Ticker

    Loading......

Sallar Nafila Da Ta Fi Daraja Cikin Nafiloli

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Malam Wace Sallar Nafila ce tafi daraja cikin Nafilolin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi wasallam yayi. ?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Alhamdulillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad ﷺ

Sallar nafila aiki ne na ibada da bawa yake yi don nuna biyayya ga Allah da neman kusanci zuwa gareshi.

Nafila nada mahimmanci ga bawa don tana cike giben da ake samu a sallar falilla. Kuma tana kusantar da bawa zuwa ga mahaliccinsa. Sallah ita ce mafificeyar ibada.

Sallar nafila tafi daraja a cikin dakin mutum, matukar ba wadda ake yi a wani guri na musamman ne ba. Annabin rahama ﷺ ya yi kuma ya koyar da nafilfili da yawa a gurare daban- daban.

Babu wani nassi karara da ke nuna sallar nafilar da tafi girman daraja a kan sauran nafilfili baki ɗaya, kowace nafila tana da falala mai girma, Sallar nafilar dare tafi na rana, kuma sallar nafila a cikin daki ya fi a masallaci, kuma sallar idi tafi duk wata nafila a ranar idin, sallar wutiri tafi sauran nafilfilin dare, sallar rokon ruwa da na kisfewan rana da wata sun fi daraja a lokacin da ake bukatar su, sallar asham tafi girman daraja a lokacin ta kuma a cikin jam’i, haka dai za ka ga wata tafi wata daraja a wani yanayi.

Lura da girman darajan sallar nafila a musulunce, malaman Fikihu sun kasa sallolin nafila zuwa gida uku:

1– Nau’in sallar nafila mafi girman daraja su ne ake kira da SUNNA MAI KARFI KO SUNNA WAJIBA. Waɗannan sallolin nafila sun fi sauran girman daraja a musulunci. Sallolin Sunna Mai Karfi ko Sunna Wajiba guda goma ne:

1 Sallar Wutiri

2 Sallar Idi karama

3 Sallar Idi Babba

4 Sallar Kisfewar Rana

5 Sallar Kisfewar Wata

6 Sallar Rokon Ruwa

7 Sallar Raka’atanul Fajri

8 Sallah Raka’a biyu na Dawafi

9 Sallah Raka’a biyu na harama da aikin hajji

10 Sai sujadar Karatun al-kur’ani a gurin Imamu Malik.

Dukkan sallonlin nan Annabi ﷺ ya dawwama a kan su har karshen rayuwar sa, ya yi umurni da yinsu. Saboda Girman darajar su, wasu malaman ma suna ganin waɗannan sallolin wajibi ne. An tsarosu ne bisa darajarsu ta ɗaya tafi ta biyu kamar yadda ta uku ta fi ta huɗu har zuwa karshe.

2– Nau’in sallar nafila mafi girman daraja a mataki na biyu su ne ake kira da FADA’IL. Waɗannan sallolin nafila suna da girman daraja amma basu kai goman farko ba:

1 – Raka’a biyu bayan alwala

2 – Raka’a biyu na gaisuwar masallaci (tahiyatu masjid)

3 – Sallar walaha (salatut Duhah)

4 – Tsayuwar dare (tahajjud)

5 – Sallar asham (tarawihi)

6 – Sallar shafa’i

7 – Sallolin nafila kafin da bayan sallar farilla (sunan al-rawatib)

3– Nau’in sallar nafila mafi girman daraja a mataki na uku su ne ake kira da NAFILFILI. Waɗannan sallolin nafila suna da girman daraja amma basu kai mataikai biyu da suka gabata ba:

1 – Sallar nafilar da batada munasaba ko lokaci, nafilar da bawa yake yi a dukk lokacin da ya samu dama cikin lokutan da ya hallata a yi nafila

2 – Nafilar da matafiyi ke yi a lokacin da zai fara tafiyar sa da kuma lokacin dawowo daga tafiyar sa (raka’a biyu)

3 – Nafilar shiga da fita daga gida (raka’a biyu)

4 – Sallar istikhara (raka’a biyu)

5 – Sallar bukata (salatul hajah) raka’a biyu

6 – Sallar tasbihi (salatut tasbih) raka’a huɗu

7 – Nafila raka’a biyu a tsakanin kiran salla da tada iƙamah

8 – Sallar nafila (raka’a biyu) a lokacin da mutum zai tuba zuwa ga Allah (salatut taubah)

9 – Sallar nafila (raka’a biyu) a lokacin da mutum zai yi addu’a

10 -Sallar nafila (raka’a biyu) a lokacin da sojoji zasu shiga yaki

WALLAHU A'ALAM

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/J1hm5Tw12uYBƙfaiPwf28l

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments