Mene ne Hukuncin Wacce Tana Azumi Lokacin Shan Ruwa Sai Jini ya zo Mata?

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Mene ne Hukuncin Wacce Tana Azumi Lokacin Shan Ruwa Sai Jini ya zo Mata?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Idan Haila tazowa mace tana cikin azumi, azuminta ya lalace, ko da jinin ya zo matane kafin magariba ko da da second ɗaya ne, wajibine ta rama azumin idan na wajibi ne, haramunne taci gaba da azumi tana haila.

    Imamun Nawawi ya ce: Al'umma ta haɗu a kan haramcin azumi ga mai haila da jinin haihuwa, ko da sun yi azumin bai yiba, Al'umma ta haɗu a kan wajabcin rama azumin ramaān a kansu, Turmuzi da ibnu Munzir da Ibnu jareer da Malamanmu sun ciro ijma'i a kai.

    Al-maj-mu'u (2/386).

    Ibnu ƙudama ya ce: Malamai Sun haɗu a kan mai haila da mai jinin biƙi bai halatta musu suyi azumi ba, za su sha azumi za su rama, idan sukayi azumi baiyi ba, Aisha Allah yaƙara yarda da ita ta ce: ( Mun kasance Muna Haila azamanin Annabi Sallallahu Alaihi wasallam, yana Umartarmu da Rama azumi, ba'a umartarmu da Rama Sallah.) Bukhari da Muslim.

    Abu Sa'idin ya ce: Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ya ce: (shin idan dayanku tana haila bakuga bata sallah bata azumi ba, wannan shi ne tawayar addininta) Bukhari.

    Haila da Biƙi ɗaya suke, domin jinin biƙi shi ne na haila, hukuncinsa shi ne hukuncinsa, duk lokacin da aka samu haila a wani yanki na rana azumi ya lalace, a farkon rana ne ko aƙarshen rana, idan mai haila ta ƙudurci niyyar azumi ta kame daka ci da sha tare da masaniyar haramcin hakan, ta aikata saɓo azuminta bayi ba.

    Kamar yanda Shaik Uthaimeen ya fada a cikin littafinsa " Addima'ul dabi'iyyah lil nisa'i" shafi na (38).

    Fatawa lajnah sukace: Idan haila tazowa mace kafin faduwar rana azuminta ya lalace, amma idan bayan rana ta faɗi, bata kai ga shan ruwa ko kiran Sallah ba, azuminta yayi, ba za ta rama Shi ba.

    idan kafin faduwar rana ya zo mata, azumi ya ɓaci, za ta rama shi, idan bayan rana ta faɗi ne, azuminta ya yi ba za ta rama ba.

    WALLAHU A'ALAM.

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/IƙsWWSpUkwk6b8hWJ6vXOO

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.