Muƙalar da aka gabatar a ajin ALH 400 (Seminar), a Sashen Harsuna da Al’adu, Jami’ar Tarayya, Gusau, Jahar Zamfara, Nijeriya, (Disamba 2022 - Janairu, 2023).
Zamani Abokin Tafiya: Ƙira Da Maƙeran Ƙarni Na (21) a Garin Talata Mafara
Samir Aminu Musa
Lambar
Waya: 08109474995
Imel: samiraminumusa95@gmail.com
Tsakure
Sana’ar ƙira sana’a ce daga cikin sauran sana’o’in gargajiya na Hausawa, da suke aiwatarwa domim samar wa kansu madogara. Wannan sana’a ta ƙira a kan ta za a waiwaya a ga wace waina zamani ya toya, ko kuma yake toyawa a cikin ta a nan cikin garin Talata Mafara, ta fuskar kayan gudanar da sana’ar da kuma kayan amfani da sana’ar take samarwa. A yayin gudanar da wannan bincike an yi amafani da wasu manya-manyan hanyoyin tattara bayanai kamar bitar ayyakan da suka gabata da kuma tattakawa zuwa wasu maƙerai da ake da su a nan cikin garin Talata Mafara.
1.0 Gabatarwa
Tun ran gini, ran zane, al’ummar Hausawa tun can
asali al’umma ce wadda ta gogara da kanta wajen samar da hanyoyin tattalin arziƙinta. Ba a san Hausawa da kasala
ko ragwanci ba, tun asalatan suka tashi tsaye tsayin daka da yin sana’o’i daban-daban
don wadatar da kansu daga buƙatunsu
na yau da kullum. Ta haka ne har ya zama a kowane gidan Bahaushe za ka tarar yana
da sana’o’in da yake aiwatarwa.
Manufar wannan bincike ita ce, nazarin sana’ar
ƙira a garin Talata Mafara, domin
a ga wane irin ci gaba sana’ar ta zo da shi a wannan zamani da muke ta fuskar kayan
gudanar da sana’ar da kuma kayan amfanin al’umma da sana’ar take samarwa.
A hasashen wannnan bincike, ana sa ran zai fito
da wani sauyi da aka samu a cikin sana’ar ƙira a garin Talata Mafara saboda
ƙarin samun abubuwan kimiyya da
fasaha da ci gaba ya zo da su,
Hausawa suka sami sauƙi
wajen haɓaka tattalin arzƙinsu
1.1 Dabarun Bincike
Domin ɗaure
akuyar bincike da iccen magarya aka yi amfani da hanyoyin tattara bayanai kamar
haka:
i.
Bitar ayyukan da suka
gabata.
ii.
Nazarce-nazarcen bugaggun
litattafai
iii.
Rangadi zuwa masana’antun gudanar
da sana’ar ƙira
a nan garin
Talata Mafara.
2.0 Waiwaye a akan sana’o’in gargajiya
Masana irin su Ibrahim (2007), Ya ce: “sana’a hanya ce ta amfani da azanci da hikima a sarrafa albarkatu da ni’imomin da ɗan Adam ya mallaka don buƙatun yau da kullum. Don haka ke nan sana’a wata
abu ce wadda mutum ya jiɓinci yi da nufin samun
abin masarufi don gudanar da harkokin
rayuwa. Sana’a abu ce wadda ta danganci tono Albarkatun ƙasa da sarrafa hanyoyin kimiyya da fasaha da
ni’imomin da suke tattare da ɗan Adam da sauransu.
Sana’o’in su ne mafi girman Matsayi da Hausawa suke amfani da su don yin dogaro
da kai, su samar da abubuwan da suke buƙata.
Ta hanyar abin da Bahaushe ya samu daga sana’arsa ne yake musanyawa ya mallaki
abubuwan da ba zai iya samar-wa kansa ba.”
Watau sana’a hanya ce ta tsururin arziƙi da al’umma suke biya lungu da saƙo dare da rana domin haɓaka
tattalin arzƙinsu.
