Bambancin Sunnah Da Bidi'a

    Sheikh Ja'afar Mahmoud Adam

    (Rahimahullah)

    Duk Ahlus-sunnah in kaci mutuncin malamin sa zaiji babu daɗi, amma ba shike nuna ya zare takobi ba ya yake dan kaci mutuncin malamin. Amma idan ka karya ƙa'idar Sunnar Manzon Allah S.A.W zai iya zare takobi ya yake ka. ƙa'idar Sunnah kenan.

    Amma ba yadda za a ce wai an zagi malamin sa yaji daɗi, yazama malamin bashi da kima a wurinka kenan. Amma an zagi malaminka za kaji babu daɗi, ba daɗi muji ka zagi wani mutum yazo ya zagi Shehu Usman bin fodiyo, ya zagi Abdullahi na gwandu, ya zagi Sheikh Muhammad bin Abdulwahab Ibn Taimiyyah, ya zagi daidai da marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi, muji ya zagi wani malami cikin malaman Sunnah a da ko a yanzu ba za muji daɗi ba! Amma ba zamu ɗauki takobi ba dan kare malamin mu yaƙe ka, ba kuma zamu kafa dandalin wa'azi ba dan ramawa malamin mu zagi, a aƙidar mu bakai daidai ba, amma bamu da lokacin da zamu ba ka amsar dan ka zage shi kaɗai, amma in kayi kuskuren ilimi sai mun maka raddi ko ka mutu ko kai rai! In kayi karya cikin Addini ko wajen tafsiri ko wani Hadisi sai mun maka raddi! Kaji haushi ɗalibanka suji haushi duk wannan bashi ya damemu ba, raddi za muyi maka ko tantama ba za muyi ba! Wannan shi ne ƙaidar Sunnah.

    ✍️ Sadik Abu-Abdallah

    ☪️ZAUREN TUNATARWA¹☪️

    https://chat.whatsapp.com/HU42MhucEVE5XT16tdzHcJ

    https://wa.me/ƙr/P7OEFXKAT4HON1

    https://www.facebook.com/abubakarmusa.usman.779

    ☪️ZAUREN TUNATARWA²☪️

    👇 https://chat.whatsapp.com/DlG1XgOpz1gI8c0uƘxgMUu

    ☪️ZAUREN TUNATARWA³☪️

    https://chat.whatsapp.com/HU42MhucEVE5XT16tdzHcJ

    ☪️ZAUREN TUNATARWA⁴☪️

    https://chat.whatsapp.com/LwiAUmsUWnƙFwXc66oƘCaJ

    Hikimomin malaman sunna

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.