Hukuncin Zubar Da Cikin Sikila Ko Waninsa

    Malamai sun yi ijma'i a kan haramcin zubar da ciki bayan an busa masa rai, saboda ya zama kashe rai ba da hakki ba.

    Amma sun yi saɓani game da zubar da ciki kafin ya kai wata huɗu, wasu sun haramta, wasu sun halatta wasu kuma sun karhanta.

    Amma abin da yake daidai shi ne ya halatta a zubar da cikin da bai kai wata huÉ—u ba, idan akwai lalura, zubar da cikin.

    Sikila ba dole ya zama lalura ba, tunda ana iya haifarsa ya rayu, ya bautawa ALLAH ya amfani al'uma, don haka barin cikin shi ne yafi, sai dai idan aka zubar kafin ya cika wata huÉ—u saboda matsalar da ake tunanin yaron zai iya fuskanta a rayuwarsa.

    Ko kuma mace tana shayar da yaron da baiyi ƙwari ba, kuma saita sami wani cikin, gashi wanda take shayarwa ya fara shan nonon sabon cikin, sai ya zama yana cutuwa daga nonon, ita ma mahaifiyar tasa tana cutuwa sosai.

    Sannan kuma ba zai yiwu a yaye wanda ake shayarwa ba, saboda ba zai iya cin abinci ba, to shi ma idan an rasa wata mafita, sai an cire cikin, ya halatta acireshi, mutuƙar baikai wata huɗu ba.

    Sannan kuma ba za a ce anyi laifi ba, tunda bai zama mutum ba, kuma ba za a tashe shi ranar Alƙiyama ba.

    Domin neman ƙarin bayani duba Ahkamu Al-janin Fil-fiƙhil Islami na Umar Ganam.

    Ko kuma a yi mana magana ta private.

    ALLAH  shi ne mafi sani.

    *****************

    Wannan É—aya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Æ˜ur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waÉ—anda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta Æ™arin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.