Da yawa daga cikin mata sukan sami rikicewa jinin al'adarsu, wata a dalilin canjin abinci, wata a dalilin canjin yanayi daga sanyi izuwa zafi, wata kuma tana kwana a ɗaki mai AC sai kuma ta sami canjin guri.
Wata kuma a dalilin Allurar planning ko saka roba, wata kuma haka kawai sai ta ga jinin yana ɗigo mata ɗan kaɗan saita sami kokonta akan azuminta ko sallah ko wanin haka.
Wata kuwa zata haihu tacika kwana arba'in ɗinta amma kuma sai
ta ga jinin bai ɗauke mata ba, har ta wuce adadin kwanakin da jinin
haihuwa yake yi.
Duk wacce ta sami kanta a ɗaya daga cikin
irin wannan matsala abinda zatayi shi ne:
Farko idan kika ga jini yazo miki ba'a lokacin da kika
saba al'adarki ba, to saiki fara duba kalar jinin da ƙarninsa
kiga shin kalarsa da ƙarninsa sunzo iri ɗaya sak da asalin
jinin hailarki.
Idan kalarsa da ƙarninsa sunzo iri ɗaya sak, to jinin
haila ne, zaki tsaya da yin azumi da sallah harsai sanda ya ɗauke.
Idan kuwa kalarsa da ƙarninsa
basuzo iri ɗaya ba, to koma me kika gani, ko brown ko kalar ruwan ƙwai, ko wata kala daban, to wannan yana ɗaukar hukumcin
jinin istihadha ne, wato jinin ciwo, shi kuma jinin ciwo baya hana dukkan
ibadah.
Sai dai idan yana zuwa mata zuwan da ya wuce misali sai
aje aga likita, domin neman magani.
ALLAH shi ne mafi sani.
ALLAH ya karɓi ibadunmu.
Duk mai neman ƙarin bayani ayi mana magana ta private.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.