Mace Za Ta Iya Tafsiri Da Lasifika?

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Mutane da yawa sun tambaye ni a kan hukuncin tara mata a masallaci, mace ta yi musu TAFSIRI da lasifika ?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Annabi Yana cewa : "Duk lokacin da mutane suka haɗu a ɗakin Allah suna kokarin fahimtar littafin Allah, nutsuwa za ta sauka gare su, Mala'iku za su kewaye su, sannan Allah zai ambace su a wajan wadanda suke tare da shi". Muslim (7030).

    Hadisin Ya nuna halaccin mace ta karantar da Alƙu'rani a masallaci, saboda ba a bambance tsakanin namiji da mace ba.

    Sai dai idan mun bi mazhabar malaman da suka inganta hadisin Amru dan Hazm akwai turnuku wajan mace ta yi tafsiri a watan Azumi, Manzon tsira ya ce: "Kar Wanda ya taɓa Ƙur'ani sai mai Tsarki" domin Babu yadda za a yi mace lafiyayyiya mai matsakaitan shekaru, ta kammala Ramadana uku ba ta yi jinin al'ada ba.

    Malaman Malikiyya suna fifita mace ta yi karatun sallah a asirce a sallolin da ake bayyanawa, saboda Annabi ya umarci mata da yin tafi idan liman ya yi rafkannuwa suna tare da maza don kar aji muryarsu, kamar yadda Bukhari ya rawaito, wannan sai ya nuna ba a son mace ta daga muryarta, to ina kuma ga Lasifikar da za ta isar da sakon ga maza, ga kuma 'yan social media a gefe waɗanda za su yaɗa hotunanta da muryarta a duniya ?!!

    Duk da cewa wasu daga cikin mata magabata suna koyar da maza da mata, sai dai ba a bainar Jama'a suke yi ba, wannan yasa yin kiyasi a kan aikinsu ba zai tafi ba, saboda sababi da illar sun yi hannun riga.

    Ayoyi da hadisai sun nuna halaccin yin wa'azi ga mace, sai dai akwai Bambanci tsakanin wa'azi da tafsirin Ƙur'ani, saboda tafsirin Ƙur'ani Yana wajabta taɓa shi yayin nazari da kuma karantarwa, hakan kuma haramun ne ga mai haila bisa hadisin da ya gabata.

    Yana da kyau mata da maza masu yin Tafsiri su yi taka-tsantsan wajan fassara zancen Allah saboda darajar littafin da kuma girman dangantawa Allah abin da mutum ba shi da tabbas.

    Akwai hanyoyi da yawa na samun Lada a Ramadana ban da tafsiri.

    Allah ne Mafi Sani

    Dr. Jamilu Zarewa

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/LMfHgWHKrUG9c16dKf9ZBH

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.