Ticker

    Loading......

Hukuncin Jinkirta Wankan Janaba Zuwa Bayan Ketowar Alfijir

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalmu alaikum, malam ina da tambaya shin Meye hukuncin matan da za su sadu da mijinsu lokacin azumi, amma ba za su yi wanka ba har sai alfijir ya fito, shin yaya matsayin azumin su yake.? Na gode.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikum assalam, ya halatta mace ta sadu da mijinta su jinkirta wanka zuwa bayan ketowar alfijir a Watan Ramadan, a zuminsu kuma ya inganta, saboda Annabi S.a.w yakan yi haka da matansa, kamar yadda Iyalansa A'isha da Ummu Salama suka rawaito hakan, kuma Muslim ya fitar da riwayar a Sahihinsa a hadisi mai lamba ta: 1874.

Allah ne mafi sani

Amsawa: Dr. Jamilu Zarewa

Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Fadakarwa  a Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Cnf26Ƙ8MPƙz9yUYU1nxƙRƙ

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments