Ticker

Littafin Zakka 01 - Zakka Da Hukunce-Hukuncenta

Ma’anar zakkah a shari’ah ita ce:

Fitar da hakkin daya wajaba daga dukiya yayin da takai nisabi ga waɗanda suka cancanta.

Zakkah rukuni ce daga cikin rukunan Addinin Musulunci kamar yadda ya zo a Hadisi:

Zakka ta kasu gida biyu:

1• Zakkah ta jiki (Wato zakkar fidda kai), bayaninta zai zo a nan gaba

2• Zakkar Dukiya.

 DALILAN WAJABCINTA

Zakka wajibi ce da nassin Alƙurani, kamar yadda AlLLAH (S.W.T.) Yace: Ku bayar da Zakkah.

 [Al Bakara Ayata: 110].

Manzon ALLAH {s.a.w} Yace: Da Mu’azu sanda ya tura shi Yemen:

Ka sanar da su cewa ALLAH {S.W.T} Ya wajabta Zakka a kansu, wadda za a karɓa daga mawadatansu, a bayar da ita ga matalautansu.

 [Bukari da Muslim]

 WAƊANDA TA WAJABA A KAN SU

Malamai sun haɗu a kan cewa zakka tana wajaba a kan Musulmi baligi mai hankali.

 Kuma wanda ya mallaki nisabi, tare da cika sauran sharuɗa, amma sun yi saɓani a kan yaro da mahaukaci.

Wasu sunce bata wajaba a kansu ba, wasu kuma sukace tana wajaba.

Amma magana ta biyu ita tafi ƙarfi, saboda hadisai ingantattu da aiwatarwar sahabbai a kan haka.

 Anas (R.A) yace:

Manzon ALLAH {s.a.w} yace:

Kuyi ciniki da dukiyar marayu, domin kada Zakka ta cinye ta.

[Ɗabarani ya rawaito].

[Duba FiKhuz Zakkat juz’i na 1, shafi:95 – 112].

Wannan ya nuna cewa za a fitar da Zakka daga dukiyar yaro data mahaukaci.

 LOKACIN FITAR DA ZAKKA

Lokacin fitar da zakka ya danganta ne da nau’in dukiyar.

Idan zakkar kuɗi da dabbobi, da kayan sayarwace, to sai dukiyar ta shekara, bayan ta kai nisabi.

Amma idan zakkar amfanin gonace, to ana fitar da itane a lokacin da aka girbe ta ko aka tsinke ta.

 Zakkar ma’adanai data zuma kuwa, a wajen mahzahar Hanafiyya, ita ma ana fitar da ita a yayin da aka fito dasu.

 (Duba FiKhul Islami Wa Adillatahu, juz’i na 3, shafi: 1814 – 15)

 SHARADAN WAJIBCIN TA

Dangane da abin da ya gabata, zamu fahimci cewa, tsabar kuɗi da kayan sayarwa suna buƙatar sharuɗa biyar kafin a fitar musu da Zakka.

1• Musulunci.

2• 'Ƴanci.

3• Mallaka.

4• Cikar Nisabi.

5• Cikar shekara.

Idan kuwa Zakkar dabbobi ce, to, sai a ƙara sharaɗi daya, shi ne: kasancewa suna fita kiwo.

Ba aɗaure suke ana nemo musu abinci ba,

wato waɗanda ba atirkesu ba.

Haka kuma idan amfanin gonane, to shi ma sai a ƙara sharaɗi ɗaya, wato ya kasance abinci ne ga ɗan Adam, amma a fitar dashi ne da sharaɗin cikar shekara.

[Duba Al-FiKhul Muyassar na Ahmad Isa, juz’i, 1, sh;220-222]

HUKUNCIN WANDA YAƘI BAYAR DA ITA

Mai ƙin fitar da zakka iri biyu ne:

1• Kodai yaƙi bayarwa ne saboda bai yarda wajibi ce ba.

2• Ko kuma yaƙi bayarwa ne saboda tsananin rowa da son abin duniya.

Idan yaƙi bayarwa ne saboda bai yarda da wajibcinta ba, to ya kafirta.

Idan kuwa don rowa ne, ko sakaci to fasiƙi ne, kuma hukuma za ta iya karɓa ta ƙarfi daga garesshi.

Kamar yadda Khalifan Manzon ALLAH {s.a.w} Abubakar (RA) ya yaƙi waɗanda sukaƙi bayarwa a zamaninsa.

[Duba za katul Ma’adni na Almukhtar bin Umar bin Al-Hussain As-Shankidi Sh:18-19].

Kuma ya kamata mu sani cewa, ƙin bayarda zakka yana jawo azaba mai muni ga mutum a lahira.

Abu Huraira (RA) yace:

Manzon ALLAH {s.a.w} yace:

Babu wani mai k'dukiya wanda baya bayar da zakkarsa, face sai an ƙona kuɗin a wutar Jahannama ya yi faɗi sannan a rinƙa manna masa a geffansa da fuskarsa, har lokacin da ALLAH zaiyi hukunci a tsakanin bayinsa, a yinin da yake kwatankwacin tsawon shekara dubu hamsin.

Sannan a nuna masa hanyarsa, ko dai zuwa aljannah ko kuma zuwa wuta.

Babu wani mai raƙuma wanda baya bayar da Zakkarsu, face sai an jefa shi a cikinsu, a wani kwari mai faɗi cike dasu, sannan su rinƙa bi ta kansa,

Idan suka kai ƙarshe, sai a dawo da na farkon, H'haka za a rinƙa yi masa, har ALLAH ya yi hukunci a tsakanin bayinsa.

A yinin da yake kwatankwacinsa tsawon shekara dubu hamsin.

Sannan sai a nuna masa hanyarsa izuwa Aljanna ko zuwa wuta.

Babu wani mai tumaki ko awaki wanda baya bayar da zakkarsu, face sai an jefashi a cikinsu, a wani kwari mai faɗi, cike da su sannan su rinƙa takashi da kofatansu, suna sukansa da ƙahonsu.

Babu mai tanƙwararren ƙaho a cikinsu, balle marar ƙaho, idan suka kai ƙarshe, sai a dawo dana farkon.

Haka za a rinƙa yi musu, har ALLAH ya yi hukunci a tsakanin bayinsa, a yinin da yake kwatankwacin tsawonsa shekara dubu hamsin.

Sannan sai a nuna masa hanyarsa zuwa Aljanna ko zuwa Wuta.

(Duba Nailul Audar na Shaukani, juz’i 2, shafi na:172-173).

ALLAH kabamu ikon aiki da abin da muka karanta.

ALLAH ka gafarta mana zunubanmu baki ɗayanmu Ameen.

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments