Ticker

Neman Yafiyar Babba-Da-Jaka

Balbela ta tuntsire da dariya, ta taɓa fikafiken Kurciya, ta ce: "Ƙawata kin ji abin da Babba-da-jaka ya ce ran nan?

Kurciya ta ce: "Kin san ni yanzu ba damuwa na yi da harkokinsa ba, sukuwa ta ƙare saura zamiya, Babba-da-jaka dai lokaci ya yi... Yauwa! Wai me ya ce ne?

"Cewa ya yi wai yana neman yafiyar tsuntsayen dajin nan, gaba ɗaya!" Balbela ta amsa.

"Zancen wofi ke nan! Lokacin da suke gallaza mana, muna neman su sassauta mana, ba izgili su kai tai mana ba?

Su kai ta faɗa mana baƙaƙen maganganu, suna cewa ba mu da haƙuri, mu ɗin ragwaye ne dai sauransu? Don haka ni ma tun da ba su ji ƙyan mu ba lokaci da muke buƙata, to su je, mun bar su da fitowar rana da faɗuwarta."

Hazbiya da ke gefe ta tsalma baki, ta ce: "Duk abin da aka shuka shi za a girba, Babba-da-jaka dai ya yi surfa mu son ransa, yanzu Tsuntsayen da akai ta kashewa a mulkinsa sakamakon sakaci da lalacinsa, duniya za su dawo su yafe masa?

Yanzu tsuntsayen da ba a haifa ba, in suka zo duniya suka tarar da irin ɓarnar Babba-da-jaka, ya tafka, ta ya za su yafe masa?"

Tattabara ta ce: "Ai maganar yafiya ma ba ta taso ba, in har ana cewa an yafe, to haka za sui ta zaluntar mutane suna cewa a yafe musu, don haka ni dai da dukkanin jinsin Tattabarai dajin nan ba mu yafe ba, a faɗa wa Babba-Da-Jaka mu haɗu ranar sakamako!"

Da ya ke dare ya fara yi, tsuntsaye kowa ya nufi sheƙarsa don shimfiɗa fiffikensa.

Daga

Mukhtar Sipikin

Post a Comment

0 Comments