Ticker

    Loading......

Yaya ya kamata a yi nafila raka'a 4 kafin azahar da bayan azahar, shin za a haɗe su ne ko kuma raka'a biyu-biyu za a yi?

 𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Yaya ya kamata a yi nafila raka'a 4 kafin azahar da bayan azahar, shin za a haɗe su ne ko kuma raka'a biyu-biyu za a yi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Sunnonin waɗanda ake cewa: rawatib guda goma sha-biyu ne wanda ambaton falalarsu ya zo a cikin hadisin ummu habiba yardar Allah takara tabbata agareta, duk wanda yabasu kulawa yana yinsu Allah zai gina masa gida A'aljannah, su ne:

Raka'a biyu kafin sallar asuba, da raka'a huɗu kafin sallar azahar, da raka'a biyu bayanta, da raka'a biyu bayan magariba, da raka'a biyu bayan isha'i.

Lokacin nafilar da'ake kafin a yi sallar farillah yana shiga dazarar lokacin sallar farillar yashiga, idan akayi kiran sallar asuba ko azahar to lokacinta yashiga kafin a yi sallar farillah.

Sannan dazarar an kammala sallar farillah lokacin nafilar da'ake bayan sallah yashiga har zuwa fitar lokacin sallar farillar.

Sannan ana yinsu ne raka'a biyu- biyu, a yi sallam ba'a haɗe su ayisu gaba ɗaya.

Bai kamata ga musulmi ya yi wasa wajan yin sallar nafilar da'ake yi lokacin sallolin farillah, ko jinkirta yinsu alokacinsu sai dai inda uzuri, kamar mantuwa ko rashin lafiya ko shagaltuwa dawani abu wanda yake dolene alokacinsu, saboda abunda ke ciki na kubcewar lada mai girma gawanda yakiyayesu alokacinsu.

Idan sun kubcewa mutum toya duba yagani saboda uzuri suka kubuce masa, kamar bacci ko mantuwa koshagaltuwa, ya halatta yaramasu akowanne lokaci yaso.

Idan ba saboda wani uzurine bai yisuba to bai halatta ya ramasuba, idan yaramasu bashi da lada, saboda duk wata ibada wacce take da lokaci kayyadadde tana wucewa da wucewar lokacinta.

Idan suka kubcewa mutum saboda wani uzuri, ya halatta yaramasu akowanne lokaci yaso cikin dare ko rana.

WALLAHU A'ALAM.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/GcU1I5wjOB18K4PA6eURƘƘ

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments