Ticker

Adabi Taskar Al’ada: Nazarin Kayan Sassaka a Karin Maganar Hausa

Cite this article as: Abdulkadair, G. (2023). Adabi Taskar Al’ada: Nazarin Kayan Sassaƙa a Karin Maganar Hausa. Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture, (2)1, 168-177. www.doi.org/10.36349/tjllc.2023.v02i01.021.

Adabi Taskar Al’ada: Nazarin Kayan Sassaƙa a Karin Maganar Hausa

Daga

Ginsau ABDULKADIR

Sashen Harsunan Nijeriya da Kimiyyar Harshe, Jami’ar Sule Lamiɗo Kafin Hausa
abdulkadirgins2017@gmail.com
ginsau.a@slu.edu.ng
08032377941, 07052820708.

Tsakure

Sassaƙa ta kasance ɗaya daga cikin manya kuma daɗaɗɗun sana’o’i masu muhimmanci da ɗan Adam ya fara gudanarwa a duniya kuma yake tunƙaho da ita. Domin ta hanyarta ne yake samar da mafi akasarin kayayyakin da ya ke amfani da su na yau da kullum a ciki da wajen gidansa. Adabi kuma wata taska ce ta adana al’adun al’umma musamman irin abubuwan da suke samarwa da hannunsu ta hanyar sana’o’in gargajiya. Saboda haka Hausawa suke amfani da azancin magana na karin magana wajen taskace sunayen irin kayayyakin da suke samarwa da hannunsu na sassaƙa. Wannan ya sa aka sami taskatuwar wasu kayayyakin al’adun Hausa waɗanda ake samarwa a sassaƙa wajen gina da bunƙasa adabin baka na Hausa, da nufin taskacewa da adanasu a ciki. Saboda haka wannan takarda ta tattaro wasu daga cikin kayan da sassaƙa ke samarwa, domin fito da muhimmancinsu tare da bayyana su ta hanyar amfani da karin maganar Hausa. Haka kuma yana da matuƙar muhimmanci a ci gaba da samar da sababbin karin magana domin adana irin waɗannan kayayyaki na al’ada waɗanda Hausawa ke samarwa ta hanyar sana’o’in gargajiya domin ‘yan baya su sami abin nazari da dogaro.

Fitilun Kalmomi: Adabi, Al’ada, Karin Magana

1.1 Gabatarwa

Amfani da adabin baka na Hausa, fannin azancin magana na karin magana wajen taskacewa da bayyana kayayyakin al’adun gargajiya na Hausa, ba baƙon abu ba ne, sai dai mafiya yawa daga cikin wasu masu nazarin al’adun gargajiya ta wannan hanya, ba su cika bayar da muhimmanci wajen al’ada ta zahiri (Material Culture) ba, wato irin abubuwan da muke iya gani, da taɓawa da amfani da su. Sun fi bayar da ƙarfi a al’ada ta ɗabi’a (Non material cuture), wato irin yadda karin magana ya taskace da bayyana gaskiya, ko mutunci, ko ƙarya, ko kara, ko wayo, ko hikima, ko tunani, ko wani abin da ya jiɓinci bukukuwa da makamantansu. A wannan aiki an yi nazari ne a kan sassaƙaƙƙun kayayyakin al’adun gargajiya, waɗanda ake samarwa a sana’ar sassaƙa ta Hausa, waɗanda adabi ya taskace su a azancin magana na karin magana. Domin haka aka tattaro karin maganganu waɗanda suka taskace kayayyakin al’adun gargajiya, waɗanda ake sassaƙawa ta hanyar sana’ar sassaƙa na Hausa.

1.2 Al’ada

Goodenough, (1957) ya ce, al’adar al’umma ta ƙunshi duk wani abin da mutum ya kamata ya sani, kuma ya amince da shi domin rayuwarsa ta gudana daidai da ta sauran al’umma. Harskovit, (1955) ya ce al’ada na nufin duk kanin wani ƙoƙari na ɗan Adam domin samarwa kansa mafita a rayuwa. Shi kuwa Burnett, (1971) cewa ya yi, al’ada abu ce wadda ta shafi ilimi da yarda, da adabi da tarbiyya da ɗabi’a da shari’a, da duk wani abin da ya shafi abin da mutane suka amince da shi suka kuma saba da shi. Sannan sai Bunza, (2006) ya ce, al’ada na nufin dukkanin rayuwar ɗan adam tun daga haihuwarsa har zuwa ƙabarinsa. Yayin da Ibrahim, (1982) kuma ya ce, al’ada ta shafi yanayin rayuwar al’umma da harkokin da suke yi na zaman duniya. Saboda haka, Ɗangambo, (1982) ya ce, al’ada abar da aka saba yi ce kuma yanki ce ta rayuwa da ta ƙunshi wasu halaye da ɗabi’u da aka saba yi kullum. Daɗin daɗawa, Sani, (1982) ya ce, al’ada na nufin haila ko wata hanya ta rayuwar al’umma ko kuma abubuwan da mutum ya saba yi a cikin rayuwarsa ta duniya. Wiliams, (2005 p. 24) da Waya, (2008 p. 152) fahimtarsu ta zo ɗaya game da al’ada, inda suka ce, al’ada hanya ce ta rayuwa wadda ta ƙunshi duk wasu harkokin rayuwar al’umma da iliminsu, kuma ana koyar da ita. Shi kuwa Har ila yau Eɓelyn, (1999) kuma cewa ya yi, al’ada karɓaɓɓiyar tsarin rayuwa ce da ta kaɗaita ga wata al’umma. Haka manazarta suka yi ta kaiwa suna komowa game da ma’anar al’ada, masanan sun haɗa da: Taylor, (1871) da Bargery, (1934) da Galadanci da wasu, (1990/1992) da Lemu, (1990) da Odegbami, (1991) da Kargi, (1993) da Amin, (2012) da sauransu.

1.3 Adabi

Gusau, (1983) da Umar, (1987) da Malumfashi, (2000) da makamatansu, sun tattauna dangane da asalin samawar adabi a duniya, yayin da suka ce sauƙar mutum a bayan ƙasa, wanda ake dangantawa da tarihin sauƙar kakan mutane, (Annabi Adamu (AS)), a wajen wani dutsi wanda ake kira da dutsen Adamu, a yankin jidda ta ƙasar Saudiyya, wurin da masana yankunan ƙasashe ke cewa, ‘gabas ta tsakiya.’ Daga nan ne ake nuna cewa, duk kowace ƙabila ta duniya ta samo asali (Malumfashi, 2000).

Kamar yadda adabin kowace al’umma ta duniya ke bin ta, haka ma Hausawa adabinsu ke bin su (Gusau, 1985). Adabin Hausa yana da dangane da mazaunin Hausawa da halayyarsu ta yau da kullum. Adabin Hausawa kuma, ya samo asali ne tun lokacin da ya fara magana har a fahimce shi. Saboda haka, a nan muna iya cewa duk inda Bahaushe ya je, to tare yake da adabinsa (Safana, 2003). ...ta haka ne adabin ya yaɗu, ta hanyar ƙaurar Hausawa da hidimar addininsu na gargajiya da kuma raya al’adunsu (Gusau, 1985).

2.1 Karin magana

Aiki irin na su Kirk-Greene, (1966) da Skinner, (1980) da Umar, (1980) da Zaruk da Alhassan, (1982), da Dangambo, (1984), da Yusuf, (1986) da Furniss, (1996), da Knappert, (1997) da Isa, (2000) da Amin, (2002) da Birniwa, (2005) da Isma’il da ’Yar aduwa, (2007) da Adedimeji, (2009) da Adeyemi, (2009) da Azima, (2011) da Ɗan Hausa, (2012) da Bugaje, (2014) da sauransu, duk sun bayyana ra’ayoyinsu dangane da fahimtarsu game da karin magana. Yayin da suka kira shi da gajere kuma dunƙulallen zance na hikima da dabarar ɓoye magana, wanda sai an yi sharhi akan iya ganewa. Amin, (2002) ya ƙara da cewa, ƙwanƙwance karin magana na buƙatar sanin al’adun al’umma dake a ciki, kaɗan ba zai wadatar ba, wajen sharhin karin magana, mai nazari na buƙatar sanin al’adun al’umma.

2.2 Sana’a

Hausawa suna cewa “Sana’a sa a”. Kalmar sana’a baƙuwar kalma ce ga Hausawa, wato kalma ce da aka aro daga harshen Larabci wato “sun’a”, mai nufin aikin da mutum zai yi na yau da kullum domin samun amfani. Da Hausawa suka aro ta sai suka yi mata kwaskwarima zuwa “sana’a” domin ta saje ta zama ’yar gida, ba tare da canja mata ma’anarta ta asali ba. Irin su Rimmer, (1948) da Usman, (1981) da Alhassan, (1982) da Idi, (1982) da Philips, (1985) da Magaji, (1985) da Dokaji, (1985) da Hassan, (1986) da Garba, (1991) da Yahaya, (1992) da Galadanci, (1992) da Masanawa, (1992) da Ɗangambo, (2008) da makamantansu suka ce, kamar yadda dukkan wani abu yake da asali a rayuwar al’umma, haka ma sana’a ta samo asalinta ne tun daga farkon rayuwar mutum.

Spiegel, (1971) shi kuma ya bayyana asalin samuwar sana’a da cewa, a sanadiyar kyaututtuka yayin bukukuwan addini aka fara musaya, har sannu a hankali al’amura suka rikiɗe zuwa baje kolin kayayyaki, daga bisani sana’a ta kankama.

Garba, (1999) ya ce, sana’o’in Hausawa, sana’o’i ne da suka shahara kuma suka bunƙasa ta wajen fasaharsu da samar da kayan amfani, kuma masu dogon tarihi. Sana’o’in Hausawa sun taso ne tare da al’adunsu da kuma harshensu, ko da yake wasu masana sun bayyana sana’ar Bahaushe ta faru ne tun lokacin da Bahaushe yake yawon cikin daji domin neman abinci, wasu kuma suka ce farauta ce farko, yayin da wasu suka ce noma shi ne fari, daga nan ta dinga bunƙasa har ta zama kowa ne gida su na da sana’arsu.

Shi kuwa Shehu, (2012 p. 1-2) ya ruwaito daga Yahaya, (1992) yana cewa, “sana’a wata hanya ce ta amfani da azanci da hikima a sarrafa albarkatu da ni’imomin da ɗan Adam ya mallaka domin buƙatun yau da kullum”. Haka kuma, sana’a abu ce wadda ta danganci tono albarkatun ƙasa da sarrafa hanyoyin kimiyya da fasaha da ni’imomin da suke tattare da ɗan Adam da sha’anin kasuwanci na saye da sayarwa da ciniki da sauransu.

Ado, (2014 p. 10-11) ya habarto daga wasu masana cewa, sana’a babbar al’ada ce mai muhimmancin gaske ga ɗan Adam. A ƙasar Hausa, an ɗauka cewa duk mutumin da ya kama wata sana’a, zai tsira da mutuncinsa daga talauci da wulaƙancin mutane. Hausawa na cewa “babu maraya sai rago.” Ke nan, Hausawa duk wani mutumin da zai sami abin yi (sana’a), ya riƙe kansa domin kar ya zama kaya, abin tausayi ga mutane (Alhassan, 1982 p. 31). Haka kuma, kamar yadda kowace al’umma ta duniya ta fara gudanar da sana’o’i, haka ma Hausawa sun fara yin sana’a domin neman biyan buƙatunsu na abinci (Yahaya, 1992 p. 48). Sana’ar farauta ita ce babbar dabara ta farko da Bahaushe ya fara yi a lokacin da ya zo ƙasar Hausa (Alhassan 1982 p. 45; Dokaji, 1985 p. 5; Garba, 1991 p. 111; Galadanci, 1992 p. 32). A lokacin da suka zo a tsattsaye suke, a gefen kogin maliya da kuma tafkin cadi (Magaji, 1985; Philips, 1985). Bincike ya nuna Hausawa suna yawo, suna neman wasu dazuzzuka da aka iya samun dabbobi da tsuntsaye. Kazalika, tarihi ya nuna cewa, Hausawa da suka fara zama a kano, maharba ne (Idi, 1982 p. 1; Dokaji 1985 p. 5). Haka ma, a katsina maharba ne suka fara zama a Durbin-ta-kusheyi (Adawa) da kuma gindin dutsen kwatarkwashi (Usman, 1981 p. 5-8).

Anan zamu fahimci cewa, Rimmer da wasu (1948) sun bayyana sana’ar noma a matsayin sana’a ta farko a wajen ɗan adam, yayin da su kuma Hassan, (1981) da Usman, (1981) da Alhassan, (1982) da Idi, (1982) da Dokaji, (1985) da Masanawa, (1992) suka bayyana farauta a matsayin sana’ar da ɗan Adam ya fara yi a duniya. A taƙaice dai, ma iya cewa noma da farauta sune sana’o’in farko da ɗan Adam ya fara, sai kuma ƙira da sassaƙa suka biyo bayan su.

2.3 Sassaƙa

Sassaƙa tana daga cikin tsofaffin sana’o’in da suka fara samuwa ga ɗan Adam tun shekaru aru-aru da suka shuɗe. An sami cewa an fara wannan sana’a ne tun lokacin da ɗan Adam ya fara samun wayewar kai da kuma ci gaba. Sana’ar sassaƙa ba bakuwar sanaa ba ce, cikin sanaoin gargajiya na Bahaushe, sanaa ce da aka daɗe ana amfani da ita wajen samar da kayayyakin amfani na al’umma. Sana’a ce da ake amfani da itace wajen aiwatar da ita. Saboda haka, mai aikin sassaƙa ake kiran sa da suna masassaƙi. Masassaƙi kan je daji ya saro itace ya masa gudumawa-gudumawa, ya ɗauko ya kawo gida, sannan ya yi amfani da kayan aikinsa na sassaƙa, domin ya sassaƙa wani abin amfani ga al’umma.

Rimmer da ingawa da wasu (1948) da Madauci da wasu (1968) da Yahaya, (1983) da Sani, (1986) da Hassan, (1998) da Mudi, (1990) da Sallau, (2012) da makamantansu, sun yi tsokaci kan sana’ar sassaƙa. Sun kawo ma’anarta da kuma irin kayayyakin da ake amfani da su domin gudanar da aikin sassaƙa, suka ce akwai makoɗi da adda da wuƙa da gatari da gizago da cinga da man kaɗanya da kuma kanwa. Sannan sun kawo wasu daga cikin irin kayayyakin da ake samarwa domin amfanin al’umma, kamar yawancin kayan da ake haɗa ganga da kujera wadda mata ke zama yayin girkin abinci, da ƙotar gatari da garma da fartanya da adda da takobi da wuƙa da manjagara da lauje da makamantansu. Sannan kuma, su ke samar da itacen da ake haɗa kwari da baka da kibiya da dunduniyar takalmi da akwashi da cokula da ludayi.

Sun ƙarƙare da cewa, da taimakon kayayyakin sassaƙa na zamani, sai aka samu kafintoci waɗanda ke sassaƙa itacen katako su samar da kujeru da bancina na karatu da gado da ƙofofi da akwatunan ajiyar kaya da sauransu. Haka kuma, sun bayyana yadda aikin sassaƙa ya samu ci gaba a kasar Hausa.

3.1 Kayayyakin da sassaƙa ke samarwa (sassaƙaƙƙun kaya)

Sassaƙar ƙasar Hausa, ta fi mayar da hankali ne ga samar da abubuwan biyan buƙata, kamar su kayan tafiye-tafiye na ruwa, irin su jirgin uwa (kwale-kwale) da gadon itace da makamantansu. Sannan da kayan amfanin gona, misali ƙotar gatari da fartanya da sungumi da lauje da sauransu. Sai kuma kayayyakin da ake amfani da su a gida irin su muciya da kuyafa da marar tuwo da akushi da bulugari da makamantansu. Haka kuma, masassaƙa ke samar da kayan taimakawa dangane da kaɗe-kaɗe, kamar su gangar jikin kayan kiɗa, irin su kalangu da tambari da kurtuku da dundufa da sauransu.

Waɗannan kayayyaki, ana samar da su ne ta hanyar amfani da itatuwa masu ƙwari, wasu kuma saboda arhar samunsu ko kariya da suke da ita wajen cin ƙwari ko makamantan haka. Itatuwan da ake amfani da su sun haɗa da, itacen kawo da ƙirya da kaɗanya da katsari da alulluɓa da gawo da ɗorawa da magarya da tsamiya da maɗaci da gamji da kuma itacen marke da sauransu. Duk waɗannan itatuwa masu ƙarfi ne da jurewa wajen gudanar da sassaƙa.

Kamar yadda aka bayyana a babi na uku wajen jero kayayyakin da ake samarwa a ƙira, haka ma a wannan babi ya ke da muhimmanci wajen ƙara tabbatar da waɗannan sassaƙaƙƙun kayayyaki, domin samun matsaya da matashiyar aiki. Kayayyakin da masassaƙa ke sassaƙawa sun haɗa da:

1.      Turmi

2.      Taɓarya

3.      Kujera

4.      Akushi

5.      Allon karatu

6.      Jirgin ruwa (kwale-kwale)

7.      Kwaure/kore (gangar jikin kayan kiɗa)

8.      Makwali/ɗankwali/kulakula. Wanda ake amfani da shi wajen kwantar da zaren sabuwar hula.

9.      Maburkaki (bulugari)

10.  Koshiya/kuyafa (cokali)

11.  Kwami na ban ruwan dabbobi

12.  Mara (wadda ake kwasar tuwo da ita ko kuma wadda ake amfani da ita wajen tuƙa jirgin ruwa (kwale-kwale))

13.  Turke

14.  Takobin ice

15.  Madaɓi

16.  Koshiya ta masaƙa

17.  Akwasa domin amfanin masaƙa

18.  Baka

19.  Ƙulƙi

20.  Ɗangarafai (takalmin ruwa)

21.  Mabuga

22.  Ɗan bugu

23.  Galibi: Wanda dukawa ke amfani da shi da sauransu.

3.2 Kayayyakin sassaƙa a karin magana

Hausawa na amfani da sunan wani kayan da suke samarwa, su gina azancin magana, da nufin ɓoye ko taskace ko bayyana wani kayansu na gargajiya a ciki. Saboda haka Hausawa suna saƙala wani kayan amfaninsu, su gina karin magana da shi, domin nuna iya gwanintar zance ko nuna naƙaltar harshe da taskace shi (kayan) a ciki. Irin wannan hikima ta haifar da samuwar kayayyaki masu yawa da ke ƙunshe a ciki, waɗanda ba domin an yi hakan ba, da yanzu wasu kayan ba a san su ba, ko kuma an manta da su, ta dalilin rashin amfani da kayan, da kuma rashin sassaƙa su a masana’antun Hausa na gargajiya.

