Wannan ɗaya ce daga cikin jerin waƙoƙin da aka yi wa Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko (ALU). A hasashen manazartan Amsoshi, ALU shi ne gwamnan ƙasar Hausa da ya fi kowane gwamna yawan waƙoƙi da aka yi masa.
Jagora: Mai kwana da shirin
yaƙi,
Sahe duk,
Sadauki Sarkin Yamma,
Alu gwamnan Sakkwato,
Na Amadu.
Yara: Mai kwana da shirin
yaƙi,
Sahe duk,
Sadauki Sarkin Yamma,
Alu gwamnan Sakkwato,
Na Amadu,
Mai kwana da shirin yaƙi.
Jagora: Ali jikan Barade
Umaru,
Kuma ɗan Barade,
Yara: Bangon Tama na
Amadu,
Baban Fodiyo jagoran,
Sakkwato na Amadu,
Mai kwana da shirin yaƙi,
Sa he duk,
Sadauki sarkin Ymman,
Alu gwamnan Sakkwato.
Jagora: Ali jikan Barade
Umaru,
Kuma ɗan Barade,
Yara: Bangon Tama na
Amadu,
Baban Fodiyo jagoran,
Sakkwato na Amadu,
Mai kwana da shirin yaƙi,
Sa he duk,
Sadauki sarkin Ymman,
Alu gwamnan Sakkwato.
Jagora: Ba su iyawa da kai,
Su bi ka kawai shi am magana,
Gwamnan Sakkwato,
Yara: Mai ja maka ya san,
Wahala ɗai ta yash shigo,
Na Amadu,
Mai kwana da shirin yaƙi,
Sahe duk,
Sadauki Sarkin Yamma,
Alu gwamnan Sakkwato.
Jagora: Ba su iyawa da kai,
Su bi ka kawai shi am magana,
Gwamnan Sakkwato,
Yara: Mai ja maka ya san,
Wahala ɗai ta yash shigo,
Na Amadu,
Mai kwana da shirin yaƙi,
Sahe duk,
Sadauki Sarkin Yamma,
Alu gwamnan Sakkwato.
Jagora: Allah shi ka son
mutum,
Yakin nan mala’iku,
Sannan ‘yan Adam su bi,
Don haka mun bi ka,
Alu gwamnan Sakkwato.
Yara: Mai ja maka zai ɗau wahala,
Koko ɗan wuta na Amadu,
Mai kwana da shirin yaƙi,
Sahe duk,
Sadauki Sarkin Yamma,
Alu gwamnan Sakkwato.
Jagora: Allah shi ka son
mutum,
Yakin nan mala’iku,
Sannan ‘yan Adam su bi,
Don haka mun bi ka,
Alu gwamnan Sakkwato.
Yara: Mai ja maka zai ɗau wahala,
Koko ɗan wuta na Amadu,
Mai kwana da shirin yaƙi,
Sahe duk,
Sadauki Sarkin Yamma,
Alu gwamnan Sakkwato.
Jagora: Suri Tozon ƙasa ƙanen Mamman,
Ɗan Barade mai turawa.
Yara: Alu sadauki kake
birni da,
Dawa daji ko gida na Amadu,
Mai kwana da shirin yaƙi,
Sahe duk,
Sadauki Sarkin Yamma,
Alu gwamnan Sakkwato.
Jagora: Suri Tozon ƙasa ƙanen Mamman,
Ɗan Barade mai turawa.
Yara: Alu sadauki kake
birni da,
Dawa daji ko gida na Amadu,
Mai kwana da shirin yaƙi,
Sahe duk,
Sadauki Sarkin Yamma,
Alu gwamnan Sakkwato.
Jagora: Ya yi cif sikiriti
na jaha,
Kuma dole a ce gwamnan Sakkwato,
Yara: Sarkin Yamma na
Saluhu,
Mai aikin gaskiya na Amadu,
Mai kwana da shirin yaƙi sahe duk.
Jagora: Kai an yi cif
sikiriti na jaha,
Kmuma doke a ce gwamnan Sakkwato,
Yara: Sarkin Yamma na
Shehu,
Mai aikin gaskiya na Amadu,
Mai kwana da shirin yaƙi,
Sahe duk,
Sadauki Sarkin Yamma,
Alu gwamnan Sakkwato.
Jagora: Kamarka ne jahag ga
kane ma,
Uban Mahadi,
Yara: Kwas same ka ba hi
yash sheƙa,
Ya ɗau wata wahala,
Kowwa ac ciki na Amadu,
Mai kwana da shirin yaƙi,
Sahe duk,
Sadauki Sarkin Yamma,
Alu gwamnan Sakkwato.
Jagora: Kamarka ne jahag ga
kane ma,
Uban Mahadi,
Yara: Kwas same ka ba hi
yash sheƙa,
Ya ɗau wata wahala,
Kowwa ac ciki na Amadu,
Mai kwana da shirin yaƙi,
Sahe duk,
Sadauki Sarkin Yamma,
Alu gwamnan Sakkwato.
Jagora: In babu hassada,
An san gwamnatinka tai aiki,
Sakkwato,
Sa’annan kuma ko da hassada,
An san gwamnatinka tai aiki,
Sakkwato.
Yara: Zama an san ta raya,
Birane kuma ta raya mutan,
Ƙauyen Sakkwato na
Amadu,
Mai kwana da shirin yaƙi.
Jagora: In babu hassada,
An san gwamnatinka tai aiki,
Sakkwato,
Sa’annan kuma ko da hassada,
An san gwamnatinka tai aiki,
Sakkwato.
Yara: Zama an san ta raya,
Birane kuma ta raya mutan,
Ƙauyen Sakkwato na
Amadu,
Mai kwana da shirin yaƙi.
Jagora: Arzikin ka ya fasa
Dutse,
Gwamna mijin Azziki,
Bangon Tama mijin Murja,
Yara: Lokacinka na ka
matsa,
Wadda duk aka tsammani,
Ka hi nan na Amadu,
Mai kwana da shirin yaƙi.
Jagora: Arzikin ka ya fasa
Dutse,
Gwamna mijin Azziki,
Bangon Tama mijin Murja,
Yara: Lokacinka na ka
matsa,
Wadda duk aka tsammani,
Ka hi nan na Amadu,
Mai kwana da shirin yaƙi.
Sahe duk,
Sadauki Sarkin Yamma,
Alu gwamnan Sakkwato.
Jagora: Kowa ad da tsohuwa
mota,
Yara: Sai ya biɗi mai tura,
Mai ita na Amadu.
Jagora: Kowa ad da tsohuwa
mota,
Yara: Sai ya biɗi mai tura,
Mai ita na Amadu.
Jagora: Kowa ad da tsohuwar
mota,
Yara: Saio ya biɗi mai tura mai ita na
Amadu,
Mai kwana da shirin yaƙi,
Sahe duk
Sadauki Sarkin Yamma,
Alu gwamnan Sakkwato.
Jagora: A ko makaho bai san,
Dare ba ya san rana tsaka.
Yara: Idan rana ta kai
wani,
Ba ya faɗa mai,
Ga jiki nai yaka ji,
Kowa ash shiya na Amadu,
Mai kwana da shirin yaƙi,
Sa he duk,
Sadauki sarkin Yamma
Alu gwamnan Sakkwato.
Jagora: Ali ka yi godiya ga
Allah,
Don baiwad da a kai,
Allah ya yi ma,
Jahar Sakkwato kai ad da,
Mutane baki ɗaya na Amadu,
Yara: Mai kwana da shirin
yaƙi.
Jagora: Ali ka yi godiya ga
Allah,
Duk baiwad da a kai,
Allah ya yi ma,
Yara: Jahar Sakkwato kai
ad da,
Muane baki ɗayan na Amadu,
Mai kwana da shirin yaƙi,
Sahe duk,
Sadauki Sarkin Yamma,
Alu gwamnan Sakkwato,
Na Amadu,
Mai kwana da shirin yaƙi.
Jaogra: Zmanin ka an
ga ci gaba,
Sosai jahar Sakkwato,
An samu ci gaban ilimi,
Raya karkara da ruwan sha,
Da titunan mota kuma inda,
Ka son NEPA
an yi mai,
Yara: Jahar Sakkwato duk
inda,
Ka son titi an yi mai na Amadu,
Mai kwana da shirin yaƙi.
Jaogra: Zmanin ka an
ga ci gaba,
Sosai jahar Sakkwato,
An samu ci gaban ilimi,
Raya karkara da ruwan sha,
Da titunan mota kuma inda,
Ka son NEPA
an yi mai,
Yara: Jahar Sakkwato duk
inda,
Ka son titi an yi mai na Amadu,
Mai kwana da shirin yaƙi.
Jagora: Tashin hankali faɗace-faɗace,
In da duk a kai gefe,
Mu ba mu da wannan,
Nan jahar Sakkwato,
Mun yarda da junanmu,
Muna hulɗa sahe duk,
Duk jahar Sakkwato kowa,
Ka nufin gina yai gida,
Yara: Jahar Sakkwato kowa,
Ka nufin mota ya sawo,
Na Amadu,
Mai kwana da shirin yaƙi.
Jagora: Tashin hankali faɗace-faɗace,
In da duk a kai gefe,
Mu ba mu da wannan,
Nan jahar Sakkwato,
Mun yarda da junanmu,
Muna hulɗa sahe duk,
Duk jahar Sakkwato kowa,
Ka nufin gina yai gida,
Yara: Jahar Sakkwato kowa,
Ka nufin mota ya sawo,
Na Amadu,
Mai kwana da shirin yaƙi.
Jagora: Ali jikan Barade
Umaru,
Kuma ɗan Barade Jaɓɓi,
Yara: Bangon tama na
Amadu,
Baban Fodiyo jagoran Sakkwato,
Na Amadu,
Mai kwana da shirin yaƙi.
Jagora: Ba su iyawa da kai,
Su bi ka kawai shi am magana,
Gwamnan Sakkwato.
Yara: Mai ja maka ya san
wahala,
Ɗzai ta yab biɗo na Amadu,
Mai kwana da shirin yaƙi,
Sahe duk,
Sadauki Sarkin Yamma,
Alu gwamnan Sakkwato
Jagora: Ba su iyawa da kai,
Su bi ka kawai shi am magana,
Gwamnan Sakkwato.
Yara: Mai ja maka ya san
wahala,
Ɗzai ta yab biɗo na Amadu,
Mai kwana da shirin yaƙi,
Jagora: Suri tozon ƙasa ƙanen Mamman,
Ɗan Barade mai turawa.
Yara: Alu sadauki kake
birni,
Da dawa daji ko gida na Amadu,
Mai kwana da shirin yaƙi.
Jagora: A suri tozon ƙasa ƙanen Mamman,
Mamman Ɗan Barade mai turawa,
Yara: Alu sadauki kakr
birni da dawa,
Daji ko gida na Amadu,
Mai kwana da shirin yaƙi,
Sahe duk,
Sadauki sarkin Yamma,
Alu gwamnan Sakkwato.
Jagora: Kai an yi cif
sikuritin na jaha,
Kuma dole a ce gwamnan Sakkwato.
Yara: Sarkin Yamma na
Salihu,
Mai aikin gaskiya na Amadu,
Mai kwana da shirin yaƙi.
Jagora: Kai an yi cif
sikuriti na jaha,
Kuma dole a ce gwamnan Sakkwato,
Yara: Sarkin Yamma na
Saluhu,
Mai aikin gaskiya na Amadu,
Mai kwana da shirin yaƙi,,
Sahe duk,
Sadauki sarkin Yamma,
Alu gwamnan Sakkwato.
Jagora: Kamar ka ne jahar ga
ka nema,
Uban Mahadi,
Yara: Kwas same ka ba hi
yash sheka,
Ya ɗau wata wahala,
Kowwa ac cikin na Amadu,
Mai kwana sa shirin yaƙi.
Jagora: Kamar ka ne jahar ga
ka nema,
Uban Mahadi,
Yara: Kwas same ka ba shi
yash she ka,
Ya ɗau wata wahala,
Kowwa ac ciki na Amadu,
Mai kwana da shirin yaƙi,
Sahe duk,
Sadauki Sarkin Yamma,
Alu gwamnan Sakkwato.
Jagora: Ali in babu hassada,
An san gwamnatin ka tai aiki,
Sakkwato sa’an nan kuma,
Ko da hassada,
An san gwamnatinka tai aiki,
Sakkwato,
Yara: Zama an san ta raya
birana,
Kuma ta raya mutan ƙauyen Sakkwato,
Na Amadu mai kwana da shirin yaƙi.
Sahe duk,
Sadauki Sarkin Yamma,
Alu gwamnan Sakkwato.
