Shin Wajibi ne Uba Ya Fitar wa Da 'Ya'yansa Zakkar Fidda Kai?

 𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Shin Wajibi ne Uba Ya Fitar wa Da 'Ya'yansa Zakkar Fidda Kai?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Zakkar fiddakai tana cikin ibadoji farillai wanda mutum zai bayar da kansa ko ta hanyar wakilinsa.

Saboda haka ba wajibi bane ya fitarwa da 'ya'yansa zakkar fidda-kai idan sun kasance baligaine kuma masu hankali, mawadatane ko talakawa, amma idan ba balagaggu bane, idan suna da dukiya to zakkar fidda kansu za a fitar daka dukiyarsu, idan basu da dukiya zakkar fidda kansu tana kan mahaifinsu ko da suna karkashin kulawar uwarsu ne datake aure a wani wajan.

Imamun Nawawi rahimahullah ya ce: Idan yaro bashi da dukiya to zakkar fidda kansa tana kan babansa, wajibi ne babansa ya yi masa ita a ijma'in malamai, Abu hanifa da ishaƙ, da Abussauri suntafi a kan haka.

 Duba Almajmu'u (6/108).

Ya sake cewa: Idan yaro yanada wadata ciyarwarsa da zakkar fidda kansa suna cikin dukiyarsa bata kan babansa ko kakansa, Abu hanifa, da Ahmad da muhammad da Ishaƙ, a kan haka suka tafi, ibnu munzir ya ruwaito daka wasu malamai, cewa: zakkar fidda kansa tana kan babansa, idan yafitar daka dukiyar yaro ya yi sabo, sannan zai mayar masa dukiyarsa.

Idan ka tabbatar da wannan, babu ban-banci wajan wajabcin zakkar fiddakan kananun yara a kan mahaifansu, Suna karkashin kulawar mahaifiyarsu ko suna karkashin kulawar waninta, domin ciyar da su wajibi ne akansa idan basu da dukiya a ijma'in malamai, hakama zakkar fidda kai.

Ibnu munzir rahimahullah ya ce: Duk waɗanda muka haddace cikin ma'abota ilmi sun yi ijma'i ciyarwar yara kananan dabasu da dukiya tanakan mahaifinsu,

Almugni(8/169).

WALLAHU A'ALAM.

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/GcU1I5wjOB18K4PA6eURƘƘ

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments