Mene ne hukuncin wanda ya sha ruwa kafin faɗuwar rana a lokacin da gari yake da gajimare ?

     𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Mene ne hukuncin wanda ya sha ruwa kafin faɗuwar rana a lokacin da gari yake da gajimare ?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Shaikh Ibnu baaz Allah ya masa rahama yana cewa "Abin da yake wajaba a kan wanda haka ta faru dashi shi ne ya kame bakinsa har zuwa rana ta faɗi, sannan akwai ramakon wannan wunin akansa Abisa zancen jumhur na malamai kuma babu wani laifi akansa (na cewa ya sha ruwa rana bata faɗi ba) idan ya kasance shan ruwan da ya yi Abisa ijtihadine da kuma ƙoƙarin gane faduwar rana ɗin, hukuncin sa kamar mutumin da ya wayi gari a ranan talatin ga watan sha'aban ne baya azumi sai labari ya riskeshi da rana cewa anga wata to zai kame bakinsa ne sannan kuma ya rama wannan azumin awurin jumhur na malamai kuma babu laifi akansa, saboda alokacin da ya ci ko ya sha bai san cewa a cikin Ramaḍān yake ba (kuma baisan cewa rana bata faɗi ba) dan haka wannan rashin sanin sai ya sarayar masa da laifin amma ramakon yana nan akansa"

    سبعون مسألة مهمة في الصيام

    Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/IƙsWWSpUkwk6b8hWJ6vXOO

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.