Jagora: Kowa adda tsohuwar
mota,
Yara: Sai ya biɗi mai tura mai ita,
Na Amadu.
Jagora: Kowa ad da tsohuwar
mota,
Yara: Sai ya biɗi mai tura mai ita,
Na Amadu,
Mai kwana da shirin yaƙi.
Jagora: Ali ka yi godiya ga
Allah,
Duk baiwad da akai,
Allah ya yi ma,
Jahar Sakkwato kai adda,
Mutane,
Yara: Baki ɗaya,
Na Amadu,
Mai kwana da shirin yaƙi.
Jagora: Gagarabadau,
Abin ruhe ƙohohi gwamna,
Uban ɗan Ama,
Yara: Gudurmutsun dutsi
kallon ka a kai,
Sai heshin ruwa na Amadu,
Mai kwana da shirin yaƙi.
Jagora: Gagarabadau abin ruƙin ƙohohi,
Gwamna uban ɗan Ama,
Yara: Gudurmutsun dutsi,
Kallonka a kai,
Sai heshin ruwa na Amadu,
Mai kwana da shirin yaƙi,
Sahe duk,
Sadauki Sarkin Yamma,
Alu gwamnan Sakkwato.
Jagora: A ko makaho bai san
dare ba,
Ya san rana tsaka,
Yara: Idan ta kai wani ba
ya faɗa mai,
Ga jiki nai yaka ji kowa ash shiya,
Na Amadu,
Mai kwana da shirin yaƙi,
Sahe duk.
Jagora: A ko makaho bai san
dare ba,
Ya san rana tsaka,
Yara: Idan ta kai wani ba
ya faɗa mai,
Ga jiki nai yaka ji,
Kowa ash shiya,
Na Amadu.
Jagora: Zamaninka an a ci
gaba,
Sosai jahar Sakkwato,
An samu ci gaban ilimi,
Raya karkara da ruwan sha,
Da titunan mota,
Kuma inda ka san NEPA an yi mat,
Yara: Jahar Sakkwato,
Duk inda ka son titi an yi mai,
Na Amadu,
Mai kwana da shirin yaƙi.
Jagora: Zmaninka an ga ci
gaba sosai,
Jihar Sakkwato,
An samu ci gaban ilimi,
Raya karakara da ruwan sha,
Da titunan mota,
Kuma inda ka son titi an yi mai,
Yara: Jahar Sakkwato,
Duk inda ka son tutu,
An yi mai,
Yanzu jahar Sakkwato,
Duk inda ka son titi an yi mai,
Na Amadu,
Mai kwana da shirin yaƙi,
Sahe duk,
Sadauki Sarkin Yamma,
Alu gwamnan Sakkwato.
Jagora: Tashin hankali da faɗace-faɗace,
Da duk akwai gehe,
Mu ba mu da wannan Sakkwato,
Mun yarda da junanmu,
Muna hulɗa sahe dut,
Jahar Sakkwato duk wanda,
Ka son gina yai gida,
Yara: Jahar Sakkwato,
Duk wanda ka son mota ya sawo,
Na Amadu,
Mai kwana da shirin yaƙi.
Jagora: Tashin hankali faɗace-faɗacen,
Da duk a kai gehe,
Mu ba mu da wannan,
Nan Sakkwato,
Mun yarda da junanmu,
Muna hulɗa sahe dut,
Jahar Sakkwato,
Duk wanda ka son gina yai gida,
Yara: Jahar Sakkwato,
Duk wanda ka son mota ya sawo,
Na Amadu,
Mai kwana da shirin yaƙi,
Sahe duk,
Sadauki Sarkin Yamma,
Alu gwamnan Sakkwato.
Jagora: Suri tozon ƙasa ƙanen Mammam,
Ɗan Barade mai Turawa,
Yara: Alu sadauki kake,
Birni da dawa daji ko gida,
Na Amadu,
Mai kwana da shirin yaƙi.
Jagora: Suro tozon ƙasa ƙanen Mamman,
Ɗan Barade mai Turawa,
Yara: Alu sadauki kake,
Birni da dawa daji ko gida,
Na Amadu,
Mai kwana da shirin yaƙi,
Sahe duk,
Sadauki Sarkin Yamma,
Alu gwamnan Sakkwato.