Musamman al’ummar Hausawa
da yake sun daɗe suna yin fafutikar neman na kai domin kar
a gani ga tsara. Kamar yadda aka sani Hausawa suna da ire-iren sana’o’in da
suke aiwatarwa, ko da yake ba a iya ƙayyade
adadin nau’ukan sana’o’in Hausawa na gargajiya, amma daga cikinsu akwai:
(1)
Sana’ar
Ƙira
(2)
Sana’ar
Fawa
(3)
Sana’ar
Noma
(4)
Sana’ar
Farauta
(5)
Sana’ar
Gini
(6)
Sana’ar
Rini
(7)
Sana’ar
Kiyo
(8)
Sana’ar
Su
(9)
Sana’ar
Dukanci
(10)Sana’ar Wanzanci. Da sauransu.
2.1 Ma’anar
Sana’ar Ƙira
Malamai irin su Zarruƙ da Al- Hassan (1987), sun bayyana ma’anar ƙira cewa: “sana’a ce da ake sarrafa ƙarfe ta hanyar narka shi cikin wuta sannan a
fito da narkakken ƙarfen a
bubbuge shi zuwa sifar da ake so ya zama.”
Haka kuma an ruwaito a cikin katafaren Ɗakin Karutun nan (rumbun ilimi), “sana’ar ƙira sana’a ce da ake sarrafa tama da ƙarafa, zinariya ko azurfa, da sauran
dangogin ƙarfe a
mayar da su abin amfani wanda ka iya zama makami ko ma’aikaci abin yin sana’a.”
Gusau da Bello (2012), sun ce: “ƙira ita ce ƙera
abubuwa kamar kayan doki ko kayan noma,
kayan yaƙi
misali sulke da takobi da mashi da sauransu.
Maƙera
su ne masu aikin ƙira
maƙeri
kuwa mutum
ɗaya ke nan, maƙera kuma ana nufin wurin da ake yin
ita ƙirar.
Akwai maƙeran
fari waɗanda suke aiki da
azurfa da
tagulla da jan ƙarfe
da zaiba da goran ruwa da dalma
da gaci da taba. Suke ƙera ƙananan
kaya irin na adon
mata kamar zobe da munduwa da kayan dawaki da
sauransu.
Kuma akwai maƙeran
baƙi,
waɗanda suke ƙera
kayan noma da yaƙi da na fawa da na aski da sauran
sauran sana’o’i.
Maƙera
masu ƙarfi
ne ga kuma jimirin zafin wuta,
har ba su kulawa da ita in suna cikin aikinsu.
Wannnan sana’a tana da sarki wanda yake shi ne
shugaban duk wani maƙeri na wannan nahiyar ana
kiransa sarkin maƙera, galibi hakimi ko sarkin gari ke
naɗa
shi. Don haka ne kowace ƙasa
ko gari da nata
sarkin maƙera.
Maƙera
sukan yi ƙira
da ƙarafa
daban-daban,
kamar zinariya da azurfa da gaci da farin ƙarfe da
baƙin
ƙarfe
da jan ƙarfe
da sanholama da dalma
da tagulla da zaiba da sauransu.
Daga nan kuma sai kayan aikin maƙera daga
cikinsu a akwai zuga-zugan da ake hura wuta da
su
da gawayi da masaba ta bugun ƙarfe da hama da
muntalaga
da hantsaki ko awartaki da uwar maƙera
da sauransu.
Lokacin ƙira
maƙeri
zai zauna maƙera
tun da farko
zai sa gawayi ya hura zuga-zugi, sai ya saka ƙarfe
cikin wuta idan ya yi ja, sai ya fitar da shi
ya riƙa
bugawa da masaba bisa uwar maƙera ya sarrafa
ƙarfen
yadda yake so. Tare da taimakawar sauran
kayan aikinsa, zai ƙera dukan abin da yake so
kamar garma ko fartanya da makamantansu. Idan
maƙerar
farin ƙarfe
ce ana amfani da waɗannan
kaya domin ƙera
kayan ƙawar
mata wato azurfa
ko tasa ko zinariya ko tagulla ko dalma.”
