Gareku Mata Da 'Yammata

    Ana samun wasu daga cikin mata waɗanda basa tsoron ALLAH,

    Wanda suke aikata zina su sami ciki, bayan sun haife cikin, sai su kuma su jefar da abin da suka haifa a bola ko a wani gurin wai saboda basason suji kunyar duniya,

    Shin bakusan me ake kira da ranar Alƙiyama ba, bakusan rana ce da kowa zaizo gaban ALLAH tsirara ba, uwa da uba, kaka da jika kowa tsirara zaizo wani baya gane wani.

    Wasu kuma sai suyi watsi da 'ƴa'ƴan nasu a gari su zama ƴan iskan lungu koma su zama ƴan daba ko ƴan fashi koma me zasu zama iyayen nasu basu damu ba, sudai kawai sun haifa ta hanyar haram sun kuma sakesu agari suyita tara musu zunubai.

    To ku sani akwai yaron da za a haifa ta hanyar haram, daga ƙarshe ya zama sanadiyyar shigar da shi kansa da iyayen Aljannah,

    Sai kuma kaga wanda aka haifa ta hanyar halal yajawowa kansa da iyayensa shiga wuta.

    Idan kika haifi yaro ko yarinya ta hanyar zina, daga baya kikayi nadamar abin da kika aikata, kika tuba wa ALLAH tuba mai kyau, kuma kika kula da abin da kika haifa har ya sami tarbiyya ya girma ya zama mutumin kirki ya bi ALLAH, harya koma ga ALLAH yana mai bin ALLAH a sanadinsa kedashi sai ku shiga Aljannah cikin sauƙi.

    Amma akwai da yawa yaran da aka haifesu ta hanyar halal su ne suke jawa iyayensu da su kansu shiga wutar ALLAH.

    Ina kira gareku iyaye mata duk wacce aka jarabceta da irin wannan ƙaddara mara kyau, kada ta yadda yaronta a bola, kada kuma ta wulaƙantashi a gari,

    Ta tuba wa ALLAH, kuma kada ta sake komawa laifin, ta kuma riƙe yaronta hannu biyu, ta bashi tarbiyya, ALLAH zaisa yaji ƙanta yaji ƙan Al'umma.

    Sannan kuma kada ki saurari maganganun mutane domin basu da wuta basuda Aljannah,

    Ba mamaki ma wani gurin boka yake zuwa, ke kuma iya yaro kika haifa ta hanyar zina, shi kuwa da yake zuwa wajen boka ya kafirta, amma a haka zaizo yana goranta miki, kada ki damu ALLAH mai rahma ne.

    Don haka a daina zubar da ciki, adaina zubarda yara a bola ko a gari, idan an samesu ta hanyar haramz kada a wulaƙantasu, a tuba wa ALLAH lallai ALLAH mai yawan rahma ne, yana gafarta zunubin da ya fi hakama.

    ALLAH TA'ALAH ka gafarta mana zunubanmu baki ɗayanmu.

    ALLAH ka bamu ikon aiki da abin da muka karanta. 

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.