𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Ana Bina Sallar Isha'i Sai Na zo Masallaci Natarar Ana
Sallar Asuba, Zanbi Jam'in Asuba Ne Bayan Na gama Sai in yi Isha'i, Kosai na yi Isha'i Sai in yi Asuba?.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wajibi ne jerantawa wajan ramuwar sallar da ta wuce mutum amazhabar jamhur din
malamai.
Ibnu ƙudama Allah yajiknasa darahma a cikin Almugniy ( 1/352) ya ce: Adunkule wajibi
ne jerantawa wajan ramuwar sallolin dasuka wuce mutum.
Imamu Ahmad yafadi hakan agurare da dama, da naka'iy da
zuhuriy da rabee'ah, da yahyal Ansary da Malik, da lais da Abu hanifah, da ishaƙ.
Imamu shafi'i ya
ce: Bawajibi bane domin ramuwar sallar da ta wuce ba wajibibane jerantasu,....
kamar azumi idan jerantawa yatabbata to wajibi ne jeranta azumi ko da mai
yawane, Ahmad yafadi haka a wani wajan.
Abu hanifa da Malik suka ce: Badole ba ne jeranta
sallolin ba idan wacce takubecewa mutum sun haura sallar dare dawuni ɗaya, saboda lura
dacewa abunda yakaru a kan sallolin
dare dawuni zaiwa mutum wahala, zaikuma cigaba damaimaitawa, saboda haka
jerantawa tafadi akansa, kamar jerantawa wajan rama azumi.
Jerantawa wajibi ne awajan jamhur din Hanafiyyah da
malikiyyah da hanabila, sai dai Abu
hanifa da malikiyyah basa wajabta jerantawa idan ramuwar sallar yakaru a kan sallolin
wuni dana dare.
Yanda ake jerantawar shi ne mutum ya zo da sallar ayanda jerangiyarsu take, misali wanda azahar da
la'asar suka kubuce masa, to inyazo ramasu zaifara yin azaharne sannan sai ya yi la'asar
Sai dai wajabcin jerantawa
yana faduwa a kan mutum abisa mantuwa ko rashin sani kokuma tsoran fitar
lokacin sallar da lokacinta yake bai fitaba, dakuma tsoran kubucewar jam'i
abisa Zance mafi rinjaye.
Misali idan ana binka salloli biyu, azahar da la'asar
saikafara yin la'asar kafin azahar abisa mantuwa korashin sani wajabcin
jerantasu sallarka ta yi babu komai
akanka.
Ko kuma kanajin tsoran fitar lokacin sallar la'asar
muktari zaifita kafin kai azahar, zakayi la'asar daka baya kayi azahar ɗin.
Haka da za ka shiga masallaci katarar an tayarda jam'in
sallar dalokacinta yake.
Shin za ka fara
sallar ramuwane kozakabi jam'in wacce ake yi?
Imamu Ahmad awata ruwaya daka gareshi wacce shaikul Islam
ibnu taimiyyah yazaba cewa jerantawa yafadi a kan mutum idan yana tsoran rasa jam'i.
Sai dai alokacin mutum zaibi,
jam'i daniyyar rama sallar wacce ake binsa, kamar wanda ake binsa sallar azahar
saiyatarar ana jam'in la'asar zaibi jam'in daniyyar azahar, ban-banci niyyarsa
da ta limaminsa bazai masa komaiba, idan aka idar sai ya yi la'asar ɗin.
Sharhin mumti'i Ala zadul mustaƙni'i (
2/138-144)
WALLAHU A'ALAM
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/BXjuXb1WxX99NV3OsXPnLV
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.