Na Makara Ban Yi Wakan Janaba Ba Sai Bayan Fitowar Alfijir

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaykum. Malam ya ibada? Allah yasamu dace. Malam don Allah ina son nasan nayi saduwa da miji neh kuma ina son nayi azumi ko naceh natashi da niyar azumi amma sai na makara ban yi wakan tsarki da wuri ba bayan saduwa ta dashi sai 6:am na makara shin zan iya ɗauki azumi na babu damuwa? Dan Allah ayi min bayani malam Na gode

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu

    Dukkan MAZHABOBIN nan huɗu sun yi ittifaki a kan sahihancin azumin mai janaba ko mai hailan da batayi wanka ba. Sai dai an ruwaito daga URWATU BIN ZUBAIR da HASANUL BASAREE cewa idan ya jinkirta wankan da gangan ba tare da uzuri ba, to azuminsa ya ɓaci.

    Amma da a ce ba da gangan bane misali da janabar ta kama shi sai ya yi barci bai farka ba sai bayan fitowar alfijir to anan Azuminsa ya inganta. Irin wannan hukunci haka yake a ramuwar Azumin watan Ramadan. Amma ga Azumi na nafila ko wadanda ba na watan Ramadan ba ko ramuwarsa to su koda alfijir ya keto yana da janaba da gangan to Azuminsa ya inganta.

    WALLAHU A'ALAM.

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/BSA30hdZD7V3WSJF8WVwUj

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.