Hukuncin Mace Ta Yi Wa'azi Ga Maza

     𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamualaikum warahmatullahi. Malam ina da tambaya? shin yakamata mace tafita gaban maza tana wa'azantarwa?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuh. Alhamdu lillahi rabbil alamin wassalatu wassalamu ala rasulillah wa ala alihi wa sahbihi ajma'in.

    Asali abin da ya fi dacewa kuma aka fi so, shi ne namiji ya koyar da maza, mace ta koyar da mata, ta wa'azantar da su, saboda kulle kofar ɓarna, da za ta iya saka sashe su ya fitinu da sashe, wanda hakan sai ya haifar da lalata ko makamancin haka. Idan ba haka ba, mace na iya wa'azi ga namiji kamar yadda namiji na iya wa'azi, wannan shi ne asali. Allah yace

    وَلۡتَكُن مِّنكُمۡ أُمَّةࣱ یَدۡعُونَ إِلَى ٱلۡخَیۡرِ وَیَأۡمُرُونَ بِٱلۡمَعۡرُوفِ وَیَنۡهَوۡنَ عَنِ ٱلۡمُنكَرِۚ وَأُو۟لَـٰۤىِٕكَ هُمُ ٱلۡمُفۡلِحُونَ

    MA'ANA: Kuma wata jama´a daga cikinku, su kasance suna kira zuwa ga alheri, kuma suna umurni da alheri, kuma suna hani daga abin da ake ƙi. Kuma waɗannan, sũ ne mãsu cin nasara.

    [Surah Aal-E-Imran 104]

    Ayar ba ta iyakance jinsin da mai wa'azi zai kira ko ya yi ma nasiha ba, kamar yadda bata ambaci maza ba kaɗai a fagen masu da'awa ba.

    Amma idan hakan bai samu ba, toh babu laifi mace ta yi wa'azi ga maza ko namiji ya yi wa'azi ga mata, kamar yadda muka gabatar, sai dai da sharaɗin idan hakan ba zai haifar da fitina ba, kuma babu wani zaɓi sai hakan.

    Don haka eh, ya kamata mace ta yi wa'azi ga maza, idan za ta nisanta daga gare su, za ta nisanci yin amfani da murya mai janyo hankali ko haifar da sha'awar ta. Allah yace

    ... فَلَا تَخۡضَعۡنَ بِٱلۡقَوۡلِ فَیَطۡمَعَ ٱلَّذِی فِی قَلۡبِهِۦ مَرَضࣱ وَقُلۡنَ قَوۡلࣰا مَّعۡرُوفࣰا

    MA'ANA: ...kada ku sassautar da magana, har wanda ke da cũta a cikin zuciyarsa ya yi ɗammani, kuma ku faɗi magana ta alheri.

    [Surah Al-Ahzab 32]

    Bayan haka sai idan za ta ɓoye adon ta daga ganin masu sauraro, ma'ana ta lulluɓe jiki da kwalliya ta, kuma za ta sauke ganin ta kamar yadda Allah ya ce:

    وَقُل لِّلۡمُؤۡمِنَـٰتِ یَغۡضُضۡنَ مِنۡ أَبۡصَـٰرِهِنَّ وَیَحۡفَظۡنَ فُرُوجَهُنَّ وَلَا یُبۡدِینَ زِینَتَهُنَّ إِلَّا مَا ظَهَرَ مِنۡهَاۖ....

    MA'ANA: Kuma ka ce wa mũminai mãta su runtse daga gannansu, kuma su tsare farjõjinsu kuma kada su bayyana ƙawarsu fãce abin da ya bayyana daga gare ta...

    [Surah An-Nur 31]

    Don haka dai idan har za’a amintu daga dukkan sabubban fitina da ɓarna ga al'umma, kuma sai idan babu wani Mallami namiji da yake masani a fannin da za ta yi wa'azin, toh shike nan, ya halatta mace ta wa'azantar da maza kamar yadda muka gabatar, idan za ta kiyaye ababen da shari'a ta wajabta a kan ta kuma ta kiyaye mutuncin ta.

    WALLAHU TA'AALA A'ALAM.

     Amsawa :

     Malam Aliyu Abubakar Masanawa

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/LMfHgWHKrUG9c16dKf9ZBH

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.