Haka kuma, Hausawa wani lokacin, suna amfani da karin magana wajen saƙala sunayen kayayyakin da suke samarwa domin nuna muhimmancinsu, har ta kai ana samun kayayyaki masu yawan gaske waɗanda masassaƙa ke sassaƙawa ta hanyar sassaƙa, da irin kayan da ake amfani da su wajen sassaƙar. Sai dai, duk da irin wannan ƙoƙari na Bahaushe, ba kowane kaya ne aka samu wani karin magana ya ambace shi ba. A’a, akwai dai karuruwan magana masu yawa, da ke ƙunshe da sunayen kayayyakin. Irin waɗannan karin magana sun haɗa da:

a.      Doki a guje mai wuyar sa sirdi

b.      Don a daka ake son turmi

c.       Gararamba, ɗankunnen taɓarya

d.     Gero tun ba a cikin turmi ba ya san ruwa

e.      Gigi-maga, wai korar sauro da ƙota

f.        Hannunka mai sanda

g.      Da ice mai kama ake yin ƙota

h.      Idan akwai rabon kura ga turmi, sai a kai shi kasuwa a sayar a sayi akuya

i.        In ka ga goɗiya da sirdi a fadama, ubangijinta ta kayar

j.        In ka iya allonka sai ka wanke

k.      Kai kuma a suwa? Kiyashi a jirgin ruwa

l.        Ko giwa ta lalace ta fi ƙarfin talle

m.   Komai girman turmi, ɗan masu gida ya fi shi

n.      Kowa da al’adar garin su, ango ya rufe kai da turmi.

o.      Kwaɗayi kere ne, in ka sunkuya sai ya wuce

p.     Mamaki furar sayarwa a akwashi

q.      Ƙashin turmi ba na wadan kare ba ne

r.       Sabo turken wawa

s.       Samun sarari, kabewa ta yi yaɗo a akwashin maigida

t.        Sara da sassaƙa baya hana gamji tofo

u.     Turmin daka goro an daka taba

v.      Zaƙin tambari na man shanu ne, da sauransu.

3.3 Bayanin ma’anonin wasu karin magana

a.      Sara da sassaƙa baya hana gamji tofo.

Itace shi ne abin tunƙahon masassaƙi, domin da shi ya ke amfani wajen samar da abubuwa yayin sassaƙa. Saboda haka kamar yadda ƙarfe ya ke a wajen maƙeri, haka shi ma itace ya ke a wajen masassaƙi. Wannan karin magana kuma, yana nuna yadda ake amfani da itace wajen gudanar da sana’ar sassaƙa, har ya ke gwada duk yadda aka sassaƙi itace ko aka sareshi, wannan ba ya hana shi ya tofo, ya ci gaba da rayuwa.

Haka kuma karin maganar yana nufin, duk yadda mutum ya kai da aikata wani abu na ƙi ko hassada ga wani, to, wannan ba zai hana shi ci gaba ba ko rayuwa. Saboda haka, ana amfani da wannan karin magana a lokacin da aka fahimci wani na son ganin bayan ɗan uwansa.

b.      Icen da za a yi cokali da shi, kauri gare shi, da sassaƙa ya ƙare.

Wannan ma, yana nuna irin tasirin itace wajen samar da kayayyakin da ake sassaƙawa. Kuma ana amfani da wannan karin magana wajen fayyace irin mutumin da ya kamata a yi wani al’amari da shi, wato ba da kowa ake kowane aiki ba.

c.       Kowa ya yi maka kan kara, ka yi masa na itace.

Wannan yana nuna mana muhimmancin itace a wajen Bahaushe. Kuma yana nuna fifikon itace a kan kara, wajen amfani da cin moriya da makamantan su. Karin maganar kuma, yana bayyana kowa ya baka ƙaramin abu, in ka samu dama ka saka masa da babbar kyauta wadda tafi tasa da ya yi ma. Idan kuma, cutar ka ya yi, sai ka yi haƙuri shi ne babban abu fiye da nasa. Domin bisa ga al’adar Hausa, haƙuri magani ne. Wato, ‘haƙuri maganin zaman duniya’, haka kuma, ‘alheri ya fi mugunta’.

3.3.1 Kalmar sanda/kere a karin magana

Sanda/Kere: Sanda da kere masassaƙa ke samar da su, domin amfanin jama’a na yau da kullum. Ana yin sanda da dukkan itace mai ƙwari da ƙarfi, domin dogarawa wajen tafiya ko a riƙe saboda abokin gaba na mutum ko dabba. Haka ma, kere ana mafani da shi wajen kora dabbobi lokacin kiwo ko jifa da makamantansu. Masassaƙa kan sami itace dogo su sassaƙƙe shi daidai yadda ake da buƙata, domin samar da sanda ko kere. Akwai karin magana waɗanda suka taskace irin waɗannan kayayyaki kuma su ke nuna aikin su, kamar haka:

a.      Abokin biri, sandarsa ba ta kwana a sama

Bisa ga al’ada biri maɓarnaci ne a gida ko a gona, kuma ga shi da wayo wajen lura da yadda ake gudanar da al’amura. Saboda haka duk lokacin da aka ajiye wani abu domin amfani, to kuwa in ba a yi da taka-tsantsan ba bir ya ɗauke ya sauya masa wuri, idan abin ci ne kuwa lalle a tarar ya cinye. Haka kuma da sanda ake korar biri a gida ko gona, idan mutum ya rataye sandarsa a sama, to kuwa, biri ya ɗauke ta, ba tare da ya yi tsammani ba.

