Tsarabar Bayan Darasi: Taƙaitaccen Sharhi Kan Waƙar Nijeriya Ta Alhaji Shehu Shagari

      Daga taskar Farfesa Abdullahi Bayero Yahya.

    Abdullahi Bayero Yahya
    Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya
    Jami’ar Usmanu ƊanfodiyoSakkwato
    Email: 
    bagidadenlema2@gmail.com 
    Phone: 
     07031961302

    Shimfiɗa

    Amfani da waƙa wajen ilmantarwa daɗaɗɗiyar hanya ce a tarihi. Mawuyacin abu ne mutum ya binciki tarihin kowace al’ummar Musulmi ya zan ya tarar da cewa ba su yin amfani da waƙa wajen ilmantar da ‘ya’yansu ba. Misali duk wanda ya tashi a ƙasar Sakkwato ba zai kasa tunawa ba da cewa a lokacin ƙuruciyarsa a yayin karatun sanin da ya yi akwai littafin Ƙurɗaba. Littafin nan da ke farawa da Yaƙulu Yahyal ƙurɗabiyyud dari/ Almurtaji masubatil Gaffari. Wannan littafi kuwa ba a ƙasar Sakkwato ko ƙasar Hausa kurum ake sa shi a karatun sanin Musulunci ba. Hasali wanda ya wallafa shi mutumin ƙasar Andalus (Spain) ne kuma ɗan garin Ƙurɗaba (Cordova a yau).

    To kuma idan muka leƙa tarihi muna iya cewa duk Musulmin ƙasar nan yana sane da irin rawar da waƙa ta taka a lokacin jihadin da Shehu Usmanu ɗan Fodiyo ya jagoranta cikin ƙarni na 18 da na 19. Wane Bahaushe ko Bafulatani ne zai ce bai ji waƙar Ma’ama’are ba? A duk tsawon jihadin da Shehu ya yi da shi da ɗalibansa da ‘ya’yansa da sauran malamai sun kasance masu mayar da wa’azin da suka yi wa al’umma zuwa waƙoƙin da ɗalibansu kan hardace su kuma baza su cikin ƙasar Hausa da kewaye. Wannan hanya ta ci gaba ko bayan kafa daular Musulunci a ƙasar Hausa. Hasali, mutum na iya cewa waɗannan waƙoƙi sun taimaka ainun wajen tabbatar da samar da ilmi ga mutanen wannan ƙasa, abin da ya tilasta ma Turawa ‘yan mulkin mallaka suka riƙa sara suna duban bakin gatari a zamanin da suka mulke mu, saɓanin yadda suka yi wa wasu al’ummomin da ba su da irin wannan tarihi.

    Rubuta waƙoƙi a matsayin tattara gundarin ilmin da ke cikin wani littafi shi ake kira nazmi. Wannan kuwa malamai kan yi shi ne domin sauƙaƙar da neman ilmi musamman ga waɗanda ba su iya karatu da rubutu ba, saboda kuwa idan aka rera waƙoƙin za su ji abin da ake faɗa. Malamai kan zaɓi waƙa ne domin ta fi zube iya jan hankali da kuma saurin isar da saƙo. Ko ba kome zumunta tsakaninta da zuciya ta fi ta tsakanin zube ko wasan kwaikwayo da zuciyar.

    A kan wannan hanya ce Waƙar Nijeriya ta samu. Wannan waƙa nazmi ne na darussan da Alhaji Shehu Shagari ya koyar da ɗalibansa fiye da shekaru sittin da suka wuce. Sharhi a kan wannan waƙa shi ne maƙasudin wannan maƙala.

    2.0 Tsarabar Bayan Darussa

    Bayanin da zai zo nan ƙasa nazari ne ko sharhin Waƙar Nijeriya wadda Alhaji Shehu Shagari ya rubuta. A wannan maƙala an kira wannan waƙa da sunan Tsarabar Bayan Darasi domin tunatarwa ga asalin samuwarta. Ɗalibai da yawa a yau suna kallon waƙar a matsayin waƙar da aka zauna cikin dare guda aka rubuta, sannan aka miƙa ta ga wata maɗaba’a ta buga. Suna kallon ta a matsayin waƙar da tushenta a ƙwaƙwalwa yake kurum, bai da wata alaƙa da wani matashin malamin makaranta mai kuzarin aiki da zimmar ganin ɗalibansa sun fahimci darussansa ba. Da yawa daga cikin ɗaliban wannan ƙarni na ishirin da ɗaya, kai watakila har ɗaliban Kwalejin Shehu Shagari a yau da ke sauraren wannan maƙala, ba sukan kalli wannan waƙa a matsayin jingar da wani haziƙin malami, ɗan shekara ishirin da ‘yan kai, ya yi ba ɗalibansa bayan ya kammala gabatar da darussansa. To amma a haka aka rubuta Waƙar Nijeriya. Kima-kima marubucinta ya riƙa rera wa ɗalibansa ita. Wato yakan rera musu baitocin da suka jiɓinci darasi ko darussan da ya koyar da su, ko dai bayan kowane darasi ko kuwa bayan kowane rukunin darussa. Ya rera musu baitocin daidai abin da ƙwaƙwalwarsu ke iya ɗauka.

     

    2.1Tarihin Marubucin Waƙar Nijeriya

    Marubucin Waƙar Nijeriya dai sanannen mutum ne ga duk ɗan Nijeriya. Shi ne Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari, zaɓaɓɓen Shugaban ƙasa mai ɗinbin iko na farko a wannan ƙasa tamu. Ya kuwa yi wannan shugabanci ne tsakanin watan Oktoba na 1979 zuwa watan Disamba na 1983. Jam’iyyar N.P.N. (National Party of Nigeria) ce ta tsayar da shi har sau biyu a wannan muƙami kuma ya lashe zaɓen har sau biyu. Soja ne suka kawar da gwamnatinsa a watan Disamba na 1983 kuma yin haka ne ya hana gwamnatin kai ƙarshen zubi na biyu a shekarar 1987.

    An haifi Shehu Shagari, (da wannan suna aka fi sanin sa) ranar Larba 25 ga watan Fabrairu na 1925 a garin Shagari cikin lardin Sakkwato. Ya yi makarantar allo kamar yadda kowane yaro da yarinya kan yi a wannan yanki na ƙasar Hausa, wato da ita ya buɗe ido wajen neman ilmi kafin makarantar boko. Ya yi karatun boko a Yabo da Sakkwato da Katsina.

    Shehu Shagari ya fara aiki a matsayin malami a Makarantar Midil (Middle School, Sokoto). Ya karantar da fannonin kimiyya da tarihi da labarin ƙasa. Haka nan kuma ya karantar a garin Argungu. Alhaji Shehu Shagari ya shiga siyasa tun a gomiyar 1950. Ya riƙa muƙamai da dama ciki har da na minister da kwamishina da kuma Shugaba mai ɗinbin iko na farko na Nijeriya. Shi ne ya jagoranci gina kasuwar Sakkwato ta yanzu. Alhaji Shehu Shagari shi ne Turakin Sakkwato a Majalisar Sarkin Musulmi. Yana da mafi darajar lambar girmamawa ta Nijeriya, wato G.C.F.R.

    Alhaji Shehu Shagari jigo ne a fagen rubuta waƙoƙin Hausa. Shi ne Uban Ƙungiyar Marubuta Da Manazarta Waƙoƙin Hausa ta Nijeriya. Waƙoƙinsa suna da yawa, sai dai kamar yadda ɗinbin rubutattun waƙoƙin Hausa suka sha ɓacewa saboda dalilai masu yawa (ciki kuwa har da kawaicin marubutansu na ƙin fitowa da su a sarari). Waƙoƙin wannan bawan Allah har yanzu ba a san yawansu ba kuma wasu ma ba a san su ba. Ya taɓa faɗa wa marubucin wannan maƙala cewa babban sanadin salwantar mafi yawan waƙoƙinsa shi ne kiran da aka yi masa a Kaduna lokacin da yake zaune a Sakkwato. Daga ofishin Sardaunan Sakkwato ne aka kira shi. A zaton Shehu Shagari kiran ba zai wuce kwana biyu ko uku ba. Saboda haka sai ya kama hanya ba tare da kimtsa littattafansa da ke cikin barayarsa ba. To amma da isarsa Kaduna ya yi gaisuwa inda Sardauna sai shi Sardaunan ya ce masa, ka iso? Sai ka yi niyya zuwa tashar jirgi ana jiran ka ku wuce zuwa Ikko. Matafiyinmu ya garzaya zuwa tashar jirgin ƙasa, ya shiga suka runtuma sai Ikko. Suna isa aka nunnuna musu masauki. Daga bisani aka tafi da su gidan gwamnati aka rantsar da su a matsayin ministocin ƙasa. Shi ke nan zama ya kama Alhaji Shehu Shagari a Ikko, matafiyin da ya baro gida da sunan yin kwana biyu ko uku. In gajarce muku labari, Shehu Shagari bai dawo Sakkwato ba sai bayan wata shidda! Kuma ko da ya dawo ya tarar da yara sun yi abin da suka saba da takardu, ciki kuwa har da Waƙar Nijeriya da sauran waƙoƙinsa waɗanda ke rubuce cikin kundin da ya yi musu. Waƙoƙin sun salwanta ke nan sai waɗanda aka iya samowa daga ɗaiɗaikun mutane musamman ɗalibansa da abokansa.

    Wannan shi ne taƙaitaccen tarihin marubucin Waƙar Nijeriya, amma fa taƙaitawar taƙaitaccen bayani ke nan.

     

    2.2              Tarihin Waƙar Nijeriya

    Alhaji Shehu Shagari ya rubuta Waƙar Nijeriya a shekarar 1948 lokacin da yake karantarwa a Makarantar Midil ta Sakkwato. Wato ke nan yana ɗan shekara 23 ya rubuta ta.Ya faɗa cewa rubuta wannan waƙa koyi ne ya yi da malaminsa Malam Adamu Koko.[1]

    An rubuta wannan waƙa da kaɗan-kaɗan har ta yi tsawo, ba don gazawa ba, a’a sai dai saboda yanayin da ya haifar da ita. Marubucinta ya faɗa min cewa dalilai biyu suka haifar waƙar Nijeriya. Dalili na farko shi ne zamansa malamin Tarihi da Labarin Ƙasa. Da shi yana karantar da Ilmin Kimiyya ne. Haka kwatsam Turawan Mulkin Mallaka suka fito da umurnin daina koyar da Ilmin Kimiyya a makarantu wai don baturen da ke karantar da shi ya mutu, kuma musamman wai ba a iya karantar da ɗalibai wannan ilmi cikin harshen Hausa saboda ba a iya fassara kalmomin fannu na kimiyya zuwa Hausa! Saboda wannan dalili ne malaman da ke akwai a lokacin, irin su Shehu Shagari aka ce a mayar da su malaman wasu fannoni daban. To shi kuwa Shehu Shagari ya karanta Ilmin Kimiyya ne domin a lokacin ana neman a horar da malaman kimiyya. Da aka soke sai ya koma yana karantar da Tarihi da Labarin Ƙasa waɗanda yake da sha’awa da su tun azal. Ke nan zamowarsa mai koyar da waɗannan fannoni ta haifar da rubuta Waƙar Nijeriya. Sannan dalili na biyu kan rubuta waƙar da kaɗan da kaɗan shi ne marubucinta ya sheda min cewa ya lura da cewa ɗalibansa sun kasance masu sha’awar waƙa ne, rubutacciya da ta baka. Shi kuma ga shi ko bayan zamansa malami shi marubucin waƙoƙi ne. Saboda haka sai ya yi tunanin amfani da waƙa wajen karantar da ɗalibansa. A kan haka ne bayan kowane darasi ko rukunin darussa sai ya rubuta baitoci masu bayyana darasi ko darussan a taƙaice a kan allo ya rera wa ɗaliban, su kuma su rera. Waɗannan baitoci da yakan zo da su ya juya kan allo su ne ɗaliban kan rera idan suka koma ɗakunan kwana na makaranta. Ta haka ne ɗalibai da dama har da waɗanda ba na ajinsa ba suka hardace baitocin suna kuma rerawa. Haka kuma akan turo malamai daga garuwa zuwa Sakkwato domin halartar gajeren kwas na ƙarin sani dangane da hanyar karantarwa. Alhaji Shehu Shagari yana daga cikin malaman da akan zaɓa su koyar da waɗannan malamai a waɗannan kwasa-kwasai. A nan ma yakan basu waɗannan baitoci bayan ya yi musu darasi. Su kuma idan suka koma ƙauyukan da suke karantarwa sai su yi kamar yadda Shagari yake yi a Sakkwato. Ta haka ne baitocin suka bazu a duk faɗin lardin Sakkwato.

    Ta haka ne waɗannan baitoci sannu a hankali suka taru har suka zama waƙa mai tsawo, suka zama Waƙar Nijeriya. To amma fa ba a matsayin littafi kamar yadda muka san ta a yau ba. Wannan ya ɗauki lokaci mai tsawo.

    A 1951 lokacin da Alhaji Shehu Shagari yake karantarwa a Argungu wani baturen makaranta ya neme shi da ya ba da wannan waƙa domin a buga ta a matsayin littafi. Marubucin ya amince da wannan bukatar. Shi kuma baturen ya kai wa Kamfanin Gaskiya don su buga. To amma sai Kamfanin Gaskiya ya sharɗanta cewa sai marubucin ya mayar da Hausar cikin waƙar zuwa abin da suka kira Daidaitacciyar Hausa. Da bature ya mayar wa Shagari da wannan martini sai ya tambaye shi mece ce Daidaitacciyar Hausa. Bature ya faɗa masa Hausar Kano ake nufi. Shi kuwa Shagari ya mayar masa da cewa ai babu marubucin da ke iya rubuta waƙar Hausa ba tare da ya surka da Sakkwatanci ba. Saboda haka Sakkwatanci ne Hausar waƙa kuma shi ba ya jin yana iya biya wa Kamfanin Gaskiya da bukatar, wato ba zai yar da kwari ya ɗauki lefe ba.

    A gomiyar 1970 ne wata baturiya mai suna Mrs Jean Boyd ta gabatar wa Shehu Shagari da shawara cewa ya kamata a buga Waƙar Nijeriya zuwa littafi wanda ‘yan makaranta za su riƙa amfani da shi, ta kuma dage da lalle sai an buga waƙar.[2] Alhaji Shehu Shagari ya sheda mata cewa shi fa a lokacin bai da wannan waƙa a hannunsa sai fa watakila idan aka ci sa’a aka same ta a hannun abokai ko ɗalibai. Boyd kuwa ta ce ba matsala. Ka san bature da ɗaukar ma rai. Nan take ta sa cigiya a jaridu cewa ana kamɓen wannan waƙa kuma duk wanda ya biya bukatar za a ba shi goro. Ba da jimawa ba bukata ta biya. Ciroman Sakkwato Alhaji Muhammadu Bello Mai Wurno ne ya kawo Waƙar Nijeriya daga cikin adane-adanensa![3] Jean Boyd ta tuntuɓi marubucin waƙar da ya sabunta ta domin ta dace da zamani. Misali a lokacin da ya rubuta waƙar ana cikin mulkin mallaka, Nijeriya ba ta sami ‘yancin kai ba. Saboda haka baitoci kamar na 66 zuwa na 85 sababbi ne domin maganar jihohi da suka ƙunsa. A ƙarshe dai an buga Waƙar Nijeriya a 1973. Tun daga 1973 har zuwa yau an sake buga wannan waƙa har sau huɗu, 1978 da 2006 da 2007 da kuma 2009.

    Ka ambaci Shehu Shagari cikin taron ɗalibai ko malamai ko marubuta waƙoƙin Hausa ko manazartansu, haƙiƙa ko tababa babu Waƙar Nijeriya ce za ta faɗo musu a rai. Kai ko a sha’anin siyasa hakan takan auku. A zamanin da yake Shugaban Ƙasa ya kai ziyarar aiki a Amerika a zamanin da Jimmy Carter yake shugaban ƙasar Amerika. A yayin da suke cin abincin rana a fadar ƙasar Amerika sai ga wata baturiya ‘yar ƙasar ta fito tana rera Waƙar Nijeriya da Hausa. To bayan da suka ƙare cin abinci, an tashi ana gaisawa, sai Bahaushenka na Allah ya nufi wadda ba Bahaushiya ba amma ta ji Hausa raƙwai har ma da rera waƙar Hausa! Abin jin daɗi ne ga kowane Bahaushe mai kishin harshensa. To amma me ya auku a wannan ganawar da Bahausar Baturiya? Kallon sa kurum ta riƙa yi. Ita kome ba ta fahimta ba don ko ‘ha’ na Bahaushe ba ta sani ba! Ashe, ashe ilmin harshe da rera waƙa kurum ta ƙware a kai![4] Nasara hasarar ƙasa. An tsara haka ne domin Shugaban Ƙasar Nijeriya ya saki jikinsa ya ji a gida yake, ya kuma ɗebe baƙunci! Ko mene ne suke nufi? Oho o o, ya dai gane!

    Janar Mamman Vatsa ya fassara Waƙar Nijeriya zuwa harshen Ingilishi kuma an buga ta a haka. Allah ne kurum ya san ko malamin makaranta nawa ne suka yi amfani da Waƙar Nijeriya a wurin karantarwarsu. Marubucin wannan maƙala na iya tuna cewa ya yi amfani da ita a karantarwar da ya yi a makarantar Sakandare ta garin Anka. A lokacin ne ya yi ƙoƙarin zaƙulo baiwar rubuta waƙa da ke kwance cikin ɗalibansa yayin da yake rera Waƙar Nijeriya tare da su. A duk lokacin da suka rera wasu baitoci tare da maimaitawa da kuma rawa sai ya ce wa ɗaliban a sake rera baitoci sannan a yi ƙoƙarin ƙirƙiro baiti cikin karin Waƙar Nijeriya.[5]

    A yau kuma bayan shekara sittin da ɗaya (61) da Shehu Shagari ya rubuta Waƙar Nijeriya ga mu mun taru a Kwalejin Ilmi ta Shehu Shagari muna nazarin Waƙar Nijeriya ta Shehu Shagari, Wannan kwalej a yau shekarunta talatin da tara (39) da kafawa. Wato dai da Kwalejin Ilmi ta Shehu Shagari da ilahirin ɗaliban da ke cikin Kwalejin Ilmi ta Shehu Shagari da kuma wasu malaman Kwalejin, duk Waƙar Nijeriya ta Shehu Shagari ta girme su!

    2.0              Taƙaitaccen Sharhi Kan Waƙar Nijeriya

    3.1Zubi Da Tsari

    Waƙar Nijeriya waƙa ce ‘yar tagwai ko ‘yar ƙwar biyu. Wato kowane baitinta yana da sheɗara (ɗango) biyu. A yadda ta fito cikin littafi waƙar tana da baiti ɗari biyar (500). Tana da amsa-amon (ƙafiya) ciki da na waje, wato ƙarami da babban amsa-amo. Babban shi ne /ya/ a yayin da ƙaramin mai iya sauyawa ne daga wannan baiti zuwa wancan kamar yadda ya gada. Ga misalin da ke nuna abubuwan da aka faɗa:

    1.                     ‘Yan yara ku zo a faɗa muku

     Ku ji labarin Nijeriya

     

    2.                     In an tambai ku ku ce musu

    ‘Mu tamu ƙasa Nijeriya

     

    3.                     Don kam da yawa aka tambaya

    Shin wai mi an Nijeriya

     

    4.                     To wagga ƙasa ce ba wata

    Ita anka sani Nijeriya

     

    5.                     Turawa su ka raɗa mata

    Wanga suna wai Nijeriya

     

    6.                     Sun kira wani kogi Niger

    Mu Kwara muke cewa, jiya

     

    7.                     Daga sunan kogin nan ɗaya

    Suka sa na ƙasa suka rataya

    A baiti na 3 da na 7 ne kurum ƙarami da babban amsa-amo suka kasance iri ɗaya, wato duka ya ne.

