𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alykum, Idan mata suna jam'in sallah shin limamiyarsu za ta jiyar dasu katarun fatiha da sura (awajen bayyanawa)? za ta bayyana kabbarori yadda za ta jiyar da su? kuma zasu haɗa ƙafafuwansu a sahu kamar yadda maza suke?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikum assalam, Babu bambanci tsakanin sallar mace da
ta namiji a zance mafi inganci, saboda babu nassoshi yankakku waɗanda suka
bambanta, don haka in mace ta yiwa mata limanci za ta jiyar da su karatu kamar
yadda namiji yake jiyar da mamunsa maza, za su haɗa sawu saboda
zukatansu kar su saba.
Idan mace ta limanci 'yan'uwanta mata za ta tsaya ne a
tsakiyarsu, in har ya zama akwai maza a kusa waɗanda ba muharramai
ba, macen za ta iya yin kasa da muryarta saboda kada su fitinu da ita.
Allah ne mafi sani.
Amsawa✍🏻
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/LMfHgWHKrUG9c16dKf9ZBH
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.