Karin maganar na nufin duk mai son samun wani abin duniya ba ya zama babu sana’a. Haka, mai son kama ɓarawo ba ya barci da dare.

b.      Don dare ke sanda, da rana Allah na nan

Domin samun amfani da kariya daga mugu a ke rufe ƙofa a lokacin dare, idan gari ya waye kowa yana tsoron taɓa kayan ɗan uwansa, kar a kama shi da zamba ko ha’inci.  

c.       Sandar da ke hannunka, da ita kake jifa

d.     Hannunka mai sanda

e.      In zomo na yawo, kere na yawo, wata rana za a haɗu

f.        Kwaɗayi kere ne, in ka sunkuya sai ya wuce.

3.3.2 Kalmar Turmi a Karin Magana

Turmi: Wani ma’aikaci ne da ake sassaƙe itace, a rarake cikinsa, a yi shi da faɗin baki da zurfin ciki, akan kuma raba jikinsa biyu, wato gangar jiki da gindi (wani maɗauki mai nauyi). Wani lokaci akan yi shi da mariƙi, sai dai kusan duk turmin da yake da mariƙi ƙarami ne. Wato, akan yi turmi babba domin yin manyan ayyuka, ƙarami kuma domin ƙananan ayyuka da ba wasu masu yawa ba. Akan yi turmi da itacen kaɗanya ko ƙirya ko maɗaci ko gamji da makamantansu. Turmin da ya fi aminci da ƙarko shi ne wanda aka yi shi da itacen maɗaci ko kaɗanya, domin waɗannan itatuwa ba su da saurin cinyewa ko tsagewa.

Ana amfani da turmi domin daka ko surfa abubuwa a ciki, kamar kayan abinci irinsu; gero da dawa da masara da makamantansu. Haka kuma ana kirɓa fura da ɗanyar kuka da kuɓewa, da kuma gyaɗa domin fitar da mai gabanin yin ƙuli. Sannan kuma ana daka ganyayyakin itatuwa da sauyu a turmi, domin samar da maganin cututtuka. Majema sukan kwantar da turmi su shimfiɗa fata a bayansa yayin da suka zo yin jima.

Saboda matuƙar muhimmancin turmi a wajen Bahaushe, kusan babu gidan da ba za a same shi ba, musamman a karkara. Turmi abin zama ne ga mata a tsakar gida, wato tamkar kujera yake a wurinsu. Irin wannan muhimmanci da turmi yake da shi ya sa Hausawa suke saƙala sunan turmi a cikin azancin maganarsu na karin magana, domin nuna ƙwarin abu ko juriya ko amfaninsa da makamantansu. Wannan ya sa Bahaushe yakan yi wa turmi kirari da cewa:

a.      Gungurun, turmi maganin mahaukaci.

b.      Daki bari, turmin gidan miji.

Manufar wannan azancin Magana shi ne, a nuna gagara da buwayar wani abu, shi ya sa aka alamta turmi da gungurun, wanda yake da girma kuma a kafe yake ba ya turuwa da daɗi. Har ila yau kuma, ga al’ada akwai turmin da ake yin daka a gidan Bahaushe, wani lokacin akan samu turamen da yawa da akan yi dake-dake a ciki. Domin haka, kusan duk wanda ya gagara akan danganta shi da turmi wanda aka daka aka bari. Wato ana amfani da wannan karin magana yayin da wani ya zama gagara badau a cikin al’umma, a tsamgwame shi, a kyare shi, amma yana nan daram daƙau bai fasa harkokinsa na yau da kullum ba. Haka kuma wanda wuyar duniya ta ci, ta bar shi, akan danganta shi da waɗannan karuruwan magana.

c. Domin a daka ake son turmi

Wannan ma yana ƙara bayyana aiki da amfanin turmi ga al’umma, wato daka. Ana amfani da wannan karin magana, a lokacin da aka fahimci amfanin wani abu ga al’umma.

d. Idan akwai rabon kura ga turmi, sai a kai shi kasuwa a sayar a sayi akuya

Wannan shi ne abin da Hausawa ke cewa “ina ruwan biri da gada”. Wato, kura ba ruwanta da itace domin ba cimar ta ba ne, amma da ya ke ta dalilin sa za ta samu abin kalaci sai a sayar da shi a sayo akuya, wadda take ita ce abincin ta, wato nama.

Ana amfani da wannan lokacin da wani ya nufi aikata wani abu marar amfani ga al’umma, amma kuma a fanni guda sai abun ya amfanar ta wata hanyar ta daban, wanda ba’a tsammanin hakan.

 

3.3.3 Kalmar Taɓarya a Karin Magana

Taɓarya: Ita ce mahaɗin turmi, duk inda kaji an ce turmi ka ji taɓarya, wato ɗan juma da ɗan jummai su ke. Taɓarya wani dogo kuma miƙaƙƙen itace ne mai kama da sanda, sai dai ya fi sanda kauri, tana da wasu mulmulallun kawuna biyu sama da ƙasa, wato a ƙarshenta. Ana yin taɓarya da itacen marke ko tsamiya ko bagaruwa, domin kuwa itatuwa ne masu tauri da nauyi da kuma miƙewa ba karkata. Kuma suna daɗewa ƙwarai da gaske, saboda sari ko gara da wuya su yi masu mummunar illa.

Ana amfani da taɓarya wajen daka ko surfa ko kirɓa ko murza ko mutsuttsuka, duk wani abin da aka zuba a turmi domin sarrafawa. Idan ba da ita ba, turmi amfaninsa ragagge ne. Saboda irin nuna meƙewar taɓarya, Hausawa kan yi azancin magana na karin magana kamar haka:

a. Kowa ya haɗiyi taɓarya ya kwan tsaye.

Haka kuma, domin nuna yadda siffar taɓarya take, wannan yasa ake siffanta mai nuna iya yi ko nuna gwaninta ko kikkifi cikin jama’a da karin magana kamar haka:

b. Iya yi iya reto, sakatar haƙori da taɓarya.

Wannan kuma, na sake nuna rashin yiwuwar al’amari, wato kowane abu da muhallinsa.

 

3.3.4 Kalmar Ƙota a Karin Magana

Ƙota: Wani mariƙi ne da masassaƙa ke samarwa, da ake haɗa shi da ruwa a samar da wani abin aiki a gida ko gona da sauran kayan aikin sana’o’i na gargajiya daban-dabam. Masassaƙa ke samar da ƙotocin gatari da fartanya da manjagara da masassabi da diga da garma da sauransu. Ana yin ƙota da itatuwan tsamiya da bagaruwa da marke da taura da kanya da aduwa da makamantansu. Saboda haka, ana samun karin magana masu jirwayen ƙota kamar haka: 

a.      Da ice mai kama ake ƙota

Wannan yana nufin, ba da kowane abu ake dukkannin al’amari ba. Idan mutum zai aikata wani abu, alhali kuma aikin ya fi ƙarfinsa. Sai a yi masa gargaɗi da irin wannan karin magana, ko ya fahimci inda aka sa gaba.

3.3.5 Kalmar sirdi a karin magana

Sirdi: Wannan kuma, wani mazauni ne da ake ɗorawa a kuma ɗaure a bayan doki ko raƙumi da makamantansu. Masassaƙa ke samar da shi domin amfanin jama’a wajen zama a kai. Sirdi ana yinsa da itace mai ƙwari, kamar itacen tsamiya ko aduwa ko marke da sauransu. Ana yin sa da makari mai faɗi a baya da kuma gaba mai ɗan tsayi domin ɗora hannu. Bisa ga al’ada ba a ganin dabba da sirdi sai in za a hau kanta, saboda haka duk lokacin da a ka ga wata dabba da sirdi a kanta ba tare da mahayi ko wani yana jan ta ba, to, lalle akwai magana. Wato dai, ruwa ba ya tsami banza. Wannan yasa Hausawa kan yi karin magana kamar haka:

a. In ka ga goɗiya da sirdi a fadama, ubangijinta ta kayar

b. In ka ga goɗiya da sirdi wani ta kayar.

Haka kuma, da yake a al’ada sai an riƙe duk dabbar da za a ɗora mata sirdi, wato a tsaye ba a tafe ba. To, a irin wannan hali sai ake ganin wuyar sa sirdin a tafe, bare ma a ce, a guje. Saboda haka, ake da karin magana kamar haka;

c. Doki a guje mai wuyar sa sirdi

Ana amfani da wannan yayin da aka kasa fahimtar wani al’amarin wani mutum.

Akwai kuma wasu karin maganar masu nuni da amfanin sirdi da aikinsa kamar haka:

 

3.3.6 Kalmar akushi a karin magana

Akushi: Wani abin amfani ne mai kama da ƙoƙo da ake yinsa da itace. Masassaƙa ke samar da shi, domin amfanin gida. Ana sassaƙe itace a yi masa ’yar kwaifa daidai zuba abinci a ciki, kuma abincin kan ɗauki lokaci mai tsawo bai huce ba, sannan kuma, baya ɓaci da wuri, ana rufe shi da faifai. Akwai karin magana waɗanda suka ginu da sunan akwashi a ciki, waɗanda ke nuna muhimmanci da darajar akwashi ko kyansa, da makamantansu. Irin waɗannan karin magana sun haɗa da:

a. Akushi a rufe mai kyan kallo

Bisa al’ada ana zuba abinci ne a cikin akushi musammam ma mai daɗi. Domin haka, duk wanda ya gan shi a rufe, yana sa ran akwai wani abu a ciki ke nan. Wannan ya sa akushin ya zama abin sha’awa da tsammanin ci. Wannan karin magana kuma, yana nufin duk abin da yake a rufe ba a iya ganin aibunsa ko lalacewarsa. Saboda haka, idan mutum yana da wani mummunan hali a ɓoye, ba a iya gane muninsa a fili, sai ya aikata a aikace a ke iya sanin halinsa.

b. Mamaki furar sayarwa a akushi

Akushi abin zuba abinci ne na musammam a wajen Bahaushe. Saboda haka, da wuya a ga ana wani amfani da shi saɓanin hakan, balle ma a ce ana sa wa kayan sayarwa a ciki domin talla. Saboda haka ne ma Hausawa ke yin azancin magana da saƙala sunan akushi a ciki domin nuna darajarsa da matsayinsa a wajen magidanta.

Karin maganar kuma, yana nufin idan mutum ya aikata wani hali na daban wanda darajarsa ko mutuncinsa bai kai nan ba, sai a yi masa azancin magana da irin wannan karin magana. (Mamaki furar sayarwa a akushi).

c. Samun sarari, kabewa ta yi yaɗo a akushin maigida.

A al’adar Bahaushe, maigida yana da akushin (kwanon) da ake zuba masa abinci na musamman, kuma ba a amfani da shi ko sa ma wani abu a ciki sai shi kaɗai. Saboda haka, idan wani ya yi abin da ya wuce matsayinsa ko aikinsa, wato ya wuce gona da iri ke nan. A irin wannan hali sai a yi amfani da wannan karin magana, domin nuna masa iyakarsa. Haka kuma, a kan yi amfani da irin wannan karin magana, idan mutum ya samu wata dama, ya aikata wani abu fiye da yadda aka saba ganin yana aikatawa.

 

3.3.7 Kalmar allo a karin magana

Allo: Wannan kuma, wani itace ne da masassaƙa kan sassake, su yi shi da faɗi, sannan da kai, wato mariƙi. Su gogeshi ya yi sumul-sumul yadda za a iya rubutu a jiki. Allo shi ne abin da ake amfani da shi wajen karatu, wato neman ilimi. Da shi ake amfani wajen rubuta duk abin da ake karantawa, domin haddacewa ko satu. Malamai sun fi amfani da shi, wannan ya sa ake dangantasu da shi a karin magana kamar haka:

a. Abin nema ya samu, matar Malami da cikin allo.

A al’adance kowa yana da buƙatar ya sami abin da yake mu’amala da shi cikin sauƙi. Shi kuwa Malami da allo aka san shi, a kansa yake rubutu kuma da shi yake karatu. Saboda haka, abin so ne ya same shi cikin sauƙi ba wahala, ba sai ya saya ba, ko ya roƙi bara a ba shi.

Wannan karin maganar yana nufin, idan wani yana da buƙatar samun wani abu, sai ya same shi cikin sauƙi a arha ta inda ba ya zato ko tsammani. A wannan hali sai a yi amfani da wannan karin magana. Abin nufi dai, wannan daidai yake da karin maganar da ke cewa ‘abin nema ya samu, matar ɗan sanda ta haifi ɓarawo’. Ko kuma, ‘abin nema ya samu, an jefi ’yar ƙauye da gatari’.

