Littafin Zakkah [ 03 ] - Dukiyar Da Ake Fitar Wa Zakka

    Dukiyoyin da ake fitarwa da Zakka kashi biyu ne:

     Akwai waɗanda suke fitattu ne, an san su. Ko dai saboda su ake yawan faɗa a bayanin zakka; ba afaɗar nau’o’in da ke cikin su.

     Ko kuma saboda su babu saɓanin malamai a kansu.

     Akwai kuma waɗanda ba fitattu ba, Ko dai saboda ba ayawan fito da su a bayani, ko kuma saboda malamai sun yi saɓani a kan su.

    FITATTUN DUKIYOYIN ZAKKA

    Dukiyoyin da akafi sani yayin da akayi maganar zakka sune:

    Zakkar kuɗi.

    Zakkar dabbobi.

    Zakkar amfanin gona.

    Zakkar ma’adanai da binanniyar dukiyar jahiliyya.

    Zakkar dukiyar ciniki.

    ZAKKAR KUƊI:

     Asalin kuɗi dai, kamar yadda muka sani, su ne zinariya da azurfa. Ko dinare da dirhami.

    A yanzu kuwa, su ne kuɗaden da ƙasashe kan buga, domin a rinƙa amfani dasu a duk duniya.

    Ko kuma a iya ƙasashen kad'ɗai, kamar dai Dalar Amurka da Nairar Najeriya.

     Malamai sun haɗu a kan wajabcin Zakka a kan zinariya da azurfa, koda kuwa ba abuga su a matsayin kuɗi ba.

     Kamar a ce suna asalin siffarsu, ko an ƙara wani mazubi dasu, ko an yi wani abin ado dasu, bana mata ba.

    Za a fitar da zakka daga zinariya (Gold) Idan nauyin ta ya kai nauyin giram (85).

     Sai a fitar da kashi biyu da rabi cikin ɗari 2.5% Wato a kasa gida arba’in 40 sai a ɗauki kaso ɗaya shi ne zakkar ɗaya cikin arba'in 1/40 shi kuma dinare wato bugagge, idan yakai dinare ashirin, sai a fitar da ɗaya bisa huɗu na dinare ɗaya.

     Ita kuwa azurfa idan nauyin ta yakai giram (595), sai a fitar da kashi biyu da rabi cikin ɗari 2.5% Wato a kasa gida arba’in 40 sai a ɗauki kaso ɗaya shi ne zakkar 1/40.

     Shi kuma Dirhami wato bugagge idan ya kai Dirhami ɗari biyu, sai a fitar da Dirhami biyar.

     Sai dai kamar yadda muka sani, duka biyun wato Dinare da Dirhami yanzu ba aamfani dasu a matsayin kuɗi.

     Don haka abin da musulmi suka yi a ƙasashensu shi ne, sukan ɗauki nisabin ɗayansu ne su kimanta kuɗin ƙasarsu da shi.

     Amma zaifi dacewa ayi kimar da Dinare (Zinariya). Saboda dalilai kamar haka:

    1• Malamai sunce kimar Dirhami tana iya canzawa, daga lokaci zuwa lokaci, ba kamar yadda take a zamanin Annabi {s.a.w} ba, shi kuwa Dinare bai canza ba.

    2• An kwatanta nisabin dinare anga ya fi zama kusa dana dabbobi dana amfanin gona.

    [Duba FiKhuz-Zakat, juz’i na 1, sh:256 – 264]

     Ke nan yadda zakkar dukiya take shi ne idan dukiyarka takai nisabi ko ta huce saika lissafata ka kasa kaso arba’in 40, sai ka fitar da kaso ɗaya daga ciki shi ne zakkar ɗaya bisa arba'in 1/40.

    ALLAH shi ne mafi sani.

    ALLAH ka ba mu ikon aiki da abin da muka karanta.

    ALLAH ka gafarta mana zunubanmu baki ɗayanmu Ameen.


    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.