Jagora: Ali jikan Barade
Umaru,
Kuma ɗan Barade Jaɓɓi,
Baban Foɗiyo,
Jagoran Sakkwato na Amadu,
Mai kwana da shirin yaƙi.
Jagora: Ali jikan Barade
Umaru,
Kuma ɗan Barade Jaɓɓi,
Yara: Bangon tama na
Amadu,
Baban Fodiyo,
Jagoran Sakkwato na Amadu.
Jagora: Ali ɗan Barde Wamakko,
Gwamnatinka tai aiki,
In ba a faɗi ijjiya ta gani,
Yara: Na Amadu,
Mai kwana da shirin yaƙi.
Jagora: Ali jikan Barade
Um,aru,
Kuma ɗan Barade Jaɓɓi,
Yara: Bangon tama na
Amadu,
Baban Fodiyo,
Jagoran Sakkwato na Amadu,
Mai kwana da shirin yaƙi.
Jagora: Kamar ka ne jahayag
ga ke nema,
Umaba Mahadi,
Yara: Lwas sameka ba shi
yash she ka,
Shi ɗau wata wahala,
Kowa ac ciki na Amadu,
Mai wakan da shirin yaƙi.
Jagora: Kamak ka ne jahag ga
ka nema,
Uban Mahadi,
Kwas same ka ba shi yash she ka,
Ya ɗau wata wahala,
Kowwa ac ciki na Amadu,
Mai kwana da shirin yaƙi,
Sahe duk.
Jagora: Miƙe tunaninka tahi,
Ja ɗamaram mulki,
Yau da wanda yas so ka,
Yau da wanda yaƙ ƙi ka,
Kama ka riƙe gwamna,
Tun da yanzu nauyin,
Yara: Kowa na bisa kanka
jahas Sakkwato,
Na Amadu,
Mai kwana da shirin yaƙi,
Sahe duk.
Jagora: Miƙe tunaninka,
Tahi ja ɗamaram mulki,
Yau da wanda yas so ka,
Yau da wanda yaƙ ƙi ka,
Kama ka riƙe gwamna,
Tunda a yanzu nauyin,
Yara: Kowa na bisa kanka,
Jahar Sakkwato,
Tun da yanzu nauyin kowa,
Na bisa kanka jahar Sakkwato,
Na Amadu,
Mai kwana da shirin yaƙi,
Sahe duk.
Jagora: Muna ganin gwamnati,
Ba dai da irin ta ka ba,
Sakkwato musakai ma,
Sun san da,
Yara: Kana mulkin Skkwato,
Na Amadu,
Mai kwana da shirin yaƙi.
Jagora: Ali jikan Barade
Umaru,
Kuma ɗan Barade Jaɓɓi,
Yara: Bangon tama na
Amadu,
Baban Foɗiyo,
Jagoran Sakkwato na Amadu,
Mai kwana da shirin yaƙi.
Jagora: Kai an yi cif
sikiriti na jaha,
Kuma dole a ce gwamnan Sakkwato,
Yara: Sarkin Yamma na
Saluhu,
Mai aikin gaskiya na Amadu,
Mai kwana da shirin yaƙi.
Jagora: Kai an yi cif
sikuriti na jaha,
Kuma dole a ce gwamnan Sakkwato,
Yara: Sarkin Yamma na
Saluhu,
Mai kwana da shirin yaƙi,
Sahe duk,
Sadauki Sarkin Yamma,
Alu gwamnan Sakkwato,
Na Amadu,
Mai kwana da shirin yaƙi,
Sahe duk,
Sadauki Sarkin Yamma,
Alu gwamnan Sakkwato.
Jagora: Gajiyayyu da
nakasassu,
Kjowane ka yi mishi albashi,
Jahar Sakkwato a daina bara,
Yara: Kowa ka bara,
Bai son gaskiya na Amadu,
Mai kwana da shirin yaƙi.
Jagora: Gajiyyyu da naƙasassu,
Kowane ka yi mishi albashi Sakkwato,
Yara: A daina bara,
Kowa ka bara bai son gaskiya,
Yac ce a daina bara,
Kowa ka bara,
Bai son gaskiya na Amadu,
Mai kwana da shirin yaƙi.
