Ticker

    Loading......

Ɗan Abai Alu - Waƙar Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko (ALU)

Wannan ɗaya ce daga cikin jerin waƙoƙin da aka yi wa Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko (ALU). A hasashen manazartan Amsoshi, ALU shi ne gwamnan ƙasar Hausa da ya fi kowane gwamna yawan waƙoƙi da aka yi masa.

 Jagora: Hadarin ƙasa mai maganin sanin kabido,

 Ali ɗan Amadu.

Yara: Uban Lamiɗo gamji Allah ya jima da ranka,

 Ina mai halin haiba?

 Mai girma a gai da gwamna Ali Ɗan Barade

 

Jagora: Hadarin ƙasa mai maganin sanin kabido,

 Ali na Amadu.

Yara:Uban Lamiɗo gamji ya jima da ranka.

 

Jagora: Ɗan sarki mai halin sarauta Ali Ɗan Barade.

Yara: Mai raba jakkuna da doki a haɗa da riga.

 

Jagora: Ɗan sarki mai halin sarauta Ali Ɗan Barade,

Yara: Mai raba jakkuna da doki ya haɗa da riga.

 

Jagora: Allah ya ba ka lokaci ba sai na hwaɗi ba,

Yara: Miƙe ƙahwahunka wanga ƙarfe wa za ka tsoro,

 Ina mai halin haiba?

 Mai girma a gai da gwamna Ali Ɗan Barade.

 

Jagora: Allah ya ba ka lokaci ba sai na hwaɗi ba,

Yara: Miƙe ƙahwahunka wanga ƙarhe wa za ka tsoro?

 Ina mai halin haiba?

 Mai girma Alu na gwamna Ali Ɗan Barade.

 

Jagora: Haɗarin ƙasa mai maganin sanin kabido Ali na Amadu,

Yara: Uban Lamiɗo gamji Allah ya jima da ranka.

 

Jagora: Hadarin ƙasa mai maganin sanin kabido Ali na Amadu,

Yara: Uban Lamiɗo gamji Allah ya jima da ranka.

 

Jagora: Ɗan sarki mai halin sarauta Ali Ɗan Barade,

Yara: Mai raba jakkuna da doki ya haɗa da riga.

 

Jagora: In mafarauta suna farauta daji,

 Da bindigogi,

 Da kiban dahinsu,

 Da sun zo sun ka iske zaki ba mai tsayawa.

Yara: Dawa ya ɓaci wani mutum ba ya jiran ƙani nai,

 Ina mai halin haiba?

 Mai girma a gai da gwamna Ali Ɗan Barade.

 

Jagora: In mafarauta suna farauta daji,

 Da bindigogi,

 Da kiban dahinsu,

 Da sun zo sun ka iske zaki ba mai tsayawa

 Dawa ya ɓaci.

Yara: Dawa ya ɓaci wani mutum ba ya jiran Baradai.

 Ina mai halin haiba?

 Mai girma a gai da gwamna Ali Ɗan Barade.

 

Jagora:Ɗan Sarki mai halin sarauta Ali Ɗan Barade,

Yara: Mai raba jakkuna da doki ya haɗa da riga,

 Iana mai halin haiba?

 Mai girma a gai da gwamna Ali ɗan Barade.

Post a Comment

0 Comments