Haka kuma, ana amfani da aikin allo wajen gina karin magana kamar haka:

b. In ka biya allonka, sai ka wanke ko kowa ya iya allonsa, sai ya wanke.

Abin nufi, kowa ya sami dama ya yi amfani da ita tun kafin rashinta ya zo. Haka kuma tana nufin in kana da kyau ka ƙara da wanka, wato dai in kana da hujjar aikata abu sai ka aikata ba taraddadi.

 

3.3.8 Kalmar Turke a Karin Magana

Turke: Wannan wani itace ne da masassaƙa kan samar dashi domin amfanin mutane. Ana sassaƙe itace ne a yi shi da kauri da tsawo matsakaici, da kai mai faɗi, ta yadda idan an ɗaura igiya ba za ta kwaɓe ba. Ana amfani da shi wajen ɗaure dabbobi ko mahaukata. Wato dai, turke shi ne wajen ɗaure duk wani abin da ba a so ya yi yawo ko ya gudu. Saboda haka, ga al’ada duk abin da yake da turke, ana nufin nan ne farkon sa ko inda ya saba zama ko amfani. Wannan ya sa Hausawa gina karin magana da sunan turke a ciki kamar haka:

a. Babban bajimi turkenka daban.

Wannan yana nuna mana yadda turke yake da muhimmanci wajen ɗaure dabbobi, kuma daidai ruwa, daidai tsaki, wato girman dabba girman turken ta. Haka kuma, karin maganar yana nufin kowa da irin abin da ya dace da shi, gwargwadon aiki, gwargwadon lada. Wato, tuwon girma, miyar sa nama.

b. Sabo, turken wawa.

Wannan kuma, yana nufin a al’ada idan mutum ya saba da abu, ba ya son rabuwa dashi, sai dole. Ga wanda kuma, ya kasa rabuwa da wani abu, saboda sabawa da ya yi da shi, alhali kuma abin cutar dashi ya ke. To, a irin wannan hali karin maganar ta fi dacewa da shi. Abin nufi, sabawa da wani abu ya zame masa turke, ya yi masa dabaibayi, ya kasa kuɓuta daga wannan abu.

 

3.3.9 Kayan kiɗa a karin magana

Kayan kiɗan Hausawa suna da yawa, sai dai kusan kowannen su akwai ta irin hanyar da ake samar da shi da kuma yadda ake amfani da shi. Mafi akasarin kayan kiɗan Hausawa da itace ake yin su, wato masassaƙa ke samar da wani ɓangare kuma muhimmi na jikin kayan kiɗan. Abin nufi a nan shi ne, duk kayan kiɗan Hausa dangin ganga, da itace ake samar da shi. Kamar tambari da kalangu da ganga da dundufa da jauje da kurya da kotso da banga da gambara da taushi da sauransu. Wannan gangar jikin ita ake kira ‘kore’. Wannan ya sa ake da karin magana kamar haka:

a. An ci moriyar ganga, za a yada korenta.

Abin nufi a nan shi ne, idan mutum ya gama amfani da wani abu, sai ya yi watsi da shi daga baya. To, a nan sai a yi amfani da wannan karin magana, domin nusar da mutumin irin halin da ya aikata.

Tambari: Kayan kiɗa ne na Hausawa, kuma yawanci ba a kaɗawa kowa sai mai sarauta musamman ma Sarki. Wannan ne ma yasa ake cewa, ‘in ka ji tambura sai sarki, ba a kaɗa wa ’ya’yan sarki’.

b. Zaƙin tambari na man shanu ne.

Wannan kuma, na nufin duk girman tambari ba ya amo mai zaƙi, sai da taimakon man shanun da ake gogawa a rufin fatarsa. Ana amfani da wannan karin magana, idan wani yana aikata wani abu, amma ba ya iya aikatawa sai da taimakon wani. Ke nan, ba don wani ba wani baya iya gudanar da wani abu shi kaɗai. Wato, da bazar wani, wani ke taka rawa.

 

c. Tambarin talaka, cikinsa.

 

Bisa ga al’adar Hausa, talaka ba shi da abin tinƙaho, balle ya samu abin kaɗawa ko a kaɗa masa. Shi dai kullum burinsa, ya samu abin da zai cika masa ciki, na ci ko sha. Sai ya buga shi yasan ya yi daidai ba wata matsala. Saboda haka, sai ake azancin magana kamar wannan, musamman a lokacin da mutum ya samu abun da ya biya masa buƙata dai-dai gwargwadon samun sa ko matsayinsa.

d. Tambarin tama sha duka

Da yake ga al’ada tambari ana sarrafa shi ne da itace, sannan a rufa shi da fatar dabba. Anan kuma, sai aka yi amfani da ƙarfe wajen bayyana shi, domin a nuna irin ƙwari da juriya da kuma muhimmancin sa wajen kiɗa. Ana amfani da wannan karin magana, yayin da wani ya ke ta faɗi fuskantar ƙalubale na maƙiya da mahassada, masu son ganin bayansa, wato gazawarsa amma shi kuma ya jure, bai ma san ana yi ba.

Kalangu: Wannan ma, kayan kiɗa ne na Hausa, wanda ake amfani da shi domin yin rawa da waƙa. Masassaka ke samar da gangar jikinsa, wato korensa da itace ake yi kamar yadda aka bayyana a farko. Ana kuma zuba wasu ’ya’yan itatuwa, domin su riƙa motsi a ciki, yadda zasu riƙa ƙarawa kalangun wani sauti mai daɗi. Saboda haka, sai ake cewa

e. Ba girin-girin ba dai, ta yi mai, kura ta saci kalangu.

Amfanin wannan karin magana shi ne, idan wani ya himmatu wajen aikata wani aiki, kuma ana ganin zai iya gazawa wajen aiwatar da aikin, sai a yi amfani da wannan karin magana. Abin nufi, ba fara aikin ba, a gama lafiya, a samu amfani da moruwa mai kyau.

