Bayani A Kan Sallar Dare (Ƙiyamul Laili)

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum warahmatullahi wabakaratuhu, ina fatan kowa yayini lafiya, malam Allah ya ƙara basira, dan Allah ina son karin bayani a kan sallar dare (ƙiyamullaili). na gode.

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikumus Salámu, 'yar uwa Ƙiyamul Laili shi ne Bahaushe ke ce masa sallar dare, wato ƙiyamul laili ibada ce da ta ƙunshi sallolin nafila da karatun Alƙur'ani da kuma sauran zikirori daga bayan sallar Isha'i har zuwa ketowar Alfijir. a kan kira shi da 'Attahajjud' idan ya kasance sai bayan an yi barci an farka sannan aka yi sallar.

    Yin sallar dare (ƙiyamul laili) yana da falala mai yawa da Allah Ta'ala ya keɓance shi da su kamar yadda ayoyin Alƙur'ani da ingantattun hadisan Manzon Allah suka tabbatar. Daga ciki akwai aya ta ɗaya zuwa ta huɗu da ke cikin suratul Muzzammil.

    Ƙiyamul Laili ba shi da adadin raka'o'i ƙididdigaggu da dole a kansu ake tsayawa, idan da mutum zai yi raka'o'i hamsin ko fiye da haka, sannan ya kammala su da wutiri, to babu laifi, Ibnul Ƙaɗɗan Alfaasiy ya hakaito cewa:

    " Malamai sun yi ijma'i a kan cewa babu iyaka a sallar dare, lallai ita nafila ce, duk wanda yaso ya yi sallar yadda yaso, ya yi da yawa ko ya yi kaɗan".

    Duba Al'iƙná'u Fiy Masá'ilil Ijmá'i (1/174).

    Sai dai abin da ya fi shi ne mutum ya yi wutiri da adadin da Manzon Allah ya yi, wato raka'a goma sha ɗaya, ko goma sha uku, yana yin sallama a kowace raka'a biyu, sai kuma ya yi wutiri da raka'a ɗaya, kamar yadda hadisi mai lamba ta 749 ya bayyana hakan a cikin Sahihu Muslim. Wannan adadi shi ne mafifici.

    Kuma mafificin lokacin wutiri shi ne ɗaya bisa uku na ƙarshen dare, amma idan mutum ya yi wutirin a farkon dare, ko a tsakiyarsa to babu laifi.

    Allah S.W.T ne mafi sanin daidai.

    Jamilu Ibrahim, Zaria.

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/Lvn6zKswf8M8cnTnYUgƘny

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.