Daga waɗannan
ma’anoni da masana suka bayar ake iya fahimtar cewa sana’ar ƙira sana’a ce da ake cin gajiyar ta, ta hanyar
amfanuwa da abubuwan da masu aiwatar da sana’ar ke samarwa na amfanin yau da
gobe. Sana’a ce da take samar da kayan da ake amfani da su domin bunƙasa tattalin arziƙi kamar noma, kare kai kamar takobi da mashi
da sauransu.
3.0 Tarihin
Ƙasar
Talata Mafara
“Mafara
Garken Haɗo Tamode Me Kamar Yau Sallah”
Akwai bayanai da yawa a game da tarihin
asalin mutanen Mafara. Amma dai abu ne da babu saɓani
ga malaman tarihi cewa, Mafarfari suna daga ƙabilar Zamfarawa. Su kuwa Zamfarawa suna da’awar cewa su maguzawa ne, kuma mafarauta waɗanda
suka samo asali daga
Kano. Da suka baro Kano sun zauna a wani wuri da ake ce ma Dutse a kusa da
garin Zurmi. Daga baya kuma suka gina Birnin Zamfara wanda ya faɗa
hannun Gobirawa a bisa ga yaƙe-yaƙe.
A
game da kalmar Talata Mafara wadda take ita ce sunan garin an haɗa
wannan ne a kan kalmomi guda biyu. Ɗayar
ita ce “Talata” guda kuwa ita ce “Mafara.” Kalmar Talata sun ce tana da alaƙa da Kasuwar garin, domin kasuwar ta kasance
tana ci ne, a ranar Talata kowane mako. Kuma mutane daga sassa daba-daban na
cikin Najeriya da wajen ta suna kwararowa zuwa gare ta. Ɓangare na biyu na sunan, watau Mafara sun ce
asalin kalmar ita ce Mafarau. Wannan suna kodai ya kasance suna ne na unguwar
da suka taso daga gare ta a can Kano ko ya kasance suna ne na ƴaƴan
wani sarkin nasu. Matanen Mafara kafin su zauna garin Talata Mafara sun zauna a
wurare daban-daban daga cikinsu akwai Tsaraka. Wannan gari ana ganin muhallinsa
na tsakanin tsohon garin Maradun da Ƙauran
Namoda.
3.1 Sana’ar
Ƙira
a Garin Talata Mafara
Talata
Mafara Hausawa ne kamar sauran Hausawa su ma, ana aiwatar da wannan sana’ar ta ƙira tun gabanin zamani ya zo akwai masu
gudanar da wannan sana’a kuma ita ce hanyar cin abincin su. Su yi aure, su
haihu har su aurar babu mai jin asirinsu. Sana’ar ƙira a garin Talata Mafara kamar sauran
garuruwan Hausawa su ma, suna da ire-iren maƙerai kashi biyu watau ƙirar fari, da ƙirar baƙi.
To
wai mice ce ƙira? Wannan tambaya an fuskantar da ita zuwa ga
wani mai aiwatar da sana’ar inda ya bayyana cewa: “sana’ar ƙira wata abu ce wadda ake sarrafa ƙarfe domin ya bayar da ma’ana, a samar da abin amfani kamar hauya,
galma, kwashe, sungumi, da sauransu.” Tattaunawa da Altini Maƙerin Baƙi, (25-12-2022, 11:30am).
Watau
sana’ar ƙira sana’a ce da ake samun ƙarfe ko tama a sanya shi cikin wuta bayan ya
yi ja, a fito da shi a ɗora a akan uwar maƙera a riƙa bugun sa har ya kasance abin da ake so ya
kasance.
Haka
kuma wani maƙerin fari
ga abin yake cewa: “Ba wani abu ba ne ƙira
face wasu hikimomi ne da ake amfani da su a sarrafa ƙarfe a mayar da shi wani abu na ado kamar azurfa,
tagulla, ƴan kunne,
sarƙa, ko kuma kayan adon doki kamar algaita, da
likkafa, ƙaraurawa da
sauransu.” Tattaunawa
da Ɗan barau maƙerin fari, (24-12-2022, 5:30pm).