Jagora: In ba ka nan maza
suka ƙarya,
Sun faɗi suna ai maza,
Da duk ka taho ba wani mai motsawa,
Sai su dangana yau dukba zakara,
Sai kai sai su dangana,
Yara: Yau ba zakara ya
zuwa,
Sai kaya na Amadu,
Mai kwana da shirin yaƙi.
Jagora: Kai in ba ka nan
maza suke kuri,
Har su faɗi su ne wai maza,
Idan har ka zo ba wani mai motsawa,
Sai su dangana.
Yara: Yau duk ba zakara ya
zuwa sai kai.
Jagora: Sai su dangana yau
duk ba,
Yara: Zakara ya zuwa sai
kaya,
Na Amadu,
Mai kwana da shirin yaƙi,
Sahe duk,
Sadauki sarkin Yamma,
Alu gwamnan Sakkwato.
Jagora: Toron giwa,
Kai ka kiyo daji kaikaɗai,
Don namu kowa ya laɓe,
Manya sun taho na Amadu,
Yara: Mai kwana da shirin
yaƙi,
Sahe duk,
Sadauki Sarkin Yamma,
Alu gwamnan Sakkwato.
Jagora: Toron giwa kai ka
kiyo daji,
Kai kaɗai,
Yara: Don namu kowa ya laɓe,
Manya sun taho na Amadu,
Mai kwana da shirin yaƙi,
Sahe duk,
Sadauki Sarkin Yamma,
Alu gwamnan Sakkwato.
Jagora: Abin yai farko,
Na shaida yana kai ƙarshe,
Kare da kura,
Gaban da su kai tai ƙarshe,
Yawan ilimi ya fara haɗasu,
Yara: Suna gaisuwa,
Na Amadu,
Mai kwana da shirin yaƙi,
Sahe duk,
Sadauki Sarkin Yamma,
Alu gwamnan Sakkwato,
Na Amadu.
Jagora: Ali jikan Barade
Umaru,
Kuma ɗan Barade Jaɓɓi,
Yara: Bangon tama na
Amadu,
Baban Foɗiyo jagoran Sakkwato,
Na Amadu.
Jagora: A suri tozon ƙasa ƙanen Mamman,
Ɗan Barade toron giwa,
Yara: Alu sadauki kake,
Birni da dawa,
Daji ko gida,
Na Amadu,
Mai kwana da shirin yaƙi.
Jagora: Suri tozon ƙasa ƙanen Mamman,
Ɗan Barade mai turawa,
Yara: Alu sadauki kake,
Birni da dawa,
Daji ko gida,
Na Amadu.
Jagora: Gajiyayyu da naƙasassu,
Kowane kai mishi albashi,
Sakkwato,
Yara: A daina bara,
Kowa ka bara bai son gaskiya,
Na Amadu.
Jagora: Yac ce a daina bara,
Yara: Kowa ka bara bai son
gaskiya,
Na Amadu,
Mai kwana da shirin yaƙi.
Jagora: Kowa adda tsohuwam
mota,
Yara: Sai ya biɗi mai tura mai ita.
Jagora: Kowa ad da tsohuwam
mota,
Yara: Sai ya biɗi mai tura mai ita,
Na Amadu.
Jagora: Icce mai kama da ɓota,
Sakkarawa ka faɗin maganan nan na ji,
Icce mai kama da ɓota,
Sakkarawa ke faɗin maganan nan na ji,
In dai gaskiya a kai malam,
Mai kamaz zuwa aka aiki,
Wa ka shiga harkar sakare,
Na Amadu,
Yara: Mai kwana da shirin
yaƙi,
Sahe duk,
Sar\dauki Sarkin Yamma,
Alu gwamnan Sakkwato,
Jagora: Ali jikan Barade
Umaru,
Kuma ɗan Barade Jaɓɓi,
Yara: Bangon tama na
Amadu,
Baban Fodiyo jagoran Sakkwato,
Na Amadu,
Mai kwana da shirin yaƙi.
Jagora: Dutsen tsakar ruwa
kake,
Ba rana kake ji ba,
Kana nan ciki,
Yara: Gabanka da baya
cikin ni’ima,
Allah yai yo na Amadu,
Mai kwana da shirin yaƙi,
Sahe duk,
Sadauki Sarkin Yamma,
Alu gwamnan Sakkwato,
Na Amadu,
Mai kwana da shirin yaƙi,
Sahe duk.
Jagora: Aliyu magatakarda,
Uban Lamiɗo ture haushe,
Yara: Ba wani mai tare ka,
Banda ikon Allah ture haushen maza,
Aliyu magatakarda,
Uban Lamiɗo ture haushin maza,
Aliyu Magatakarda,
Uban Lamiɗo ture haushin maza.
Jagora: Alhaji Aliyu ɗan Barade,
Toron giwa mai kiyo inda ya so,
Yara: Ba wani mai tare ka,
Banda ikon Allah,
Ture haushin maza,
Aliyu Magatakarda,
Uban Lamiɗo ture haushin maza.
Jagora: Alhaji Aliyu ɗan Barade,
Toron giwa mai kiyo inda ya so,
Yara: Ba wani mai tare ka,
Banda sarauta Allah,
Ture haushin maza,
Aliyu Magatakarda,
Uban Lamiɗo.
Jagora: Maza na ta hassada
tai,
Yara: Gulbi ya haɗe su,
Ba su tantance ba,
Ture haushin maza,
Aliyu Magatakarda uban Lamiɗo.
Jagora: Maza na ta hassada
tai,
Yara: Gulbi ya haɗe su,
Ba su tantance ba,
Ture haushin maza,
Aliyu Magatakarda uban Lamiɗo.
Jagora: Ko da ma ina ta
cewa,
Gwamna ti za ka yi Alu,
Yara: Da ikon Allah.
Jagora: Ko da ma ina
tunanin,
Yara: Gwamnati za ka yi
Aliyu,
Da ikon Allah,
Ture haushin maza,
Aliyu Magatakarda uban Lamiɗo,
Ture haushin maza.
Jagora: Ga mu mun taho ma,
Alhaji ɗan Barade,
Yara: Ka ɗau kayanka,
Ture haushin maza.
Jagora: Ga ni na taho ma,
Yara: Alhaji ɗan Barade,
Sai ka ɗau kayanka,
Ture haushin maza,
Aliyu Magatakarda,
Uban Lamiɗo.
Jagora: Alhaji Aliyu ɗan Barade,
Toron giwa mai kiyo wurinda ya so kiwo,
Yara: Ba wani mai tare ka,
Sai sarauta Allah.
Jagora: Alhaji ɗan Barade,
Toron Giwa mai kiwo inda ya so,
Yara: Ba wani mai tare ka,
Sai sarauta Allah,
Ture haushin maza.
Jagora: Alhaji Aliyu ɗan Barade,
Toron giwa mai kiyo inda ya so,
Yara: Ba wani mai tare ka,
Sai sarauta Allah,
Ture haushin maza,
Aliyu magatakarda uban Lamiɗo,
Ture haushin maza,
Aliyu Magatakarda uban Lamiɗo,
Ture haushin maza.
Jagora: Ɗan Barade toron giwa,
Mai kiwo inda ya so,
Yara: Ba wani mai tare ka,
Sai sarauta Allah,
Ture haushin maza,
Aliyu Magatakarda uban Lamiɗo.
Jagora: In ka ga mutane suna
ta dibi,
Yara: Jirgi ya ɗaga sama da ikon
Allah,
Ture haushin maza,
Aliyu magatakarda uban Lamiɗo.
Jagora: In ka ga mutane suna
ta dubin jirgi,
Yara: Ya ɗaga sama da ikon
Allah,
Ture haushin maza,
Aliyu magatakarda uban Lamiɗo,
Ture haushin maza,
Aliyu magatakarda uban Lamiɗo,
Ture haushin maza,
Aliyu Magatakarda uban Lamiɗo,
Ture haushin maza.
Jagora: Ɗan Barade toron giwa,
Mai kiyo inda ya so,
Yara: Ba wani mai tare ka,
Banda sarauta Allah,
Ture haushin maza,
Aliyu Magatakarda uban Lamiɗo.
Jagora: Ni Mamman ina
tunanin,
Ali kana sama hakan ga,
Shi,
Yara: Ba shakka ture
haushin maza,
Aliyu Magatakarda uban Lamiɗo,
Ture haushin maza.
Jagora: Ɗan Barade toron giwa,
Mai kiyo inda ya so,
Yara: Ba wani mai tare ka,
Sai sarauta Allah,
Ture haushin maza,
Aliyu Magatakarda uban Lamiɗo,
Ture haushin maza.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.