Ticker

    Loading......

Mene ne hukuncin mace ta ƙare haila ba ta yi wanka ba mijin ta ya sadu da ita?

 𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaykum, malam ina da tambaya. Malam mene ne hukuncin mace ta ƙare haila ba ta yi wanka ba mijin ta ya sadu da ita?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikum assalam, Maganar mafi yawan malamai shi ne: ta jira sai ta yi wanka kafin su sadu, kamar yadda suka fahimta a aya ta 222 a suratul Bakara, amma Abu-hanifa yana ganin halaccin haka, saboda ya fahimci tsarki a ayar da yankewar jinin haila kawai.

Riko da mazhabar farko shi ne ya fi saboda Allah ya kira haila da cuta.

Babu wata kaffara ga wanda ya sadu da matarsa kafin ta yi wanka bayan yankewar jinin haila.

Allah ne mafi sani:

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/GUƙ2GCCzlcdL6nknƙLYYox

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments