Ɗanmaraya Alu - Waƙar Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko (ALU)

 Wannan ɗaya ce daga cikin jerin waƙoƙin da aka yi wa Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko (ALU). A hasashen manazartan Amsoshi, ALU shi ne gwamnan ƙasar Hausa da ya fi kowane gwamna yawan waƙoƙi da aka yi masa.

Jikan Umar a gashe ka,

Babban mutum da imani

Haba ɗa da Wamako

 

In na shigo cikin ɗasku

Muddin garin yana haske

Koko garin yana ƙyalli

A’a ko damina ko ta zauna,

Garin ko ya yi ɗan sanyi,

Aliyu na cikin binni,

Koko yana ko Wamako.

 

Haji Aliyu Wamako,

Difiti gwamna

Ɗan Barade gaishe ka,

Jikan Barade gashe ka

Jikan Umar a gaishe ka,

Ɗan nan ina da adalci,

Ɗan nan yana da imani,

Allah ya ƙara girma kau,

Allah I ƙara imani

Babban mutum da imani,

Babban mutum da dauuure kirki.

 

Amma yadda yai wa mai waƙa

Ɗan Maraya ya fode dokt

Ɗan Maraya ya dode

Sharaɗi Ɗan Maraya albarka,

Sharaɗi Ɗan Maraya ya gode.

 

…kwata gwanin tashi,

Na shige cikin Zazzau,

Funtuwa ko nan na wuce,

Binnin Gusau ko na zarce,

Binnin Gusau ko naz zarce,

Sai ga ni nan cikin esko,

Babbab ƙasak ko ko ɗon Shehu,

Albarkar Aliyu Wamako,

Jikan Umar a Gaisheka.

Allah I ƙara imani,

Dattijo mai halin kirki.

 

Amma Sakkwato ga baki ɗai,

Nai kira ko ga ɗanku,

Sakkwatawa ku nai kira kun ji?

Ku tabbata ko ga ɗanku,

Goyon baya muke buƙata

Ai suka ce ai gari ko sun ba shi,

Tuntuni ko ya samu.

 

Allah i ƙara imani,

Al’umma ta Sakkwato nac ce,

To Ɗan Maraya ya gode,

Allah i ƙara imani.

 

Allah Ubangijin bayi,

Mai dare da rana kau,

Sarkin da ba kama tai kau,

Allah ya ƙara imani.

 

Na Arziƙi a gaishe ka,

Mijin Hajiya Arziki a gaishe ka,

Dattijo Allah ya ƙara imani,

Allah ya ƙara inganci,

Albarkacin Rasulilla.

 

Baban Yasira gaishe ka,

Baban Fodiyo ubana ne,

Baban Madi ya biya waƙa,

Baban Bello mai gida na ne,

Ina wan Dawa Uban Isah?

Babaaann su Rayyanu,

Baban Halima gaishe ka,

Baban Hindatu ubana ne,

Baban Habu a gaishe ka,

Baban su Lamiɗo,

Baban Bello mai gidana ne,

Bello Koc a gaishe ka,

Allah i ƙara imani,

Albarkacin Rasulilla.

 

Ga wan dawa uban Bello,

Ga wan dawa Uban Bello,

Allah i ƙasa imani.

 

Mai rabo hanun Allah,

Lamarinshi bai muni,

Lamarinshi bai aibu,

Lamarinshi bai ɓaci

Haji, Aliyu Wamakko,

Babba magatakardan kirki,

Allah i ƙara imani,

Allah i ƙara inganci,

Haba sannu dai bikin daula.

 

Allah i ƙara inganci,

Allah i ƙara imani,

Albarkacin Rasulillah Ɗ2

 

Allahu mafificin bayi

Wanda babu iri nai ya Allah

Allahu ka taimaki ran,

Kun ji kiɗan difiti gwamna,

Amma Sakkato zan koma

Kun ji kiɗan difiti gwamna,

Haji Aliyu a gaishe ka,

Wamako, Allah shi maka albarka,

Allah shi maka sakayya,

Albarkar Manzon Allah.

 

Walahi a gida ya zuwa daji,

Sannan ko gida ko zuwa daji,

Sharaɗi birni da cikin ƙauye,

Tuntuni na ji suna taɗi,

Ai tun-tuni tun-tuni sun san ko,

Sharaɗi ko an san ka akwai kirki,

Koko kana ko ba alheri,

Ka san darajar sana’ar kowa,

Ka san darajar aikin kowa.

 

Wani yai aiki,

Wani yai sana’a,

Wani mai wasa da maciji ne,

Wani ɗan ….. jakai ne,

Shi za shi sayar fa i sai rogo,

Don i samu abincin d zai ci.

 

Allahu mafificin bayi,

Na ji maza jiya na taɗi,

Abuja suna taɗi,

Kazaure suna taɗi,

Sannan Kogi suna taɗi,

Amma Bauci zuwa tsola,

Haka na san Gwambe suna taɗi,

Adamawa tuntuni ma sun ce,

Maiduguri tuntuni ai sun ce,

Na ji Jigawa suna taɗi,

Birni na Kano birnin Kebbi,

Hatta Zamfara na taɗi,

To balle na cikin S.A.,

Sun ce tuntuni sun san ka,

Amma sabo da halin kirki,

Domin ko kana fa ɗa imani,

To Allah maka sakayya,

 

Ɗan Barade m,azan fari,

Jikan Barade mazan fari,

Ɗan Barade mazan fari,

Jikan Barade mazan fari,

Jikan Umaru gaishe ka,

Allah ya ƙara maka imani.

 

Wajen yaƙi kan zaɓe shi,

Don kun san asalin yaƙi,

Domin ku ne yaƙi,

Ka ga karatu kun san shi

Don kun gaji ko alheri,

Allah shi maka albarka,

Da gida da dawa da cikin daji,

Domin ka gaji abin kirki.

 

Allahu mafificin bayi,

Marmaza ɗauki takobinka,

Da garkuwa ko zuwa ƙarfe,

Dattijo ina ka baro mashi,

Ka je ku kwana fagen fama,yaƙi ai ka gaje shi,

To yaƙi ai ya gaje ka,

Na tabbata yaƙi ya san ka,

Na tabbata kai ka san yaƙi,

Don zaga dawa da cikin daji,

Domin yaƙi kuka gado.

 

Allah shi maka albarka,

Allah shi maka sakayya,

Da gida da dawa da cikin daji,

Allah shi maka albarka.

 

Domin kyauta yai gado,

Ya gaji yabon gado,

Domin mulki kai gado,

Arziki ka gaje shi,

Ilimi ka gaje shi,

Sannan kai gadon yaƙi,

Yaƙi ai yag gaje ka,

Sannan ka leƙa zuwa Rasha,

Ka faɗa ko ƙasan Landon,

Suna tun tuni sun san ka,

 Domin ƙarfi a fagen yaƙi.

 

Allahu mafificin bayi,

Wanda babu irin nasa ya Allah,

Allah yai maka sakayya,

Sakayyan nan ko ta alkairi.

 

Canjin salon kiɗa da rera waƙa

 

Allah mai Wahidin Allah da girma ike.

 

Allah ji mai duniya,

Wamako ni zan shige,

Allah …… nike,

Magatakarda na ce,

Aliyu mai duniya,

Bai fushi bai faɗa shi,

Bai san gardama ba.

 

Ala gyara mishi, (Ala a nan ya gajarce sunan Aallah ne)

Ala kyauta mishi,

Ko gida ko dawa,

Ala gyara mishi.

 

Ya biya mai kiɗi,

Ya biya mai kiɗi,

To ko gida ko dawa,

Allah saka mishi.

 

Allahu mafi duniya,

Allahu mafi lahira,

Ka taimaki ran ɗan Adam,

Ka taimaki ran ɗan uwa.

 

Aliyu mazan duniya,

Aliyu mazan duniya,

Kai ko a gida ko dawa,

Ko birnin wa kakae,

A nan faɗin duniya,

Ka san Aliyu akwai martaba,

Baya fushi bai fada shi,

Bai gudun ‘yan uwa,

Ba ya fushi bai faɗa,

To ba ya gudun ‘yan uwa,

To ina da mutunci ƙwarai,

Lallai shina da zumunci ƙwarai.

 

Magatakarda mazan duniya,

Wamako nakan je kuma,

Yadda yai mini ni na yaba,

Na yaba manyan ƙasa,

Yadda yai mini ni na yaba,

Na yaba manyan ƙasa.

 

Wammakko fa binni take,

Ga haƙuri na sani,

Ba su faɗa na sani,

Ga tausai na sani,

Don ba su fushi ba faɗa,

Ba su gudun ‘yan uwa,

Suna da zumunci ƙwarai,

Na san ko mutanen ƙwarai,

Ala taimaki ran ‘yan uwa (Ala, ma’ana Allah).

 

Allahu mafi duniya,

Allahu mafi lahira.

 

Na Arziki ni na yaba,

Mijin Hajiya Arziki,

Mijin Hajiya Murja ne,

Yadda yai mini ni na yaba,

Ala taimaki manyan ƙasa,

Ba ya fushi bai faɗa,

Don ba ya gudun ‘’yan uwa,

Ala taimaki manyan ƙasa,

Ala ɗaukaki manyan ƙasa,

Ala agaji manyan ƙasa,

Yana da mutunci ƙwarai.

 

Rasha zuwa Ingila,

Na farin ai na faɗi,

Balle ko mutuan Fotigal,

Ai tuntuni su sun faɗi,

Kana da mutunci ƙwarai,

Da kansu su ma sun faɗi,

Kana da mutunci ƙwarai,

Balle ko mutan Faris,

Tuntuni su sun faɗi,

Kana da mutunci ƙwarai,

Ga son ‘yan uwa,

Ala agaji manyan ƙasa,

Ala ɗaukakai manyan ƙasa.

 

Canjin salon kiɗa da rera waƙa

 

Allahu mafi girma,

Wanda babu iri nai ai Ala taimaki dattijo,

Ala taimaki mai girma

Aliyu masoyin jama’a.

 

Ya kwan da shirin daga,

Ya tashi shirin daga,

Na Arziki mai noma,

Ya kwan da shirin daga,

Ya tashi shirin daga,

Na Arziki mai girma,

Ala taimaki mamana,

Mijin Hajiya Murja,

Na Arziki mai girma.

 

Baban Yasira ubana ne,

Ala taimaki mai girma,

Ala taimaki mai girma,

Baban Bello ubana ne,

Baban Fodiyo gaishe ka,

Baban Madi a gaishe ka,

Baban Halima ubana ne,

Baban Hindatu gaishe ka,

Baban Lamiɗo a gaishe ka,

Sannun ka uban Bello Koc,

Ala taimaki mai girma,

Ya kwan da shirin daga,

Ya kwan da shirin daga,

Ala taimaki mamana,

Baban Ɗan Ama gaishe ka,

Ala taimaki mai girma,

Ka kwan da shirin daga.

 

Canjin salon kiɗa da rera waƙa

 

La’ila ha illallahu duniya

…. Ɗan Adam …….

Aliyu mazan duniya,

Gidanka da daɗin zuwa,

Ga madara ga zuma,

Amman ko da daɗin zuwa,

Don ga madara ga zuma,

…. Duniya.

 

Wamako nake son zuwa,

Ina Aliyu mazan duniya,

Magatakarda,

Wamakko da daɗin zuwa,

Garinku da daɗin zuwa,

Don ko da daɗin zuwa

Don ko ga madara ga zuma

Aliyu mazan duniya,

Wamako da daɗin zuwa,

Ɗan Barade mazan duniya,

Jikan Barade,

Babba jikan Umar,

Babba jikan Umar

 

(An samu iska a nan na ƙanƙanin lokaci da ke nuna akwai abin da aka faɗa wanda matsalar rekodin ta sa ba za a iya ji ba. Sai dai ɗan kaɗan ne).

 

Canjin salon kiɗa da rera waƙa

 

La’ilan ha’ilallah,

Yau daɗa magani sai Allah,

Haji Aliyu bawan Allah,

Magatakarda bawan Allah,

Dattijo ɗan mutan Wammako,

Haji Aliyu na Allah,

Maagatakarda na Allah,

Dattijo ɗan Mutan Wamako.

 

Allah ina bayanka,

Annabi ma shina bayanka,

Kowa i yarda da Allah,

Lamarin shi ba ya ɓaci.

 

Aliyu ga shi Aliyu,

Aliyu bawan Allah,

Mai rabo a hannun Allah,

Aliyu babbar yatsa,

In ba ki ba kaɗi ba noma,

Sannu ko babban yatsa,

Komai ake da ke za a haɗa,

In ko ba da ke ba ta ɓaci,

Aliyu ɗan mutan Wamako.

 

Na Abubakar dattijo,

Na Abubakar dattijo,

Ɗan Barade na Allah,

Jikan Barade na Allah,

Ɗauko garkuwa da ƙarfe,

Mu doshi filin yaƙi,

To tun da kun riga kun saba,

Idan batun mulki ne,

Ka riga ka saba,

Allahu ai ya ba ka,

Idan batun kuɗɗi ne,

Allahu ai ya ba ka,

 

Idan batun ilimi ne,

Wannan akwai a gidanku,

In tuntunin kun gado,

Idan batun ilimi ne,

Kun riga kun gado.

 

Saboda ikon Allah,

Saboda ikon Jalla,

Ka ba ni rigar mulki,

Ka ba ni wandon mulki,

Ka ban kuɗi in ɗan ga,

Ka ban abin hawan zamani,

Abunku ne kun gado.

 

Dattijon dattijo,

Ɗan Baraden Allah,

Jikan Barade na Allah,

Na Abubakar a’a na Abubakar Wamako,

Na ɗan Abubakar Wamako,

Na Abubakar Wamako,

Na Abubakar Wamako,

Jikan Umar mutum mai kirki,

Ya yarda da Allah,

Ya yarda da ikon Allah,

To kowa i yarda da ikon Allah,

Al’amarin shi ba ya ɓaci.

 

Ina ta roƙon Allah, Dare zuwa kuma rana,

Ka daɗe a aikin gwamnati,

Ubangiji ya ma jagora,

Don kowa i yarda da Allah,

Al’amarin shi ba ya ɓaci.

 

Amma na faɗa wa mutane,

Na ce su yarda da Allah,

A jefa sama

….. ba bu mai tantama,

Na Abubakar da Aƙilu,

Na Abubakar da Aƙilu,

Baraden Wamako,

To Allah ina bayanka,

Yikan Umar da Aƙilu,

Ubangiji shi ma albarka,

Amma na faɗa wa mutane.

 

Haji Aliyu bawan Allah,

Magatakardar Allah,

Ga Aliyu ɗan Wamako,

Mijin Hajiya Arziki,

Matanka guda biyu daidai,

Dukansu alhazai aka yi su,

Allahu shi yay yi su,

…… ƙanana.

Post a Comment

0 Comments