    Idan aka yi nazari za a iya lura da cewa baitocin sun kasu zuwa rukuni-rukuni dangane da ƙananan jigoginta. Abin nufi a nan shi ne za a sami jerin baitoci a kan wani saƙo sannan wani jerin ya biyo baya yana magana a kan wani saƙo. Misali, baiti na 1 zuwa na 7 sun ƙunshi saƙo kan yadda aka yi aka ƙirƙiri kalmar Nijeriya aka ce sunan ƙasa ne; baiti na 8 zuwa na 9 bayani ne kan dangantakar kogin Niger da Nijeriya; baiti na 10 zuwa na 11akwai bayanmi kan tekun da kogin ya faɗa cikinsa da kuma maƙwabtan Nijeriya a arewa inda Hamada take; tarihin waɗannan maƙwabtan ƙasashe na arewacin Nijeriya shi ne saƙon da baiti na 12 zuwa na 19 suka ƙunsa, cewa can da a ƙarƙashin mulkin Faransa suke. Sai kuma baiti na 20 zuwa na 65 waɗanda ke ɗauke da bayanin yadda Nijeriya ta kasance yanki-yanki, lardi-lardi a ƙarƙashin mulkin mallakar Turawan Ingila. A rukuni-rukuni kamar waɗannan za a tarar da baitocin nan ɗari biyar na Waƙar Nijeriya. Wannan shi ya tabbatar da cewa Shehu Shagari ya rubuta wannan waƙa zubi-zubi dangane da darussan da ya karantar wa ɗalibansa.

    Ɗangogin wannan waƙa gajejjeru ne kuma mafi yawansu kammalallun jimloli ne. Suna da sauƙin fahimta ga yara. Kalmomin cikinta daidai fahimtar yara suke. Manyan kalmominta suna da sauƙin bayyanawa ga babba, wato malamin yaran. Misali, kalmar ‘hatsaniya’ a baiti na 86 ana iya fassara ta da ‘yawan faɗan baki’, Kalmar ‘amalta’ kuwa a baiti na 497 ana iya fassara ta da ‘abu ya girma ƙwarai kamar raƙumi, don raƙumin da ya girma haka shi ake kira amali’.

    Marubucin yakan yi hattara ga kawo Kalmomi masu tsauri sosai, inda yakan yi saurin fassara su da misali. Alal misali, ɗalibi zai so sanin ma’ana ‘tozartacciya’ a baiti na 254 inda Marubucin ke cewa:

    254.             Dag arewa a kai bayi kudu

     A yi musanya tozartacciya.

    Nan take a baiti na gaba sai ya kawo misalin manufar kalmar:

    255.             Don mutum ake bai a sayo giya

     Ko bindiga lalatacciya

    3.2              Salo

    Salon cikin wannan waƙa mai sauƙi ne. Haka kuwa ya dace da yanayin fahimta da rayuwar yara. Da salon ya kasance mai tsauri ne to da kuwa sha’awarsu ga waƙar ta taƙaita. Da kuma ba su ƙallafa wa kansu hardace ba balle su yaƙa ta ga junansu. Mai karatu zai fahimce abin nufi a nan idan ya kalli waɗannan baitoci:

    1. ‘Yan yara ku zo a faɗa muku

     Ku ji labarin Nijeriya

    243.             Ɗan yaro in ka so sanin

     Kurmi da tsiri Nijeriya

    244.             Taso a Arewa ka yo kudu

     Ka ga yadda suke sassakiya

     

    Kai da jin waɗannan baitoci ka san da cewa an yi la’akari da tunanin yara. Baiti na ɗaya ya fara da kwaɗaitarwar ba da labari, kamar dai malamin ya hangi cewa hankulan ɗalibansa suna wani wuri. Shi kuwa yaro da ka ce masa zo ka ji in faɗa maka wani abu ka san da cewa zai tara hankalinsa duk a gare ka. Haka nan kuma an kwaɗaitar da yara ga yin tafiye-tafiye don neman sani a baiti na 243 da na 244. Haƙiƙa waɗannan baitoci guda biyu sun fito fili a zuciyar marubucin wannan maƙala lokacin tafiyarsa ta farko daga Sakkwato zuwa Ikko cikin mota. Tsirrai da yanayin gidaje sassakiya suke yayin da mutum ya tashi daga arewacin Nijeriya ya yi kudu.

