Idan Na Riski Daren Lailatul Ƙadri Wacce Addu'a Zan Yi?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum Malam. tambaya na anan shi ne in har Allah ya sa mutum ya dace da daren lai-latul ƙadar wani irin addu'a ya kamata ya yi kuma shi addu'an so nawa ake yi? Kuma shi lai-latul ƙadar ɗin tana da wasu alamomi ne na ganinta?

 Na gode

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Dangane da amsar tambayarka ta farko, akwai hadisi wanda Imamu Muslim da Imam Ahmad da Tirmidhiy da Abu Dawud suka ruwaito daga Sayyiduna Ubayyu bn Ka'ab (rta) cewa shi ya ce : "Ina rantsuwa da Allah wanda babu abin bautawa da gaskiya sai Shi, Hakika shi wannan daren a cikin Ramadana ne. Kuma ina rantsuwa da Allah ni nasan daren da take. Ita ce daren nan wacce Manzon Allah ya umurcemu da Tsaiwarta. Ita ce daren Ashirin da bakwai.

Alamominta kuma, Rana za ta ɓullo a safiyar ranar, fara sol babu tartsatsi gareta.

2. tambayarka ta biyu kuma : Imam Abu Dawud da Tirmidhiy da Ibnu Maajah sun ruwaito daga Nana A'ishah (ra) tace : "Nace "Ya Ma'aikin Allah, shin idan nasan wacce ce daren Lailatul Ƙadari, Mai zan ce a cikinta?". Sai ya ce kice:

اللّٰهُمَّ إِنَّكَ عَفُوٌّ تُحِبُّ الْعَفْوَ فَاعْفُ عَنِّيْ

"ALLAHUMMA INNAKA 'AFUWWUN TUHIBBUL 'AFWA FA'AFU 'ANNEE"

 (Ya Allah kai Mai Afuwa ne, kuma kana son yin afuwa. To kayi afuwa gareni)

Kaima ita wannan addu'ar za ka rika yi kamar yadda Annabi ya koyar.

WALLAHU A'ALAM.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Fc3hX6HoDt65aKhhKOiDpX

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments