𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum. Mutum ne zai je Umara cikin Azumi, sai ya zama jirginsu zai tashi ƙarfe biyu na ranar, shin zai kame baki ne daga safe zuwa lokacin tashin ko kuwa ba zai yi Azumi ba kwata-kwata a ranar?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikum assalam. Zancen mafi yawan Malaman Hanafiyya da Malikiyya da
Shafi'iyya shi ne: Idan mutum ya yi tafiya a tsakiyar yini, to ba zai ci abinci
ba, sai dai idan ya shiga wahalar da ba zai iya jurewa ba. Amma a wajan Malaman
Hanabila ya halatta, saboda Allah ya halattawa matafiyi cin abinci a suratul Baƙara kuma bai bambanta tsakanin wanda ya yi tafiya a
farkon yini ba da wanda ya yi a tsakiya.
Don neman ƙarin bayani duba:
Al'insaf, 3/205
Allah ne mafi sani.
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Fadakarwa a Sunnah.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/IƘUc0RxgCwA3JFiEKl8j5E
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.