4.1 Kammalawa

Yana da kyau hukumomin kula da bunƙasa al’adun gargajiya, su ɗauki nauyin binciko da tattaro irin waɗannan kayayyaki na gargajiya, tare da adana su a wani gida na musamman. Hakan zai taimaka wajen bunƙasa kayayyakin al’adun gargajiya na Hausa. Haka kuma yana ba wa masana da manazarta shawara, da su ƙara zurfafa bincike a kan kayayyakin da ake samarwa, musamman ta hanyar sana’o’in Hausawa na gargajiya domin a sake inganta irin waɗannan kayayyaki. Sannan kuma da ƙara yin amafani da nau’o’in adabin baka na Hausa domin taskace su a ciki, wato a riƙa ƙirƙirar sababbin karin magana waɗanda za a riƙa tsattsafa irin waɗannan sunayen kayayyaki a ciki.

Haka kuma, wannan bincike yana kira ga Gwamnati da ’yan kasuwa da su ɗauki nauyin inganta irin waɗannan masana’antu na gargajiya, da kuma ɗaukan nauyin taskace yadda ake aiwatar da irin waɗannan sana’o’i cikin na’urorin zamani, ta yadda za a riƙa sayarwa ga baƙi ’yan yawon buɗe ido da ma masu sha’awa, ana samun ƙuɗin shiga. Sannan kuma, za a samu abin kallo a gidajen Hausawa da ma wasu al’umomin. Wannan zai ƙara sanya Hausawa musamman yara da matasa, su ƙara sanin daraja da muhimmancin sana’o’in su na gargajiya, da irin kayayyakin da suke samarwa da hannunsu. Abin nufi yadda suke sarrafa itatuwa domin samar da abubuwan amfani ga al’umma. Hakan zai taimaka wajen kawar da hankalin jama’a wajen amfani da kayayyakin da baƙi ke shigowa da su, waɗanda suke ƙoƙarin danne namu na gargajiyar Hausa, misalin irin kayayyakin ƙasar Sin da na Turawan yamma da Indiyawa da Amurka da makamantansu.

Sannan kuma, gwamnati ta ware wasu ranaku na musamman a duk shekara, waɗanda a cikin su za a riƙa nuna irin kayayyakin fasahar al’umma, waɗanda suke samarwa da hannunsu a gargajiyance. Ko kuma a samar da wani titi na musamman a birane da mayan garuruwa na ƙasar Hausa, waɗanda za a riƙa baje-kolin kayayyakin fasahar Hausa na hannu, har ma a riƙa sarrafa kayayyakin a wurin, tare da taimakon ƙwararru, kamar yadda ƙasar Sin ta yi a farkon shekarar da ta gabata (2016). Sannan kuma, a buɗe wuraren cin abinci da shan lemo, saboda baƙi ’yan yawon buɗe ido da masu kallon kayayyakin domin huce gajiya. Tare da buɗe gidajen kallo na kayayyakin al’adun gargajiya domin jawo hankalin baƙi da matasa sosai, saboda su iya ganin halaye na musamman na al’adun ƙasar Hausa, da ma na wasu ƙasashen masu maƙwabtaka da su.

Haka zalika, a ware wasu ranaku domin yin bukukuwan gargajiya, inda za a gayyato ƙwararru a fanni daban-dabam na sana’o’in Hausa, domin nuna irin fasaharsu a wajen. Sannan kuma, da ƙara jawo hankalin ’yan kallo da masu yawon buɗe ido su ƙara fahimtar al’adun gargajiyar Hausawa. Irin wannan zai taimaka wajen watsawa da haɓakar kayayyakin gargajiya na Hausa a duniya, ta dalilin ɗaukan hotuna da bayar da kyautar kayayyakin ga baƙi ’yan ƙasashen waje da kuma sayar musu kayan cikin farashi mai rahusa.

 Manazarta

Almajiri, T. S. (2012). Karin Magana (Proverb) As Conflict Resolution Mechanism in Hausa Society. Champion of Hausa Cikin Hausa: ABU, Press Zaria.

Amin, M. L. (2002). Hausa Metaphisical World View: A Pharmacological Expostion. Unpublished PhD. Thesis Department of Nigerian and African Languages and Cultures. Ahmadu Bello University.

Amiru, M. (1991). “Tasirin Zuwan Turawa A kan Sana’o’in Gargajiya Ƙasar Hausa”: Kundin Digiri Na Ɗaya Jami’ar Byero Kano

Bachaka, T.M. (2006). Karin Magana Cikin Waƙoƙin Sarauta: Nazarin Kan Waƙoƙin Sani Aliyu Ɗandawa.

Berley, N. (1972). Structural Approach to the Proverb and Maxim in Proverbium 20.

Bugaje, H.M. (2014). Karin Magana A Mahanga Tunani: Nazarin Lokaci A Hausa: PhD. Thesis; Department of African Languages and Cultures. Zaria: Ahmadu Bello University.

East, R. M. da wasu, (1948). Zaman Mutum da Sana’arsa: Zaria; Northern Nigeria Publishing Company

Garba, C.Y (1991). Sana’o’in Gargaajiya A Ƙasar Hausa. Spectrum Books, Ibadan.

Ibrahim U (2011). “Tasirin Haye A Sana’o’in Hausawa Na Gargajiya”. Kano: Kundin Digiri Na Biyu, Jami’ar Bayero.

Madauci da wasu (1968). Hausa Customs. NNPC Zaria . pp 50-63.

Magaji, A. (1985). “Gudummawa A Kan Ƙoƙari Da Ake Yi Na Samar Maƙalar Binciken Adabi Na Harshe Da Al’adun Hausawa, Don Juyayin Habibu Alhassan”. Sakkwato: Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usumanu Ɗanfodiyo.

Makane, W. (1970). Proverbs: A New Approach Philadelphia; the Westminster Press.

Malumfashi, I. da Ibrahim, N. M. (2014). Ƙamusun Karin Maganar Hausa: Garkuwa Publications: Kaduna, Sokoto, Kano.

Rudiger K.B.K (1996). Dictionary of Hausa Crafts: A Dialectical Documentation.

Sani, D. (1986). “Sassaƙa A Ƙasar Hausa”: Kundin Digiri Na Farko Jami’ar Bayero Kano

Shehu M. (2012). “Gurbin Sana’a A Ma’aunin Karin Magana”: Sokoto; Kundin digiri na biyu, Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

Post a Comment

0 Comments