Shin Ya Halatta Wanda Bai yi Sallar Isha'i Ba, ya bi Mai Sallar Tarawihi?

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Shin Ya Halatta Wanda Bai yi Sallar Isha'i Ba, ya bi Mai Sallar Tarawihi?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Ya kamata Musulmi yazama Mai gaggauta Yin Ayyukan Alkhairi, Musamman Alokuta Kebantattu kamar Watan Ramadan da'ake Buɗe ƙofofin rahma, Ake kulle ƙofofin Wuta, ake tsare Shaiɗanu, kowanne dare mai kira yana kira, Duk Mai neman Alkhairai yaƙara himma, mai ayyukan sharri ya Bari.

    Wanda Sallar Isha'i ta wuceshi tare da liman, bai riski jam'i ba, ana duba yanayin halin mutum, idan ka tarar Angama sallah kuma kuna da yawa kuka rasa Jam'in isha'i ɗin, daga biyu zuwa Sama, za ku yi sallar jam'i tsakaninku, donku kubuta daga saɓanin Malamai na Sallar farillah Abayan Mai nafila. Idan Mutum ya zo ana Tsaka da Sallar Asham, ko ya zo liman yafara sallar Asham da tazarar lokaci kaɗan, Kuma yana tsoran l kebewa ya tayar da Wani jam'i na Sallar isha'i da bai yi ba, zai sawa wasu rudani, anan Abunda ya fi shi ne ya bi Sallar tarawihi ɗin da niyyar Shi Isha'i yake yi, idan Liman ya yi Sallama daka raka'a ta Biyu saiya Tashi ya cikaso.

    Kamar Yanda Malam Bin Baaz Ya ce: A cikin Maj mu'u fatawa dinsa, Yana mai Hujjah da Hadisin Mu'azu Bin Jabal Allah yaƙara masa yarda ya ce: Yana Sallah Tare da Annabi Sallallahu Alaihi Wasalla., sannan Saiya koma Wajan mutanensa ya sake Yin wannan sallar dayayi Tare da Annabi da Mutanensa, Amatsayin shi nafila yai mutanensa Kuma sun yi farillah..

    WALLAHU A'ALAM.

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/J1hm5Tw12uYBƙfaiPwf28l

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.