Bugu
da ƙari ya bayyana cewa ita wannan sana’a ta ƙira a nan garin Talata Mafara tana da shugaba kamar sauran garuruwa,
sarkinta kuwa shi ne Malam Yahaya amma ya rasu wata uku da suka shige.
Ya ƙara ba da haske cewa ƙirar
fari ita ce ake kiran shugabanta da sarki amma ƙirar baƙi ana ce wa shugabanta mazuga.
3.2 Kira
Jiya a Garin Talata Mafara
Kamar
yadda Altini maƙeri ya
bayyana cewa “Ƙira a jiya
ana amfani ne da wasu kayan gudanar da sana’ar waɗanda
a yau ko dai an daina amfani da su ko kuma an rage amfani da su. A jiya ana
amfani da “tama” shi wannan wani dutsi ne da shi ake samar da kayan gudanar da ƙira kamar guduma da awartaki da mulgu, ana
sanya shi cikin wuta bayan ya yi ja, sai a fiddo shi a riƙa bugun sa har a warwatse shi”
Shi
kuma Jamilu maƙerin fari
ya bayyana cewa: “a lokacin
kafin a sami dabarar yin amfani da gyare to zuga-zugi ne ake hura wuta da shi
wanda kuma shi zuga-zugi ɗin nan ba
kowa ba ne yake iya hura ma wuta da shi yadda ake buƙata face wanda ya gaji sana’ar ko kuma wanda yake maƙwabcin maƙeri ne kuma yana zama akai-akai yana ganin
yadda ake yi to, irin waɗannan suna
iya hura ma wuta da shi.”
3.3 Kayan
Gudanar da Ƙira
Mafi
yawan kayan da ake gudanar da ƙira
a jiya duk da har yau ana samun wasu daga cikin su ana amafani da su, ba a
daina ba irin waɗannan kaya sun haɗa
da:
1)
Zuga-zugi:
wani abu ne da ake yin shi da fatar awaki bayan an jeme fatar a sanya mata ƙota da ita ake hura wuta.
2)
Uwar
maƙera: ƙarfe ne dunƙulalle ake
kafewa a kan shi ake bugun karfen da ake son sarrafawa.
3)
Masaba:
Abin bugun ƙarfe ce da
ake yin ta da zallar ƙarfe.
4)
Awartaki
ko Araftaki: Ƙarfe ne ake
yin sa don ɗauko ƙarfe daga wuta.
5)
Majayi:
Shi ne ake jawo gawayi da shi ana yinsa da rodi a yau.
6) Guduma: Ƙarfe ne ake yi masa ƙota. Da ita ake dukan ƙarfen da ake son ƙerawa bayan an ɗora
shi a kan uwar maƙera.
7) Ƙarfe: Shi ake ƙerawa.
8) Gawayi: Shi ne makamashin wuta.
9) Tama: Sinadari ne da ake yin kayan aiki
da shi.
10) Kasko: Ana zuba ruwa a ciki da wasu
lokutan ake tsoma ƙarfen da
ake son rage zafinsa.
11) Kurfi: Da shi ake sara ƙarfe.
12) Gizago: Ana sassaƙe ƙota da shi idan buƙatar
hakan ta taso.
13) Matsoni: Da shi ake yin huda (ƙofa) a jikin ƙarfe.
14) Madashi: Da shi ake huda ƙota bayan an saka shi a wuta ya yi ja.
3.4 Kayan Amfanin Al’umma da Sana’ar ke Samarwa
A ɓangaran
maƙeran baƙi suna samar da kayan amfani kamar irin su:
1)Hauya
2)Kwashe
3)Galma
4)Laushe
5)Maƙwarƙwasa
6)Takobi
7)Adda
8) Munjagara
9) Aska
10) Huƙa
11) Gatari
12)Magini. Da sauransu
A ɓangaran
maƙeran fari suna samar da kayan amfani kamar
haka:
1)Sarƙa
2)Ƴan kunne
3)Ƴan hannu
4)Zobe
5)Algaita
6)Ƙaraurawa
7)Likkafa
8)Linzami. Da sauransu
4.0 Tasirin
Zamani A Kan Sana’ar Ƙira
a Garin Talata Mafara
Masu
iya magana kan ce “ Zamani rigar doli a saka ki a huta” shi zamani riga ne idan
ba a saka ba to, sai a ga mutum tsirara. A lokacin da ake tattaunawa da wani maƙeri wanda zamani ya yi tasirin a kansa da
sana’ar da yake yi ta ƙira, ya
bayyana cewa “ Yanzu ƙira ta sami sauye-sauye ta fuskar kayan
gudanar da sana’ar da kayan
amfanin al’umma da
sana’ar take samarwa. Domin a halin yanzu ana ƙera tasa wadda ake niƙa ko malkaɗe
da ita, da injimin niƙar
shinkafa, injimin niƙar hatsi
kamar gyero dawa, da injimin niƙar
kara kamar karan dawa domin a ba
shanu su sami abinci.” Tattaunawa da Muhammad Sani, (24-12-2022, 11:30am).
Haka
kuma Ɗan Barau ya bayyana cewa “Yanzu ci gaban da
suka samu har ta kai yanzu ba sai sun yi amfani da gyare ba a wajen zuga kamar
ma wani tsohon ya yi ne, saboda yanzu suna amfani da wutar lantarki da wasu
kayayyaki da zamani ya zo da su sai su riƙa haɗawa domin su huta da samun mai yi musu hurin
wuta yayin da suke gudanar da aikinsu.” Abubuwan da suke amfani da su sun haɗa
da:
Ø Fanka: Ita wannan fanka ta rediyo ce suna
amfani da ita ta hanyar haɗa ta da
wata waya sai a jona ga wuta sai ta zama a maimakon yaron da zai riƙa hura wuta idan ana aiki.
Ø Sola: Ita sola tana zama maimakon wutar
lantarki ne watau idan ba wuta suna amfani da ita ana laƙo ta ne a saman rufin ɗaki
inda rana ke fuskantar ta.
Wannan dai yana nuna irin tasirin da zamani
ya yi a kan sana’ar ƙira a garin
Talata Mafara.
4.1
Ta Fuskar Kayan Gudanar Da Ƙira
A ɗan
binciken da aka gudanar an ga kayan gudanar da ƙira a yau sun haɗa
da:
1)
Ƙarfe:
Kafin a sami ƙarfe ana
samar da kayan gudanar da sana’ar da wani abu da ake kira “tama” shi wannan wani dutsi ne ake sarrafawa a
samar da kayan aiki. Amma yanzu zamani ya zo da ƙarafa kamar rodi da sauransu, ma’ana yanzu
kayan sun zama duk zalla ƙarfe
ne.
2)
Gyare:
Shi ma wani tasiri ne da zamani ya kawo shi domin kafin a san shi da zuga-zugi
ake yi kamar yadda bayanin sa ya gabata tun a 3.1
3)
Wutar
Lantarki: Wannan yana daga cikin tasirin da zamani ya yi kamar yadda aka
bayyana a cikin 4.0
4)
Almakashi:
Shi ma wannan yana daga cikin kayan da ake iya cewa zamani ya zo da shi a cikin
sana’ar ƙira.
5)
Mawashi:
Shi ma wani abu ne da maƙera
suke amfani da shi domin wasa kayan da aka samar kamar wuƙa, takobi da sauransu.
6)
Durom-durom:
Shi kuwa kamar yadda Muhammad Sani mai ƙirar zamani ya faɗa cewa suna
sawo waɗannan durom-durom daga masu sayar da man juye
da gas da kalanzir (kerosine), suna sarrafa su su samar da kayan amfanin
al’umma kamar tasoshin niƙa
da sauransu kamar yadda aka bayyana a cikin 4.0
7)
Filaya
(plier): Ita ma wannan zamani ya zo da ita kafin a san filaya da awartaki ake
amfani.
