Gulma Na Jawo Asarar Lada A Lahira

    Ke da kike shiga ta mutunci kullum, kina cikin hijab ko da yaushe, bakya wasa da zuwa makaranta, ga hadda, ga kiyaue sallah, ga iya zaman aure, ga biyayya ga miji, kuma kina girmama iyayenki da maƙobtanki,

    Amma kullum sai kinyi gulmar wance da wane, ai wance karuwa ce, ai wance ƴar Lesbian ce, ai wance ɓarauniya ce, ai wance kaza da kaza takeyi, to sai an wayi gari ita, ta shiga Aljannah ke kuma kin shiga wuta.

    Domin ke ana ɗibar ayyukanki ne na alkhairi ana bata, a yayin da zatazo filin hisabi a ganta da tarin ayyukan lada, alhalin ba ita ta yi aikin ba anan duniya,

    Amma saboda an kwasosu ne daga mai gulmarta, nan kuma ga ayyukanta na zunubi, ga kuma tarin lada, idan a kaga ladan ya fi zunubin yawa, sai a tura ta Aljannah a yafe mata zunuban na ta.

    Ke kuma kinyi wahalar banza anan duniya anturaki wuta, an bawa wata dukkan naki ladan.

    To kaima da kake zagin wane da wane, kana cewa ai wane baida aiki sai zina, ko ɓarawo ne, ko baida aiki sai zaman banza, kai kuma kana sallah a kan lokacin, haka kaima za ka shiga wuta shi ma ya shige Aljannah.

    Don haka mu kiyaye harshensu daga zargi da zagin mutane, mu kiyaye harshenmu daga gulmar mutane domin za ta jawo mana asarar ladanmu a ranar Alƙiyama.

    ALLAH ka bamu ikon aiki da abin da muka karanta.

    ALLAH ka yafe mana zunubanmu baki ɗayanmu Ameen

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.