    Marubucin Waƙar Nijeriya ya tsara ta ta yin la’akari da al’adu da addinin ɗalibansa. A kai a kai yana tunatar da su hikima da baiwar Mahaliccin Sarki Allah. Dubi yadda ya gabatar da wani ɓangare na Labarin Ƙasa:

    124.             ‘Yan Adam mu ji tsoron Rabbana

     Shi ya yi ƙasa da samaniya

    125.             Ya yi taurari da farin wata

     Yai abin da ka haskaka duniya

    126.             Ita rana amfaninta biyu

     Haskenta yakan game duniya

    127.             Sannan ga zafi nata ne

     Kullum take zafafa duniya

    Wannan gabatarwa tana koya wa yara sanin iko da jinƙayin Mahaliccinsu zuwa ga mu bayinsa. Daga nan kuma sai marubucin ya shiga bayanin ilmin kimiyyar da ke cikin wannan jinƙayi da Allah ya yi wa bayinsa, wato yadda ɗalibansa ke iya gane cewa wani yanayi ya shigo (baiti na 131-2, da na 136-7) da kuma yadda rowan sama kan samu (baiti na 140-4) da dai sauransu. Haka kuma akwai irin wannan salon gabatarwa ta yin la’akari da addini a baiti na 161 a yayin da marubucin yake son yin bayani kan albarkatun ƙasa, dabbobi da itace da amfaninsu ga ‘yan Adam.

     

    Jaweabin Kammalawa

    Ba nufina ba ne in feɗe biri har wutsiya dangane da hikimomin da ke cikin Waƙar Nijeriya. Babu fili kuma babu lokaci sannan uwa uba ilmi ya ƙaranta. Abin da na yi bai wuce nuni ga ɗaliban nazarin waƙa, musamman na Kwalejin Ilmi ta Shehu Shagari, domin su sami ƙaimin nazarin wannan waƙa sosai da sosai. Ina da ra’ayin cewa ɗalibi na iya saka ta a matsayin abin Nazarin ƙwaƙƙwafi don samun digirin dokta, wato Ph.D. “Ƙwarewa a Aikin Karantarwa: Nazarin Dubarun Koyarwa Cikin Waƙar Nijeriya ta Shehu Shagari” take ne da ɗalibi mai neman Ph.D. kan iya jinjinawa.

    MANAZRTA

     

    Dunfawa, A.A. (2002), “Waƙa A Tunanin Yara”, kundin neman digiri na uku, Sokoto: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

    Ɗangambo, A (2007), Ɗaurayar Gadon Feɗe Waƙa, Zariya: Amana Publishers

    Shagari, S. (2007), Waƙar Nijeriya, Zariya: Northern Nigerian Publishing Company (NNPC).

    Shagari, S. (2009), Waƙar Nijeriya da Waƙar Hanƙuri, Kaduna: Sonia Computer

    Yahya, A.B. (1997), Jigon Nazarin Waƙa, Kaduna: Fisbas Media Services

    Yahya, A.B. (2001), “Dangantakar Waƙa Da Tarbiyyar ‘Ya’yan Hausawa” cikin HARSUNAN NIJERIYA XIX, Centre for The Study of Nigerian Languages, Kano: Bayero University, sh. 94-109

    Yahya, A.B. (2001), SALO ASIRIN WAƘA, Kaduna: FISBAS,



    [1] Duba littafin Waƙar Nijeriya da Waƙar Hanƙuri na Alhaji Shehu Shagari (2009), shafi na 5.

    [2] Duba kamar sama.

    [3] Bayani daga marubucin waƙar a cikin hirar da mai wannan maƙala ya yi da shi ranar Lahadi 07/06/2009. Ciroma kuma ɗaya daga ɗaliban marubucin waƙar ne.

    [4] Hira da Marubucin waƙar ranar Lahadi 07/06/2009.

    [5] Watakila yanzu wani ko wasu daga waɗannan ɗalibaina sun nare da rubuta waƙoƙin Hausa. Allah ne Masani

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.