Salamun alaikum. Allah ya taimaki Malam, an biya min aikin Hajji sai mijina ya mutu, shin zan iya tafiya?

     𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Salamun alaikum. Allah ya taimaki Malam, an biya min aikin Hajji sai mijina ya mutu, shin zan iya tafiya?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa alaikum assalam. Allah ya yi masa rahma. Ba za ki tafi ba, saboda Allah ya umarci wacce take takaba a Suratul Baƙara da ta zauna a gida, kar ta fita.

    Idan mace ta tafi aikin Hajji sai mijinta ya rasu bayan ta isa Makkah za ta ci gaba da aikinta, ba za ta tsaya ba ko ta dawo, saboda ƙa'idar: الدفع أسهل من الرفع, "tunkuɗe abu kafin a fara ya fi sauƙi a kan tunkuɗe shi bayan an tsunduma.

    Allah ne mafi sani.

    Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/K7RkƘRMf2b57l3UENoJ1Or

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.