4.2 Ta Fuskar Kayan Amfanin Al’umma
A
yanzu an sami ƙari a kan
kayan da ake samarwa domin a yau maƙeran
zamanin nan suna da basirar ƙera
wasu kayan amfanin al’umma kamar irinsu:
1)
Kayan
da ake sanyawa a wajen gine-gine kamar:
Gambuna da tagogi (windows), da kuma kayan
aikin gini kamar baho, sheburi
da sauransu.
2)
Injimoman
niƙa
3)
Baruka
kamar dogon baro da guntun baro
4)
Murahu
5)
Tukwanen
ƙarfe
6)
Gadaje
7)
Kujeri
na ƙarfe
8)
Tasoshi
na suya kamar suyar ƙosai da
sauransu.
9)
Tandodin
ƙarfe domin gashin masa/waina.
Bugu
da ƙari a yau maƙeran fari suna ƙera zobba irin na samari da ‘yanmata masu ɗauke
da sunaye, da sarƙoƙi masu kwalliya irin ta zamani.
Yanzu har ana zuwa a yi sarin irin waɗannan
kaya a yi fatauncin su zuwa wasu wurare. Tattaunawa da Jamilu Maƙeri, (24-12-2022, 6:00pm).
5.0 Sakamakon Bincike
Sakamakon
wannan bincike ga alama bai ci karo da hasashen binciken da aka bayyana a sama
ba. Wannan muƙala ta ci
nasarar gano wasu sauye sauye da sana’ar ƙira ta samu da suka haɗa da:
a.
Kayan
gadanar da ƙira kamar filaya
(plier) wadda kamar yadda aka sani ana amfani ne da awartaki.
b.
An
gano cewa yanzu maƙera suna
amfani da wutar lantarki ko sola ta hanyar haɗawa
da wasu wayoyi da fankar rediyo a samar da iska.
c.
Bugu
da ƙari an gano cewa yanzu maƙera suna yin aiki tare da masu walda ta
zamani domin an ce in dambu ya yi yawa ba ya jin mai suna samar da kayan amfani
kamar injimin niƙar hatsi da
kujerin ƙarfe da
sauransu.
d.
Haka
kuma an gano yanzu ƙarfe ne
zalla maƙera suke
amfani da shi a maimakon tama wanda aka san cewa shi dutse ne.
5.1 Kammalawa
Kamar yadda aka gani sana’ar ƙira sana’a ce da take daɗaɗɗiya mai tsohon tarihi a ƙasar
Hausa. Kuma hanya ce ta gwagwarmaya da faɗi-tashi da
Hausawa suke nema domin samar wa kansu mafita daga wasu matsalolin rayuwa.
Manazarta
C.B.T.T.M. (2008). Talata Mafara Jiya Da Yau.
Gusau, S. M., & wasu. (2012). Gusau Ta Malam Sambo.
Century Research and Publishing
Limited.
Abuja Kano Kaduna Lagos
Zariya. https://www.rumbunilimi.com.ng|
Yahaya, I. Y., (2007). Darussan
Hausa, Don Manyan Makarantun Sakandare,
Littafi Na Uku University Press
Ibadan.
Zarruƙ, R. M.,
& wasu. (1987). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don
Makarantun Sakandare Littafi Na
biyu.
University Press Ibadan.
Tattaunawa da Altini Maƙerin
Baƙi a Ranar 25/12/2022, a Garin Talata Mafara,
Ƙaramar Hakumar Jahar Zamfara Nageriya.
Tattaunawa da Ɗanbarau
Maƙerin Fari a Ranar 24/ 12/2022, a Garin
Talata Mafara, Ƙaramar
Hukumar Zamfara Najeriya.
Tattaunawa da Jamilu Maƙeri
a Ranar 24/12/2022, a Garin Talata Mafara,
Ƙaramar Hukumar Zamfara Najeriya.
Tattaunawa da Muhammad Sani a Ranar 24/12/2022, a Garin Talata Mafara,
Ƙaramar Hukumar Jahar Zamfara Najeriya.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.