Ittikafi 02 - Sharaɗan Ingancin Ittikafi

    Li’itikafi yana da sharaɗan inganci guda bakwai:

    1• Musulunci: Li’itikafi baya inganta ga kafiri.

    2• Balaga: Baya inganta ga yaron da bai balaga ba, ko mahaukaci.

    3• Tsarki: Ba ya inganta ga mai janaba ko haila ko nifasi, sai dai idan janaba ta sami mutum yana cikinsa, sai yayi wankan tsarki.

    4• Masallaci: Li’itikafi baya inganta a cikin gida ko ɗaki ko Masallacin da ba'a sallar jam’i a cikinsa, dole dai indai za'ayishi ya wuce kwana 7 to sai dai ayishi a masallacin juma'a saboda ba'aso maiyinsa ya fita ko ina.

    5• Azumi: Li’itikafi baya inganta ba tare da Azumi ba.

    6• Barin runguma ko sumbatar mace da daddare ko da rana.

    ALLAH {S.W.T} yace: Kar ku rungume su (mata), lokacin da kuke li’itikafi a cikin Masallaci.

    [Suratul Baƙara: ayata:178]

    7• Neman iznin miji: Li’itikafin mace baya inganta idan mijinta baiyi mata izini ba.

    ME KE ƁATA IITIKAFI

    Li’itikafi yana ɓaci don aikata babban laifi kamar: Zina da shan giya da ƙarya da ƙazafi.

     Haka kuma yana ɓaci don yin jima’i da sumbata da daddare ko da rana bisa sha’awa.

     Haka kuma yana ɓaci da zuwan haila, haka kuma yana ɓaci da cin abinci ko shan ruwa da rana, haka kuma yana ɓaci in an fita daga Masallaci ba don neman abinci ko wata buƙatar ɗan’adam ba.

    ALLAH shi ne mafi sani.

    ALLAH ka ba mu ikon aiki da abinda muka karanta.

    ALLAH ka gafarta mana zunubanmu baki ɗayanmu Ameen.

    Duk mai neman ƙarin bayani ya tuntuɓe mu ta private.

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.