasance yana yin buɗe baki kafin ya yi sallah da danyen dabino, idan bai samu danyen dabino ba sai ya yi da busassun dabino, idan kuma bai samu busasshen ba, sai ya kurɓi wasu kurɓi na ruwa". Tirmidhi ya ruwaitoshi

ALLAH NE MAFI SANI

Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Fadakarwa  a Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/BpO6i5KwGBm8IcVtlhBr0j

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments