𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Shin Wajibi Ne
A Kan Mai Kula Da Maraya Ya Fitar Masa Da Zakkar Fidda-Kai?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Idan maraya yanada dukiya kamar ta gado ko wata sadaka da
akayi masa za a fitar da zakkar fidda
kansa daka cikintane, zakkar fidda kai tazama dole a cikin dukiyarsa.
Imamun Nawawi rahimahullah ya ce: Amma marayan dayake da dukiya to zakkar fidda-kai tazama wajibi a
cikin dukiyarsa awajanmu, a kan wannan jamhur din malamai suka tafi, daka
cikinsu akwai malik, da Auza'i da Abu hanifa, da Abu yusuf, da ibnu munzir.
Almajmu'u (6/109)
Amma idan bashi da dukiya, kaine kake ɗaukar ɗawainiyarsa,
bai zama wajibi a kan ka fitar masa
da zakkah ba, domin zakkar fidda-kai tana wajaba a kan wanda ciyar dashi yake
wajibi akanka, amma wanda ciyarwarsa bawajibi bace a kan mutum, rashin wajabcin
ciyarwar dake kanka ya barrantar da mutum, bai wajaba a kan mutum fitar masa da
zakkah ba.
Ibnu ƙudama ya
ce: Wannan magana ita ce maganar mafiya yawan malaman mazhabar mu, saboda fadin
Annabi sallallahu Alaihi wasallam (kubayar dazakkar fidda-kai ga wanda kuke
ciyarwa) Abul kidab yazabi wannan magana ya ce: zakkar fiddakansa bata wajaba
akansa ba, ita ce maganar mafi yawan maluma, kuma ita ce ingantacciya
insha'allahu. Almugni (2/362).
Hadisin dake cewa (kubayar da zakkar wanda kuke ciyarwa) mai
raunine mafi yawan malamai sun raunanashi, Nawawi ya ce: isnadinsa mai raunine, baihaƙi ya ce: isnadinsa bashi dakarfi,
kuma baihaƙi ya ruwaitoshi ta hanyar ja'afar bin muhammad daka babansa daka
Annabi sallallahu Alaihi wasallam shi ma dai mursali ne, Abunda yake akwai
wannan kalma ta wanda kuke ciyarwa bata tabbata ba, Almaj mu'u (6/68).
Idan ma munyarda da tabbatuwarsa ciyarwar da'ake nufi a cikin hadisin ita ce wacce take wajiba.
WALLAHU A'ALAM.
Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin
mu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/Cnf26Ƙ8MPƙz9yUYU1nxƙRƙ
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.